*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_*Happy 4th Anniversary*
*_KARAMCI WRITERS ASSOCIATION_📚**_Shekaru huɗu kenan da kafa wannan ƙungiya, wadda take da burin taimako ga marubuta masu tasowa ta hanyar jajircewa wajen horar dasu dabaru da kuma ƙa'idojin rubutu._*
*_Alhamdulillahi marubuta da dama sun koya sun iya kuma har ma suna koyawa wasu, duk da dai shi ilmi musamman na rubutu kullum cikin koyansa ake, amma alhamdulillah muddin daga ƙungiyar karamci ka koyi rubutu lallai za a ga hakan daga labarinka. Tabbas idan ka tsaya za ka koya, idan ka mayar da hankali za ka koya, idan ka jajirce za ka iya. Madalla da ƙungiyar KARAMCI🥰❤🔥_*
Page 14
Ji tayi ya rungumeta tsam a jikinsa, babu abinda taji saboda ita bata ɗauki abin a yadda shi ya ɗauka ba, farkon zuwanta ne dai ta tsorata dashi, amma tunda ya bata abinci ya kuma tarairayeta ya yi mata alwallah ya kuma ce ta kirashi da Yaya sai taji kawai shi ɗin Wanta ne.
Ku san mintuna biyar suka ɗauka a haka sannan ya ɗago ya kuma janyeta daga jikinshi, ya ɗan samu nutsuwa amma har a lokacin bai daina jin feelings ba, sai dai ba zai taɓa iya farma ƙaramar yarinya kamar Ablah ba, wadda daya kalleta yaga sam bata fahimci komai daga abinda ya yi ba, shi ya rungumeta ne dan ya samu nutsuwa, ita kuma tambayarsa take "Baka da lafiya?"
Kai ya gyaɗa mata.
"Sannu" Ta furta a sanyaye tana kallonshi.A hankali ya tashi ya ɗauki cup ya zuba ruwan lipton tare da matsa lemon tsami a ciki, ko sugar bai saka ba ya fara sha a hankali yana sauke numfashi, sai daya shanye tas sannan ya koma kan sofa ya kwanta. Har ya lumshe ido sai kuma ya buɗe ya kalleta, yaga itama har lokacin idanunta a kanshi.
"Idan kina buƙatar wani abu ki faɗa min, idan kuma kwanciya za kiyi ki hau kan gadon"
"Uncle ka hau kan gadon ka kwanta baka da lafiya"
Kai ya girgiza ya lumshe ido yana faɗin "Nan ma ya isa."****** ******
Sai daya fito a motar sannan ya zagaya ya buɗe mata ta fito, tayi kyau sosai cikin abayar daya saya mata, kasancewarta fara sol, ta kuma saka abaya blueblack.
Ganin tana raɓe-raɓe yasa shi cewa "Karki damu muje ko"
Kai ta gyaɗa, yana gaba tana biye dashi."Barka da zuwa Alhaji" Aliya ta faɗa tana washe haƙoranta, Ablah bata taɓa ganin dariyarta ba, tana ta mamaki shi gashi tana masa dariya.
"Nan ne inda Ablah take zaune?"
"Eh uwar riƙon nata tana ciki 'yallaɓai" Ta faɗa tana russunawa kamar wanda ya girmeta, bayan ita za ta iya yin shekaru arba'in da biyar zuwa hamsin, shi kuwa Affan ba zai wuce shekaru talatin da biyu zuwa da uku ba.
"Mu shiga daga ciki bismillah" Ta furta tana matsawa, ta kalli Ablah tare da ɗan taɓe baki.
Magajiya sai nan-nan take dashi dama tunda Aliya ta faɗa mata zai zo da kanshi ya kawo Ablah da sassafe taje ta sayo kaji aka yi jar miya, aka kuma dafa lafiyayyen abinci aka sayo drinks, sannan da yazo kuwa babu wuta sai haƙuri take bashi, gashi dai itace uwar ko wace 'yar bariki a garin amma kuma gidanta ko generator babu, muhuci ta kawo masa ta kuma nemi tayi masa fifita da kanta amma ya hana, kayan abinci dake cikin manyan kuloli sabbi ƙal ta kawo ta dire gabanshi.
"Alhaji ga abinci"
Kallon kayan ya yi yana murmushi kafin ya ce "Mun ci abinci kafin mu zo nan, amma na san Ablah za ta buƙata."

YOU ARE READING
RAINA FANSA(Complete)
Historical FictionƘaddara ta kan zo wa mutum ba tare daya shirya mata ba, wala mai kyau wala akasinta, sai dai Zeenat ita ta yakicowa kanta mummunar ƙaddarar da mayar da ita rabi mutum rabi dabba. Ablah musaka ce, tana da dogayen hannuwa sai dai dungulmi ne, ma'ana b...