*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_Page 3
"Zeenat dama mun yi dashi kan cewa zai kwanta dake sau ɗaya in ya mana wannan aikin."
"Me...?" Zeenat ta furta a matuƙar tsorace, shi kuma murmushi ya yi tare da faɗin "Mene abin tsoro tunda dama kun saba, kuma ko a ranar da aka yi abin na jaddada cewa ina fatan zaku cika min alƙawari kuma kika amsa da bani da matsala, amma ya nake hango damuwa ƙarara a fuskarki?"
"Zuby...!" "Zeenat dole haka ta faru in dai muna son asirinmu ya rufu."
Zeenat ta mayar da kallonta ga Zaheedah wadda take latsa waya tana taunar cingam kamar bata san ana yi ba. "Zuby yanzu dama mutuncina kika bayar akan ƙuntata wa wani? Duk mene amfanin haka?" Zeenat ta faɗa tana jin wasu ƙwalla sun cika kurmin idanunta.
Da fa ta Zeenat tayi "Wai mene a virginity Zeenat? Ke kina tunanin za ki iya samun kamilin namiji? To bari kiji duk haka abin yake kanwar duk ja ce"
"Ba zan iya zina ba, ni na haƙura, dama Ashraf ɗin nan ni bai ɗaɗani a ƙasa ba, kawai saboda naga kin damu ya saka nayi hakan, amma sanin kanki ni kyawu bai dameni ba, auren mai kuɗi shi ne zaɓina saboda in rufawa kaina da kuma iyayena asiri, kuma kin ga ina samun masu kuɗin amma yanda suke fito da halayyarsu ta iskanci ya saka nake haƙura saboda tabbatarwa da ba aurena za suyi ba akwai abinda suke nema, amma duk irin killacewar da nayiwa budurcina kuma kike son na barar dashi anan, akan wani cikar burin da bashi da amfani. Zuby Ashraf ɗin da kike tunani wallahi girman kan ne kawai, amma bashi da ko sisi ranar har bayanshi nabi naga gidansu, wallahi duk talaucinmu Ashraf sun ninka mu, dan gidansu ko ƙofa babu sai wani labule na zanin atampa, shi ma ya gaji da datti da kuma tsufa."Tana dasa Aya Zuby ta ɗora da faɗin "To idan kuwa mai kuɗi kike so ki aura dole ki basu jikinki, hakan ba yana nufin lalata ba, a'a soyayya ce, su sun saba da haka"
"Idan kuwa har haka soyayyar take, gara na dagewa karatuna na tara kuɗaɗena amma ba zan iya zina da sunan soyayya ba."Sai lokacin Zaheedah ta tsoma baki "Wai ke uban mene a virginity ɗin? To bari kiji ƙawayena bila adadin sun yi harka kuma sun yi aure sun kuma zauna da mazajensu lafiya, idan har kika ga namiji ya gane baki zo gidanshi da budurci ba to shi ma ɗan hannu ne, tunda in bai san mata ba, ba yadda za ai ya gane a yanzu da ake harka ta matsi" Shiru Zeenat tayi kamar mai tunanin wani abu sai kuma ta juya zata fita "Zeenat ni za ki watsawa ƙasa a ido?"
"Zuby kiyi haƙuri amma ba zan iya amsar buƙatarku ba gaskiya." Tana gama faɗa ta wuce ta bar ɗakin da sauri."To ku sani wallahi zan iya tona asiri idan har ban cimma muradina ba"
"Kayi haƙuri Abdul insha Allah zan shawo kanta a hankali"
"Yanzu kun sa nayi asarar kuɗin ɗaki dana kama?"
"Ga Zaheedah sai ta rage maka zafi"
"Wace Zaheedah? Haba ni kam daga nan ma Tahir nayi dan Babyna yana can yana jira"
"To wai ya akai ita bata harka ku gashi kuna yi?"
"Bar 'yar iska kawai, kai dai a sannu za tazo hannu"
Murmushi ya yi yana shafa wuya.Zeenat napep ta tara kai tsaye tayi gida, a yanda ta shiga gidan ya saka ƙaramin ƙaninta da Nabiha suka ɗago suna kallonta "Ya dai naga kin faɗo a tsorace kamar an biyo ki" Umma ta furta lokacin da ta fito daga bayi da buta a hannu "Umma wallahi wani ne ya biyo ni, kamar ma a buge yake wai sai na bashi lamba"
"To ku dai kula sosai, dan samarin zamanin nan sai dai du'a'i"
"Yauwa Adda kizo ki ƙarasa masa home work ɗin"
"Kai Nabiha daga dawowata, kiyi masa mana"
"To ni kam Adda wallahi duk na manta wasu abubuwan gaba ɗaya fa daga mun gama JSCE muke tsayawa a bokon, Nadia ma saura ƙiris ta jona zaman gida"
Kallonta Umma tayi tana faɗin "Ke kuma haka kike so ko? Kina faɗa da murna, to idan ta dage sai ki ga ta samu an biya ta cigaba" Ita dai Zeenat gaba tayi zuwa ɗaki dan tana buƙatar samawa ƙwalwarta nutsuwa.
YOU ARE READING
RAINA FANSA(Complete)
Historical FictionƘaddara ta kan zo wa mutum ba tare daya shirya mata ba, wala mai kyau wala akasinta, sai dai Zeenat ita ta yakicowa kanta mummunar ƙaddarar da mayar da ita rabi mutum rabi dabba. Ablah musaka ce, tana da dogayen hannuwa sai dai dungulmi ne, ma'ana b...