Page 34

110 4 0
                                    

*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
   𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_

Page 34

Ji ya yi kansa ya fara juyawa, yana so ya tuna wani abu amma sam ya kasa tuna menene. Zama ya yi kan kujera tare da dafe kai.
"Doctor lafiya kuwa?"
Kai kawai yake girgiza masa, a take a gurin kuma ya sume.

_Few minutes later_

A hankali ya buɗe idanunsa da suka masa nauyi sosai, ya kalli ɗakin da yake ya gane doctors room ne, an saka masa drip. A hankali ya tashi zaune, ya kai hannu ya zate drip ɗin sannan ya fita daga ɗakin. Ya haɗu da 'yan uwansa Likitoci suna ta jera masa sannu, haka dai ya wuce ya nifi ɗakin da Ablah take, har lokacin tana nan yadda ya barta, tana ta bacci kawai, yana kallon yadda take numfashi ya gane cewa numfashin ta baya fita yadda ya dace.

So yake ya tuna ko wace ce, ko kuma wata alaqar da ta haɗasu, amma ya kasa gane komai.

Fita ya yi ya kira Doctors ya kuma bayar da umarnin a fara mata first treatment, yana gama faɗa kai tsaye ya nufi gida.
Tunda ya shigo Mom ta hango shi ta sama, yadda ya fito yana tafiya ta san ba lafiya ba. Ranar Diana ma tana gida kwananta biyu mijinta ya yi tafiya zuwa wata ƙasar.
"Mommy lafiya?"
"Naga Irfan ya shigo a hargitse, ban tunanin lafiya" Tana gama faɗa taji door bell, tabbas kam ta san shi ne, da sauri ta ƙarasa ta buɗe masa.
"Irfan lafiya?"
Kallonta ya yi idanunsa sun yi jajir, kawai ya wuce ya zauna ɗaya daga cikin kujerun tare da riƙe kansa ta yake ji yana masa barazanar tarwatsewa.

Mommy ta sauri ta ƙarasa ta zauna, tare da dafa kanshi, taji zafi sosai. "Baka da lafiya kuma ka baro asibiti, meyesa baka kira Doctor ya dubaka ba."
"Mommy bana buƙatar wani Dr ku faɗa min ni wanene? Akwai wani abu da yake rayuwata ina so na tuna amma sam na kasa, Mommy yau na ga wata yarinya muna kama sosai kuma ance min daga Nigeria aka kawo ta, Mommy ko dai mun taɓa zaman Nigeria?"
"Irfan kada ka nemi ka takurawa kanka, dan ka haɗu da mai kama da kai ba yana nufin kana da alaqa da ita ba, kada ka manta fa a duniyar nan kowa yana da mai kama dashi guda 7, to ka ga kuwa ba abin mamaki bane"
Shiru ya yi jin abinda ta ce, dan har ya manta da wannan. "To amma Mommy tun kafin ma naga wannan yarinyar ina yawan jin kamar akwai wani abu dana manta a rayuwata, a times ina son tunawa amma kuma sai na kasa."
"Dalilin daya saka Dad ɗinku ya ɗaukar ma Doctor na musamman da yake duba ka, kana da matsala ne a brain ɗinka"
"Mom ni da babban likita ne, taya ni na kasa ganowa?"
"Saboda abin a kanka yake, shiyasa consultant yake dubaka"
Ajiyar zuciya ya sauke kawai.
Sai lokacin Diana ta ce "Ya kamata ka samu kaje ka kwanta ka huta"

Miƙewa ya yi, jikinsa a sanyaye ya shige ciki, duk suka bi shi da fuskar tausayi.

                             ********

Kallonsu kawai yake ya kasa cewa komai, sai dai idanunsa da suka kaɗa suka yi jajir. "Mommy dan girman Allah kar kuyi haka" Sabrina ta faɗa tana kuka. Itama Mommy hawaye ta goge, ta janyo Sabrina ta rungume, lokacin kuma aka ɗauki Nabil za a wuce dashi. Juyowa ya yi a fusace ya shaƙe wuyan Salim, duk da da ciwo a hannunsa amma hakan bai hanashi damƙarsa ba.
"Sai na kashe ka, na tsaneka" Ya furta a haukace.
Da ƙyar aka ɓamɓare shi daga jikin Salim.

"Ku ɗaure shi saboda komai zai iya faruwa" Cewar Salim, yana ta shafa wuyansa.

Ana tafiya da Nabil Sabrina ta zube a gurin ta fara kukanta a fili, Amal ma hawaye ta goge ta fara ƙoƙarin ɗago Sabrina, da ƙyar suka iya fitar da ita Salim na ta masifa.

_Washe Gari_
*_09:30am_*

Kamar wadda ƙwai ya fashewa a ciki haka ta sauko daga upstairs, dukkansu suna dinning area suna breakfast, sai dai ta ga Mommy ta kasa cin komai, kawai tana zaune ne tayi shiru.
A parlour Sabrina ta zauna, taja throw pillow ta ɗora kanta, wasu zafafan hawaye ne suka saukar mata, kawai ta miƙe a fusace.
"Haba Mommy wai mene Nabil ya yi muku da zaku kai shi gidan mahaukata ku rufe, dukansu fa ake acan"
Mommy tasowa tayi daga dinning area ɗin ta ƙarasa gaban Sabrina.
"Zauna mu yi magana"
Hannu ta saka ta goge hawaye sannan ta zauna.
"Duk wanda zai so Nabil a bayana yake Sabrina, ba zan taɓa yin abinda zan cutar da Nabil ba"
"Mommy Yaya Salim ba gaskiya ya faɗa ba, wallahi Nabil yana da hankalinsa Mommy, taya mara hankali ya san ya yi visa, kuma ko baya da hankali bai cancanci a kulleshi ba har a gidan mahauka, Mommy ina laifin ma a kira Doctor ya riƙa duba shi a gida, haba Mommy kawai dan ya sayar da haƙƙinsa, akwai yaran da sata ma suke yiwa iyyensu fin abinda Nabil ya sata sai ace hauka ne suma?"
"Su idan sun sata ai gina kansu suke ba gina wani ba"
"Mommy shi ma ceton rai ya yi" Ta furta da tsawa.
"Ni kikewa tsawa Sabrina?"
Cikin kuka da kwantar da murya ta ce "Kiyi haƙuri Mommy ban san nayi ba, amma dan darajar annabi ki bani dama na bar garin nan, Mommy ba zan iya zama ina kallon wannan abin ba ba zan iya jura ba"
Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta koma kujerar da Sabrina take "Na san kina jin zafin abin saboda shaƙuwar da kuka yi amma ba zai daɗe ba, wata ɗaya kawai zai yi a gurin, idan muka ga ya warware sosai za a sake shi, kuma ba za a dakeshi ko a hanashi abinci kamar yadda kike tunani"
"Ni na san Nabil ba mahaukaci bane"
"Kiyi haƙuri" Ta furta tana ƙara rarrashinta.

RAINA FANSA(Complete)Where stories live. Discover now