3

558 54 0
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

      by maman shureim
              🌺sad-nas🌺

*©Pure Momment Of Life Writers*

here is a page for you miemiebee,Allah yabar zumunci ameen❤🌸

Page 3
Dukda cewa Farhan ya janye jikinsa,amma sam mubinat tak'i sakeshi. "Sis mubee ga mijinki yazo,kije ku tafi."
"Bazan jeba,dan Allah ka kyaleni Ya farhan kadena tayar min da ciwon zuciyata kabarni in kasance tare dakai koda na wannan lokacinne,inama da Allah zai d'auki rayuwata ayanzu,danafi kowa farinciki domin ina tare dakai habibina."
  Murmushi yayi tare da janyeta daga jikinsa yace "kinsan me kike cewa kuwa,matar aurece ke ayanzu kuma kina rungume da wani taya zakiso Allah ya d'auki ranki sis mubee,haka babu kyau karki sake fad'an hakan kinji?" Tundaya fara maganar take kallonsa tana hawaye,sedaya gama tace ai duk nasan wannan Ya farhan,koka mance ka koyar dani a islamiyya,kawai dai ahalin da nake cikine yanzu babu wani abu danyi inji dad'i hakan."
Ajiyar zuciya yayi yace "nafahimceki,amma fa shi bawa ana sonshi da tawakali da kuma imani aduk lokacin da Allah ya jarabcesa,dan haka kiyi k'ok'ari kicinye wannan jarabawan kamar yadda kike cinye jarabawan makaranta kinji?"
  Ido ta k'ura mishi tareda cewa cin jarabawan makaranta,ya akayi kasan hakan bayan baka iya gane koni wacece agurinka? K'irjin Ya farhan ya buga sosai danya so ya kwapsa,seyai saurin wayancewa yace "em ai shureim yana gayamin koma akanki shiyasa,ya k'are maganar yana murmushi,ita kuwa kallonsa kawai takeyi bata ko kyafta ido.
"Hannunta ya kamo batare dayace komai yakaita hargun da atif yake tsaye,sannan ya kamo hannun atif yayahad'a danata tace ga sis mubee a damk'amaka ita atif,dan Allah ka rik'eta da amana,sannan kayi hak'uri daduk wani abu dazata maka,ka d'aukeshi amatsayin yaranta nasan watara zata dena."
  "Ke kuma sis mubee kisani aljannarki tana gareshi tun lokacin da aka d'aura muku aure,dan haka zab'i yana gareki, kisani miji ya wuce iyayenki a yanzu,dan shiyake da iko dake ba iyayenki su sunriga dasun gama nasu,dan haka kiyiwa mijinki biyayya kicire komai aranki hakan shizaisa kusami zaman lfy kinji k'anwata"
  Duda dai mubinat tana cikin wani hali,amma kalaman farhan sun ciga jikinta sosai wanda yake k'ara fito da kwalla daga idanunta,nagode tace dashi cikin muryan kuka sannan ta janye hannunta daga nasu ta fita da sauri tana kuka.

Ahmad yasan kawai farhan daurewa yayi amma akwai ciwo babba azuciyarsa. Shi kuwa atif godiya sosai yayi sannan yabi bayan mubinat.
Fad'awa kan gado farhan yayi yana zubar da kwalla tare da fad'in "innalillahi wa inna ilaihir raji'un" ahmad ne yayita dannansa harya d'an samu sa'ida sannan sukaci gaba da shirya kaya.

Tunda mubinat ta koma cikingida aikin kuka kawai takeyi,dan tabbas maganar Ya farhan gaskyace,sannan tasan koda wasa Ya atif bazai tab'a rabuwa da itaba,dan haka taci kukanta harta godewa Allah. Nasiha sosai abbanta yayi mata hakama umma,shi kuwa shureim tayata kuka yakeyi yana cewa "sis mubee dan Allah karki tafi kibarni,rungumesa tayi sunata kuka dan tana mugun son k'aninta kuma autansu fiye da kowa aranta,da kyar aka rabasu sanan aka wuce da amarya gun motocin da suke jere acikin gidansu.
  Motoci ba'a magana,duk dadai masu karatu basusan waye atif ba,amma kuci gaba da biyoni zan warware muku komai.
  Motar da akasa amarya sabuwce dal,dama musamman yasayeta dan d'aukan sis mubee nashi kuma amaryansa. Abokinsa mansur ne kejan mota amal tana gaba se kuma mubinata da yapendoninta biyu abaya.
  Hmmm gidan amarya sedai muce masha Allah base nayi bayaniba,koma dakomai ansa,bayan sun shiga yapendoni suka sake mata fad'a dama ance babu wanda zai kwana agidan se k'awayenta guda biyu kamar yadda abba ya tsara wato amal babbar k'awarta kuma aminiyarta se kuma k'anwar atif wato aisha.

  Bayan an maida kowane se ango da abokansa 'yan rigima sunata k'orafi wai ba'ayi event ba ko guda d'aya ai biki baiyiba kenan. Ati ya fusa yace "wai meyasa kukemin hakane,kunfi kowa sanin yadda akayi auren amma kuma kuke k'orafi i hate this wlh." Mansur yace sorry man bai kamata ango yana fushiba come down tsokanarka muke,but idan komai ya daidaita atsakaninku dolene mu had'a party. Wani wawan kallon ya watsawa nabil tare da wucewa ciki suka bishi a baya.
   Nanma bawani dad'ewa sukayiba baya sun ajiye musu abin ciye ciye sannan sukayi sallama suka tafi.
Gida ya rage ango da amarya se kuma amal da aisha,duk cikinsu babu wanda yace komai kowa yayi shuru,amal tace aisha ina zamu kwanta ne dan gaskya nina gaji bacci nakeji. To nan dai d'akintane cewar aish,sedai muje d'aya d'akin. Babu inda zakuje,duk anan zamu kwana.
Amal tasan halin mubinat,dan haka bata tsaya jayayyaba kawai ta gyra kwanciyarta se bacci. Aisha kuwa cewa tayi "mubinat kinsan dai ni k'anwar Ya atif ce uwa d'aya uba d'aya,kuma kinsan naso aurenki da Ya farhan 100% amma Allah baisa shine mijinkiba,dan haka dan Allah kimance da baya kirik'eshi da amana pls mubinat,Ya atif yana miki k'aunar da komai kikace kina so zaiyi amma fa bazai iya sadaukar dake ga waniba.
Mubinat tayi kuka harta gaji dayin kukan dan haka tayi shuru tare da cewa aisha to.
Tabbas tasan aisha tana sonta sosai,dan haka ta mik'e tare da cewa aisha "kuci abinci mana, dan kuma bakuci komaba,bari naje na watsa ruwa."
  Aisha taci ta k'oshi sannan ta kwanta. Bayan mubinat ta fito ne ta goge jikinta kawai sannan tasa doguwar riga itama ta kwanta,kuma yunwa takeji sosai danko karyawa batayiba.

Shikuwa atif yana can shi kad'ai yanata kiran number'n sis mubi amma ba'a d'auka dantabar wayan acan gida cikin walldrop nata. Number'n amal ya kira akashe,dan haka ya fito daga d'akinsa zuwa nata,abakin k'ofa ya tsaya yana nocking tare da kiran sunanta "sis mubi" ahankali yake kiran sunan. "Na'am ta amsa tare da tunanin mekuma yazoyi?"
Komawa yayi hanyar zuwa d'akinsa,koda ta bud'e bata ganshiba seta hangoshin nesa da ita. Bayan ta rufo k'ofarne tanufi inda yake tsaye tace "gani." Hannunta ya rik'o tare da janta a hankali seta janye hannunta ta tsaya cak tare da b'ata rai.
  Matsowa yayi inda take ya sake rik'o hannunta yace "kiyi hakuri magana zamuyi yanzu zaki koma" hakan yasa tabishi a baya har suka shiga d'akinsa.
   "Kiyi hak'uri ki zauna pls"
"Ni bazan zaunaba"
"Y?"
"Bakomai"
"To shikenan ni bari in mik'e,hakan yamiki?"
"Silent"
Hannunta ya rik'o "sis mubi yunwa nakeji,nasan kema bakici komaiba pls kizauna ga yogot na kawomiki dan nasan kina so."
Bamusu ta zauna ahankali dan gaskiya tana jin yunwa sosai. Dad'i yaji,dan haka ya d'auko tare da cips da sauransu ya ajiye agabanta yace"indinga baki?" Kai ta girgiza masa alaman a'a,"to bisimillah kifar ci."
Hannu takai kan yogot d'in,seyace barina bud'e miki,mik'amata yayi tasha sata ajiye ta fara cin cips d'in shima haka.

Bayan tajci ta k'oshine setace "nizanje in kwanta"
"Ok kijira ingama se'in rakaki."
Shuru tayi tana kallon gefe harya gama sannan ya mik'e tare da kamo hannunta yace "tomuje."
  Yana rik'e da hannunta har suka isa k'ofan d'akinta sannan ya sake rik'o d'ayan hannunta ya janyota jikinshi ahankali tafad'o a jikinsa,seya rungumeta da hannayensa biyu.
Karon farko kenan da hakan yafaru da yardanta,dan haka setaji wani iri. Magana taji yayi cikin wata irin murya mai kashe jiki yace "I love you sis mubinat,i luv u so much tare da sake matseta a jikinshi." Ita kuwa seta fara kwalla tana tuna Ya farhan. Ahankali ta janye jikinta daga nashi tace "seda safe" sam yak'i sakin hannunta duka biyu yana rik'e dasu,ita kuwa seta sunkuyar da kanta tak'i kallonsa,sake matsowa yayi dab da ita ya rik'o fiskarta tare da manna mata kiss a lips nata yace "Allah ya tashemu lfy" da sauri ta shige d'aki sannan shima ya tafi zuciyarsa cike da farinciki...

Vote and comment

                       Team KNJ

KOMAI NISAN JIFAAWhere stories live. Discover now