31

315 20 0
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

       by maman shureim
              🌺sad-nas🌺

*©Pure Momment Of Life Writers*
         We don't just entertain and educate,we also touch the hearts of the readers💐







Page 31

    ASALIN LABARIN

Alhaji Bakari sanannan mutum ne sosai a garin Gombe,sabida arziki da Allah ya bashi.
Matarsa d'aya ce tak mai suna Hajiya Aisha. Yaransu ukune kacal a duniya,Maza biyu da kuma Mace.
Muhammad shine babban d'ansu na miji,se kuma Abdullahi,sannan Amina itace autarsu.
Haka suka tashi cikin gata da samun kulawa agun iyayensu har suka girma.
Kansu a had'e yake dukkansu,kuma suna son junansu sosai.
Shi Abdullahi ya fisu sakewa sosai da mutane,hakan yasa shiya fisu jama'a inda ya had'u da wani mai irin sunanshi shima Abdullahi har suka k'ulla abota sosai kowa yasan da zaman abotarsu harma aka zama kamar 'yan'uwa duk familys ansan juna sosai ana zumunci mai k'arfi.
  Wata rana aka tashi da rashin mahaifinsu wato Alhaji Bakari. Babu ciwo babu komai kwanane kawai ya k'are.
Matarsa Hajiya Aisha da yaransa ukun sun shiga wani irin hali na rashin Mahaifi sosai.
Bayan anyi arba'inne aka raba musu gadonsu inda suka samu kud'ad'e masu yawan gaske da gidajen mai da manyan filaye.
Dukkanninsu sunyi karatun boko mai zurfi. Haka sukaci gaba da zama tare da mahaifiyarsu har suka kammala karatunsu. Dama shi Abdullahi aboki suna gama secondary school ya samu kyautar karatu wani uncle nashi ya biya mishi acan Madina,inda shine sanadiyan rabuwansu da amininsa Abdullahi Bakari,amma koda yaushe suna manne a waya.

Lokacin da dukkansu suka gama kararune shi Babban Yayansu Muhammad yayi aure tare da matarsa jamila. Shi kuwa Abdullahi ya auri Maryam duk a cikin garin gomben. Ita kuwa Amina a Yola tayi aure inda take zaune lafiya har Allah ya bata ciki lokacin haihuwa Allah ya karb'i abinsa,daga ita har babyn'ta suka rasu.
Bayan rasuwarta da shekara d'aya Jamila matar Muhamma ta haifi d'anta na miji mai suna Mustapha,ta sake haifan Abdulhamid sannan Mijinta ya sake k'ara aure inda ya auri bafulatana a cikin gomben mai suna Khadija.
Shi kuwa k'aninsa Abdullahi har yanzu shuru Allah bai bashi haihuwa ba,inda abokai suketa bashi shawaran ya k'ara aure amma sam yak'i saboda yana son matarsa sosai suna zaman lafiya.
Abokinsa Abdullahi dake Madina kuwa acan ya samu wata balarabiya suna son junansu matuk'a dan tare suke karatu acan Madinan. Koda yazo mata da magan aure ta sanar da iyayenta amma sam sukak'i amincewa wai bazasuba d'an Nigeria auren 'yarsu ba.
Salma Taimoor 'yar wani Attajiri ne sosai a k'asar Madina,dan kaf familynsu ma manyane suke aurensu acan d'inma.
Haka dai akaita fama da iyayen Salma,ita kuwa tace sam babu wanda take k'auna se Abdullahi.
  Ganin babu yadda suka iyane yasa akayi musu aure,da yake shima Abdullahi ba laifi suna da hali suma amma an kafa mishi dokoki kan cewa 'yarsu salma bazatayi nisa dasuba dan haka suka mallaka musu tapkeken gida a garin Madinan acan suke zaune lafiya da matarsa.
Lokacin da khadija matar Muhammad ta haifi d'anta namiji mai suna Ra'is da kwana biyu Salma matar Abdullahi ma ta haifi d'anta mai kama da ita wato Farhan.
Tun daga lokacin shi Abdullahi Bakari ya shiga damuwa ganin har yanzu Allah bai bashi haihuwa,dan haka sukaje gurin Doctor domin a dubasu ko matsalar daga garesune. Bayan an gama dukkan gwaje gwajene sakamako ya fito cewa dukkanninsu lafiyarsu k'alau babu mai matsala a cikin su.
Jin hakanne yasa Abdullahi da matarsa hankalinsu ya kwanta,yayi alk'awarin bazai k'ara aureba tunda dukkansu lafiyarsu k'alau.
Haka dai sukaci gaba da zamansu cikin soyayya,da kusan shekara uku sannan khajida ta sake haifan d'anta namiji mai suna Atif.
Wannan yaro yaga gata kamar shine na fari a gunta,idan ka ganshi bakace d'ansu bane dan daban ya fita da sauran yaran.
Lokacin tafiya Umrah Abdullahi da Matarsa Maryam tare suka tafi daga can suka ziyarci gurin Amininsa Abdullahi Abban Farhan.
Maryam tana ganin Farhan seta fashe da kuka sabida yadda take son haihuwa amma Allah bai basuba har yanzu,satinsu guda agun amininsa sunyi zaman dad'i sosai gashi itama matar tashi akwai fara'a a d'an wannan kwanakin suka saba sosai har suka dawo Nigeria.
 
Su Farhan suna da shekara goma sha uku shida Ra'is inda Atif kuwa yakeda shekara goma a duniya Maryam matar Abdullahi ta samu ciki.
Murna agunsu baya misaltuwa duk wani son duniya an d'aurawa cikinnan,hakama k'awarta aminiyarta zainab ita se'a lokacin tayi aure dan ta tsaya karatu tana aure ta fara aikinta kud'i sosai take samu dan tama fi mijin nata arziki.
Cikinsu yana da wata hud'u suka gama sayayyan komai da komai da za'a buk'ata sudai kawai haihuwan suke jira yazo.
Ita zainab k'awartan bata fiye shiga harkan mutane ba,amma tana da son jama'a sedai duk cikin k'awayenta tafi son Maryam sun shak'u sosai.
Haka akaita renon ciki,su Atif kuwa sunata karatu har cikin yakai watan haihuwa anan ne Maryam ta haifi 'yarta mace son kowa k'in wanda ya rasa taci sunan kakarta Hajiya Aisha inda ake kiranta da Mubeenat.
Hmm! Bazan iya bayyana muku irin gata da wannan 'yar tashaba,saboda kaf dangin babu 'ya mace se ita kuma dama an dad'e ana fatan Abdullahi ya samu 'ya ko d'a a duniya se gashi an samo mace.
Hakanne ma yasa Atif ya Fara kiranta da Sis Mubeenat dan yana son yara tun tashinsa. Bayan wata d'aya k'awarta zainab ma ta haifi 'yarta mace mai suna Amal,itama dai tasha gatan sosai.
Suna da wata takwas Mahaifiyar su Atif ta sake samun ciki inda ta haifi macen itama aka sa mata sunan kakanta Aisha wanda hakan ake kiranta da shi har yanzu.
Tun daga lokacin babu wanda ya sake haihuwa a cikinsu dama ita Mahaifiyar su Ya Musty kam ta gama haihuwar ta,itama kuma Mahaifiyar su Atif ta gama.
Ita dai Maryam Umman Mubeenat tana so ta sake wani haihuwan amma shuru har seda Mubeenat takai shekara sha uku kafin ta sake sanun ciki inda ta haifi d'anta namiji mai suna Shureim.
  Tana cikin jegonsane sark'ewar hak'ori ya kamata wanda shine sanadiyarta na barin duniyar. Idan kaga mubeenat dole ka tausaya mata saboda sun shak'u sosai ga soyayya da kulawa da ake nuna mata.
A lokacin ne Amininsa Abdullahi sukazo Nigeria tare da Matarsa Salma Taimoor da kuma d'ansu tilo wato Farhan.
Koda yaga Mubeenat tana kuka seyaje kusa da ita yana mata maganan cikin harcen larabci ko kallonsa bata yiba. Nan ya tuna da abinda Abi nasa ya gaya masa "Idan mukaje k'asarmu hausa zaka dinga yi musu tunda na koya maka kaji?"  
Nan yace da ita "Meya faru kike kuka?"
D'agowa tayi tana kallonshi cikin mamaki "Kai waye?"
"Farhan"
"Daga ina kake?"
"Daga Madina muka zo da abi na gaisuwan rasuwa"
Nan ta sake fashewa da kuka inda Farhan ya rud'e tare da rik'o hannunta "Kiyi shuru ki dena kuka zan baki choculate na kawo miki dewa"
"Ka sakeni bana son choculate d'in kanaga Ummana ta rasu ta barni ni yanzu bani da Umma"
Tausayinta ya kama Farhan nan ya rik'o hannunta zo muje in baki kyautan Ummi na kina so?"
Kai ta d'aga mishi alamun eh. "Toki shiga ciki ki dena kuka zakiga wata mai kama dani kice mata Farhanne ya turoki"
"To" sannan ta wuce yana binta da kallo...

                             Team #KNJ

KOMAI NISAN JIFAAWhere stories live. Discover now