58

391 32 3
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

      by maman shureim
             🌺sad-nas🌺

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
    ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛ'Ş❤

#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com

NOTE
Masoyana da kuma followers d'ina a wattpad ina mai baku hak'uri dan account nawa na wattpad da kuka sanni dashi mai @Sad-Nass ya samu matsala kuma bana amfani dashi a yanzu,amma na sake bud'e sabon account zakuga pix d'in MUBEENAT ajikin cover'n sannan da @Sadnass na bud'e account d'in,dan haka ina mai sake baku hak'uri daku sake following d'ina ta sabon, and pls karku manta da  voting d'ina har dama comment.
       🌹I LOVE YOU ALL🌹


      Page 58
Samira kuwa ranar bata nan taje unguwa dan haka batama san abinda yake faruwaba,hakama shi Abban Amal ba'a sanar dashi ba dan baya nan kuma number'n shi baya shiga.
Atif kwance yake yanata kiran number'n Mubeenat amma bata d'agawa,dan haka yasa Aisha ta kirata shima k'in d'agawa tayi dan tasan duk shine. Amma a cikin ranta tausayinsa take sosai,dan takan tuna rayuwarsu na baya.
Wayarta ce ta sake yin k'ara,tana dubawa sai taga Ya Farhan ne da sauri ta d'aga tare da cewa "Assalam"
"Wa'alaikis salam"
"Ya Farhan ina kwana?"
"Lfy k'alau ya jiki yasu Umma?"
"Alhamdulillah kowa lfy"
"Na kira wayan Abba dana Umma duk baya shiga,ki sanar dasu cewa mun taso"
"To insha Allah,Allah ya kare ya kawoku lfy"
"Ameen Ahmad yace agaisheki da jiki"
"To nagode agaishe shi"
"To zaiji sai mun iso"
"Ya Farhan?"
"Na'am"
"Wai fushi kake dani ne?"
"Na isa? Ki bari idan muka tsaya zan kira"
"To shikenan dama na d'auka ko fushi kake,tunda ba haka bane ba komai Allah ya kawoku lafiya"
"To ameen nagode."

Dad'i Mubeenat taji dan ita duk a tunaninta fushi yake da ita.
Gun Umma ta wuce ta sanar da ita sak'on Ya Farhan,sannan suka tsunduma kichine domin shirya abinci.

5:12pm su Farhan suka iso har k'ofar gidan su Amal. Da gudu ta fito ta rungume Ummanta suna kuka,su Mubeenat ma ba'a barta a baya ba tazo ta rungumeta tare da 'yar k'walla tace "Mun godewa Allah daya dawo mana dake Umma"
"Sannunku Mubeenat,baki da lafiya ne? Naga duk kin rame"
"Eh amma naji sauk'i" sannan ta d'auki kaya ta wuce dashi ciki.
Bayan an gama shiga da kayanne su Farhan suka koma can gida domin su d'an watsa ruwa kuma suci abinci,Ahmad dai yak'i zama dan haka ya wuce gida shima.

Mubeenat ta d'auki abincin su Umman Amal takai musu harda shi Malam Buba da aka sauk'eshi a parlour'n Abban Mubeenat.
6:00pm saiga Samira da Sagir sun dawo daga nasu damuwar batare da sun san abinda yake faruwa ba.
Ai kuwa suna shiga sai sukajiyo murya anata hira,wa zasu gani? Umman Amal ce zaune ita da Umman Mubeenat ga kuma Amal Mubeenat da Shureim ana zazzaune anata hira. Ai daga Samiran har Sagir sake matsowa sukayi dansu tabbatar da abinda idanunsu yake nuna musu,suna had'a ido Samira ta fad'i sumammiya wanda yayi dai-dai da shigowan Abban Amal dayake Abban Mubeenat ya kirashi yace lallai yazo gida yanzu.
Da sauri ya k'arasa ya d'ago Samira yana jijjigata tare da cewa Sagir "Tome ka tsaya kanayi yi maza-maza kabani ruwa"
Sagir kam ai sayya fara cewa "Shikenan,wlh shikenan komai ya lalace tunda ta dawo"
Cikin rashin fahimta Abban Amal yace wa kenan?"
Sagir ya nuna Umman Amal da yatsan hannu yace "Gata can,dama Malam na ruga ya fad'a min wlh indai ta dawo to komai ya k'are asirinmu ya tonu kenan"
Abban Amal saiya tsaya ganin Umman Amal kamar wani zombi.
Shi kuwa Sagir saiya hau fad'e-fad'e kamar an tambayesa ya basu labarin abinda ya faru tun daga farko har k'arshe.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" aketa maimaitawa agun. Duk daya gama basu labari saiya d'aura da cewa "Ganin bata samu cikin bane yasa na bata shawaran neman wani Namijin a waje domin ta samu ciki muce naka ne,shine ta had'u da wani saida suka gama duk abinda zasuyine yake sanar da ita cewa yana d'auke da cutar k'anjamau yanzu haka daga asibiti muke kuma an tabbatar da cewa tana d'auke dashi itama.
  Abban Amal dake rik'e da Samira a jikinshi ai saiya saketa a k'asa yana "Allah ya isa tsakanina daku bazan tab'a yafe mukuba wlh"
Umman Mubeenat ce ta mik'e tare da d'ibo ruwa ta yayyafawa Samir,cikin wasu mintina kad'an ta farfad'o tana zazzare idanu tare da binsu da kallo.
"Tashi ki tattara komatsanku kubar min gida na sakeki saki Uku Samira,sannan wlh Allah ya isa tsakanina daku bazan tab'a yafe muku ba azzalumai kawai kun cutar dani da mamata harma da 'yata wlh dolema Allah ya d'aura miki wannan bala'in tashi ku fita nace!"
"Dan Allah kayi hak'uri nicefa Samiranka ka yafemin,idan ka koremu ina zamu je?"
Ai baima jira ta gama fad'in abinda take cewaba ya wuce ya d'auko wani igiya ya fara zuba mata kamar wani tsohon mahaukaci ita kuwa sai ihu take kamar jaka,shi kuwa Sagir d'aki ya wuce ya kwashi kayansa ya fita da gudu dan yasan idan ya shiga hannu tofa zaisha wahala sosai.
Umman Mubeenat ce taketa bashi hak'uri amma ina baya sauraron kowa duka kawai yake,ganin hakanne yasa Shureim zuwa gida ya sanar da Ya Farhan dasu Abba.
Ai cikin sauri suka shigo harda Malam Buba sannan fa aka samu aka ceci Samira data zama kamar wata mahaukaciya duk ta yaye kayan jikinta da birgima har pant nata ana hangowa gashi bulalan ya kwanta a jikinta rad'a-rad'a.
Mubeenat da Amal sai dariya sukeyi tare da cewa "Dama ai mun tab'a gaya miki Samira KOMAI NISAN JIFA lallai k'asa zai dawo,jifanki rayi nisa sosai wanda har muke tunanin kodai bazai fad'o bane,sai kuma gashi ya dawo."
Sam babu wanda ya dakatar dasu saida suka mata tass! sannan suka wuce d'akin Umman Amal suna k'arasa gyare gyare da Amal ta fara bata k'arasa ba.
Abban Mubeenat yace su shiga daga ciki tukunna ayi magana,amma Abban Amal yak'i fur yace ai babu sauran wani abu tunda ya saketa. D'akinta ya wuce ya d'ibo mata kayanta dama a had'e suke dayake bata da gaskiya ko jera kayan batayi a wall drop suna cikin akwatinta dan haka ya fito dasu yace ta kwashe tayi gaba.
Kuka takeyi tana bawa Umman Amal hak'uri da neman yafiya,Umman Amal tace "Na yafe miki Samira kije can kiyita fama da abinda kike d'auke dashi,sannan daga yau ki manta da cewa kinsanni a rayuwarki barema har kiyi tunanin sake zuwa inda nake."
Farhan ne ya fitar mata da kayanta har wajen gate sai ihu takeyi tana kuka kamar zararriya anan ya barta ya dawo cikin gida yayinda mai gadima yake zaginta iya son ran sa...

Vote and comment

                      Team #KNJ

KOMAI NISAN JIFAAWhere stories live. Discover now