57

389 34 3
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

      by maman shureim
             🌺sad-nas🌺

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
    ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛ'Ş❤

#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com

NOTE
Masoyana da kuma followers d'ina a wattpad ina mai baku hak'uri dan account nawa na wattpad da kuka sanni dashi mai @Sad-Nass ya samu matsala kuma bana amfani dashi a yanzu,amma na sake bud'e sabon account zakuga pix d'in MUBEENAT ajikin cover'n sannan da @Sadnass na bud'e account d'in,dan haka ina mai sake baku hak'uri daku sake following d'ina ta sabon, and pls karku manta da  voting d'ina har dama comment.
       🌹I LOVE YOU ALL🌹


Page 57
Shuru Mubeenat tayi tana tunanin kalamansa,ga dukkan alamu fushi yayi.
Ganin su Umma sunzo ne yasa Farhan komawa gida.
Mubeenat bata kwana ba aka sallameta ganin ta samu sauk'i sosai. Shi kuwa Atif yana can yana fama da nashi tare da jin haushin Farhan fiyema dana da.
Abba ya kirawo Farhan akan yazo ya maida su Mubeenat gida,koda yazo tambayarta kawai yayi yaya jikinta tace da sauk'i. Bayan nan bai sake ce da ita komai ba harya mai dasu gida yacewa Umma zai koma asibiti gurin Atif sannan ya fice.

Shima Atif kwanansa biyar aka sallamesu amma baya iya takawa saida wasu k'arafe guda biyu.
Doctors sun tabbatar da cewa zai samu lafiya da yardan Allah nan da wani lokaci.
Mum d'insa ce take kulawa dashi sosai a gida,amma duk ya rame saboda damuwa daya sawa ransa,ga rashin Sis Mubee ga kuma Farhan daya tsole masa ido.
Kullum k'ok'arinsa shine ya samu lafiya kamar yadda yake a baya dan a nashi tunanin zaije ya shawo kan Mubeenat.
Farhan kuwa tun maganan da Mubeenat tayi masa a asibiti saiya sauya mata kwata-kwata baya ma shiga harkarta iya kacinsu gaisuwa bayan wannan kuma shikenan.
Tun abun baya damunta har yazo ya fara damunta amma sam,bata nuna mishi saboda itama idda takeyi.

Yau tafiya ya kama Ahmad zuwa garin Zamfara wanda daga gurin aikinsu Ogansa ya aike shi. Suna zaune da Farhan yana gaya masa sai yace zai raka shi tunda kwana d'aya kawai zasuyi.
Suna zaune a parlour'n Abba ya shigo tare da sanar dasu cewa zasuje Zanfara shida Ahmad amma gobe zasu dawo insha Allah.
Sukai masa fatan alkhairi sannan ya fice suka tafi,zuciyoyinsu cike da k'una daga shi har Mubeenat.
A ko wace irin yanayine Farhan baya son abinda zai had'ashi da Mubeenat harma yayi baya-baya da ita,amma ya zama dole musamman ma yanzu da take cikin iddanta.
Kamar zata kirashi taji kosun isa lafiya sai kuma ta fasa domin ta tsare mutuncinta kar yaga kamar tana neman shishshige masa ne a nata tunanin.

Washe gari kafin su tasone Ahmad yaji kansa na tsananin ciwo,hakan yasa Farhan karb'an tuk'in ya kuma garzaya dasu asibiti mafi kusa dasu.
Bayan sunga Doctor an gama komai ne sannan aka bashi magunguna suka fito.
Dama Malam Buba ya kawo Umman Amal asibitin sakamakon ciwon ciki da yake damunta. Ai kuwa saita hango wata fuska daga nesa wanda ita dai tasan wannan fuskan a gidansu k'awarta wato Umman Mubeenat.
Nan ta tuna da cewa Farhan ne bak'in Madina,harsun shige mota suna shirin barin gurin sai tayi saurin sanar da Malam Buba, nan yayi saurin zuwa gun motar yana bubbuga da hannunsa ganin har sun fara tafiya.
Cak Farhan ya tsaya tare da cewa Ahmad "Lafiya kuwa,ina zuwa" sannan ya tsayar da motar tare da fito ya mik'awa Malam Bubu hannu suka gaisa.
"Bawan Allah ko kaine Farhan daga Madina wanda yake zaune a Gombe yanzu haka?"
Mamaki sosai Farhan yayi dan yasan shi bayida kowa a Zamfara.
"Eh nine,saidai ban ganeka ba?"
"Tabbas bazaka ganeniba amma zaka iya gane wannan matar?"
Juyowa Farhan yayi yana kallon Mahaifiyar Amal sosai. Nan yayita tunanin inda ya tab'a ganin fuskar,tabbas shidai bai santaba,amma ya tab'a ganin fuskar ta.
Nan ya tuno lokacin dasu Abba suke ta raba hotunanta harma a gidan TV.
Zare ido yayi tare da cewa "Umman Amal ce ko?"
Nan take ta fashe da kuka shi kuwa Malam Buba yace dashi "Kwarai kuwa ita ce"
"Allahu Akbar, Alhamdulillah" sannan ya juya da sauri ya koma gun motarsu tare da bud'ewa yace "Ahmad fito ga Umman Amal"
A firgice Ahmad ya fito yama nemi ciwon kan ya rasa yana bin inda Farhan yake da ido.
Tabbas wannan Umman Amal ce,dan kusan kullum saiya ga hotonta a wayar Amal. Nan ya sunkuya ya gaishe su cikin girmamawa suka amsa,sannan Farhan yace su shigo mota saisu k'arasa gida.
Haka kuwa akayi suka shige anata tattaunawa tun daga hanya yayinda suke ta mamakin bayanin da Malam Buba yake basu game da had'uwarsu da Umman Amal.

Zaune suke a tsakar gidan Malam Buba yana basu cigaban labarin har zuwa mafarkinta na shekaran jiya datayi. Yaci gaba da cewa "Dama yau zamuje garin Gomben,sai kuma ta tashi da rashin lafiya ashe kuma da rabon zata ganku ne"
"Allahu akbar,Allah mai girma da d'aukaka Allah maiyin yadda yaso a kuma lokacin daya so,Alhamdulillah gaskiya bansan wani irin farin ciki 'yan Gombe zasuyiba na dawowarki Umma,musamman Amal kullum cikin kuka take wlh"
Malam Buba yace "Ai dole tayi kuka yaro,kuka ya zama dole,amma daga yau ai kuka ya k'are sai kuma kukan farin ciki"
"To yanzu yau zaku koma kenan?"
"Eh dama yau zamu koma,amma zamu bari sai gobe inyaso saimu tafi gaba d'aya daku" cewar Farhan.
"Toh ba komai Allah ya nuna mana goben"
"Ameen" sannan Farhan ya kira Abba ya sanar dashi wannan abun farin cikin,yayita mamaki tare da murna harma ya had'asu da Malam Buba suka gaisa tare da tabbatar masa da cewa zasu taho gobe dasu Farhan.
Nan Abba yayita godewa Allah tare dayin murna  ya kuma nasar dasu Umma.
Amal da take kwance a gida sai taga wayar Ahmad,take ta d'aga tana cewa "Kun taso ne?"
"A'a bamu taso ba sai gobe insha Allah"
"Amma kasan ba haka mukayi da kai ba ko?"
"I'm sorry ina kuma tayaki murnan dawowar farin cikinki wato Umma,gata ku gaisa"
Amal bata gane me yake nufi ba dan haka tace "Me kake fad'i ne?"
Muryar Ummanta taji cikin kuka tace "Amal?"
K'irjintane taji ya buga take ta mik'e gami da dafe k'irji tace "Ummana kece kodai kunnena ne?"
"Nice Amal ba kunneki bane,nice dai Mahaifiyarki Amal d'ita"
Nan take Amal ta fara kukan farin ciki tana magana da mahaifiyarta cike da so da kuma kewarta har ji take inama da itace suke tare a yanzu ba Ahmad ba.

Hmmmm Allah sarki duniya,babu wani abu da yake dauwama har abada indai mutum ne yayi ba Allah ba.
Dukiya,mulki,arziki,tak'ama duk zasu k'are,idan kuma basu k'areba tofa lallai kai daka ajiyesu ko kake gadara dasu zaka k'are ka barsu watan wata rana.

ALLAH KASA MUFI K'ARFIN ZUCIYOYINNU AMEEN...

Vote and comment

                       Team #KNJ

KOMAI NISAN JIFAAحيث تعيش القصص. اكتشف الآن