24

338 20 0
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

      by maman shureim
             🌺sad-nas🌺

*©Pure Momment Of Life Writers*
        We don't just entertain and educate,we also touch the hearts of the readers💐

        🌷🌹🌷🌹
Sad-nas🌺 novel bazan tab'a gajiyaba gurin yimuku dedicating page saboda yadda kuke nuna k'aunarku a gareni,thankyou so much Allah kuma ya had'amu a aljannar fiddausi da sauran 'yan'uwa musulmai baki d'aya ameen❤❤❤💐



Page 24
"Gayamin damuwarka Ya Atif insha Allah zanyi iya bakin k'ok'arina inga cewa na baka shawara mai kyau akai"
"Sis Mubee i... se kuma yayi shuru
"Go on Ya Atif tell me" tana rik'e dashi tare dayi mishi murmushi.
Kallonta yakeyi sosai se kuma ya rungumeta "I don't wonna missed you love,zan zauna dake ko a wani irin hali babu wanda ya isa ya rabani dake my love right Sis Mubee?"
"Came down Ya Atif,me kake cewane babu wanda zai rabani dakai ka dena sa komai aranka domin kai nawane ni kad'ai mubar wannan maganan kawai bana so hankalinka yayita tashi."
Atif yayi k'ok'arin fahimtar da Mubee amma sam bata bashi damaba ta rungumeshi hakan yasa yayi shuru yabar zance.

Bayan isha suna kwance Mubee tanata gwada mishi irin soyayyar da take mishi,wanda sam shiya kasa sakewa sema k'ok'arin dakatar da ita da yakeyi amma ina Sis Mubee tayi nisa saboda a tunaninta wannan shine damuwarsa ga kuma nasihar da akai mata dan haka ita da kanta ta shige masa tun yana hanata harya sauya batare daya san me yake cikiba.
  Hmm Sis Mubee dai kusan ita ta shigewa Atif a daren yau,yayinda shi kuwa ya shiga wani irin yanayi wanda bazai iya dakatar da kanshiba bare kuma ya dakatar da ita,tun danaji yana karanta wasu addu'oi nima nayi saurin barin d'akin na tsaya daga waje ina sauraron abinda kunnena suke jiyomin, dukda haka Mubee taban tausayi sosai dan dagaji ta wahalu sosai.
Muryan kukan Atif danaji ne yasa nayi sauri komawa cikin d'akin,gabad'aya babu yadda suke musamman Sis Mubee.
"Sis Mubee i'm sorry" ya fad'a cikin muryan kuka. Hankalinta ya tashi sosai,meyake damun Ya Atif haka,shidaya kamata yayi murna kuma shine yake kuka,to kodai baiji dad'ina bane,nashiga uku ni Mubinat Abdullahi. Haka ta daure tare da matsowa inda yake ta rungumesa ta baya "Ya Atif lafiya,mesa kake kuka?" Cikin sauri ya juyo tare da kunna wuta mai haske ya rik'o fuskarta da jajayen idonsa "Bakomai Sis Mubee" se kuma ya rungumeta yana hawaye a b'oye.
Janye jikinta tayi tace "Dan Allah ya Atif ka gayamin wlh har kasa na fara tsarguwa kodai bakaji dad'in tarayya dani bane?"
Tausayi ta bashi sosai dajin hakan,murmushi yayi tare da goge k'walla yace "Wlh naji dad'inki 1milion% Sis Mubee please kiyimin alk'awarin bazaki barniba a ko wace irin hali na shiga please promise me?"
"Ka tabbata ka gamsu dani Ya Atif?"
"Sis Mubee da ina tunanin zan iya rabuwa dakene cikin sauk'i,but a wannan dare naji cewa bazan iya rabuwa dakeba,kuma babu wanda zai rabani dake ko my love?"
Murmushi tayi tana shafar fuskarsa "Ya Atif namaka alk'awari duk rintsi ina tare dakai babu wanda zai rabani dakai se mutuwa."
Ananne hankalin Atif ya kwanta,rungume junansu sukayi sosai sannan Atif ya mik'e zuwa toilet.
Wasu zafafan hawayene suke saukowa daga idanun Mubee "I'm sorry Habibi,duk tunanina shine in hana Ya Atif kaina dan gani nake kamar zan dawo gurinka ashe ba haka abin yakeba,Allah sarki Habibina Allah ya baka mata ta gari wacce ta fini da komai ameen."
Mubinat ta tsunduma sosai cikin tunani da zancen zuci,sam batajin abinda Atif ke cewa seda ya tab'ata "Sis Mubee,na had'a muki ruwa muje in miki wanka."
K'wallan ta share sannan tayi murmushin k'arfin hali tare da mik'a mishi hannunta. "Sis Mubee meya faru kike hawaye?"
"Ba komai nima haka kawai naji hawayen yazo min."
Ba tare daya sake cewa komaiba ya d'auke zuwa toilet.
Bayan sun fitone sukai shirin bacci suna manne da junansu.
"Ya Atif?"
"Yes my love"
"Gobe su Ya Farhan zasuyi taro zamuje ko?"
Atif bai isa ya hanata zuwaba dan yasan ta dad'e tana burin zuwan wannan ranan,dan haka yace da ita "Ofcause ai mune shuwagabanni a gurin,da wurima kuwa zamu fita"
Murmushi tayi tace "Thankyou" wayar sace taki k'ara,sunan Farhan ya gani akan screen nashi. "Hello Farhan"
"Em Atif,dama na kirane domin in sanar dakai da kuma Sis Mubee muna da taro gobe by 10:00am."
"Ok zamuzo insha Allah,ga Sis Mubee d'in"
"Ok"
"Ya Farhan,kayi hak'uri ban zamo d'aya daga cikin masu shirya wannan taroba wanda hakan baimin dad'iba,amma gobe zamuzo da wuri dan nima in samu koda balun ne in d'aura guda d'aya."
"Hhhh ai nida Amal da Ahmad mun miki naki aikin dan haka ki dena damuwa."
"To shikenan nagode,seda safe"
"Allah ya bamu alkhairi,emm Sis Mubee?"
"Na'am"
"Nayi farin ciki dana dawo gida na tarar bakya nan,Allah ya baku zaman lafiya."
"Ameen thankyou."
Bayan ta mik'awa Atif wayanne taketa tunanin hiransu a yanzu,idanunta ta rufe se bacci...

Washe gari bayan sunyi sallan asuba Mubee taji jikinta yayi nauyi sosai.
"Atif yace da ita suje hospital,amma sam tak'i paracetamol tasha sannan tad'an kwanta"
Kichine ya shiga ya dafa musu indomie da egg,sannan ya kira Farhan a waya ya bashi hak'uri akan rashin zuwansu har yanzu, Mubee ne bataji dad'in jikin taba amma yanzu zamu shirya mu fito,sannan ya wuce d'aki ya tasheta dan yaga 9:20am gashi ko wanka basuyi ba.
Ahankali ta tashi tana murza ido "Good morning my love" ya fad'a tare da d'agata se toilet ya wanketa tas sannan shima yayi wankan suka fito yana d'auke da ita kamar baby. "How are you felling now?"
Murmushi tayi tare dajin kunyarsa tace "I'm fine"
Murmushin yayi shima sannan suka shirya junansu suka wuce daining.
"Yaushe kayi girkin?"
"Kina bacci"
Bayan tayi spoon d'ayane ta kalleshi tare da cewa "Wooow! Your so sweet Ya Atif,gaskya nayi dacen miji wannan girki aikoni iyaka kenan,Alhamdulillah."  Sannan ta tashi ta rungumeshi tare da peck mai zafi a kumatunsa.
Hakadai sukayitayi suna  soyayyarsu har suka gama suka sake d'an kimtsawa,jan gawn ne a jikin Mubee da wani cream daga saman rigan zuwa hannun daga k'irjin rigan kuwa red ne da tsones bab'i se red 'yankunne da sark'a da kuma red gyale mai d'an black kad'an-kad'an ajiki tayi d'auri dashi akanta tasha kwalliya da red lips💋she looks... baridai inyi shuru idanunku zasuyi kallo,suka kama hanya se gurin taro.

Gurin taro ya had'u sosai se kallo inda kowa yasha wanka.
Farhan yana sanye da farin kaya tare da parmala black asaman farin kayan se hanki fari daga aljihun gaban parmalan yayi kyau sosai.
Kowa ya halarci wannan taro hardasu Abba,iyaye matane dai basu samu  zuwaba,Amal da Aisha ansha gayu sosai shima Shureim ba'a barshi a baya ba.
Su Atif suna shigowa aka juya kallonsu dan sunsha gayu sosai gyalen Mubee bisa kafad'arta.
Tun daga nesa Farhan ya hangosu tare da k'are musu kallo yana murmushi,cikin zuciyarsa kuwa shiyasan me yake ji.
Da gudu sukazo suka rungume Mubee suna murnan ganinta,itama murna sosai takeyi aka tsaya gaisawa.
Farhanne tsaye daga nesa yana mata murmushi itama tana mayar masa da nata.
Wucewa tayi zuwa inda yake tsaye tace "Congrats Sir" tana dariya
"Thankyou,how are you feeling now?"
Mamaki tayi sosai waya gayamishi bani da lafiya? "I'm fine" tace dashi
"You look beautifull Sis Mubee"
kunya taji tace "Thankyou and you too"
Sprying kawai sukaji akansu tare da flowers da ake zubo musu.
Gabad'aya kallo seya koma gunsu anata ihu da tapi,Farhan yayi saurin barin gurin ya kamo hannun Atif ya kawoshi gurin sannan ya koma gefe yana tafin shima yayinda jikin Mubee yayi sanyi...

Vote and comment for each page pls

                    Team #KNJ

KOMAI NISAN JIFAAOù les histoires vivent. Découvrez maintenant