19

353 27 0
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

     by maman shureim
           🌺sad-nas🌺

*©Pure Momment Of Life Writers*
        We don't just entertain,we also educate and touch the hearts of  readers💐

💐🌹💐🌹💐🌹💐
Wow! About 500 people reading my book on wattpad,i'm so happy you know😇 Thanks all for d luv nd care💋
  sadnas always love you more❤❤❤



Page 19
"Ya Atif please wake up" ruwa taje ta d'ibo a cup tana yayyafa masa sannan ta d'auki wayansa dake gefensa ta kira number'n Abbanta.
Babu b'ata lokaci ya d'auka suna zaune dukkansu a parlour ana gaisawa. "Salamu Alaikum Atif" Abba yayi magana,cikin muryan kuka Mubinat tace "Abba nice,ga Ya Atif nan kwance ya fad'i ko motsi bayayi dan Allah Abba kazo yanzu."
Cikin rud'ewa Abba yace "Subhanalillah,ganin zuwa" sannan ya katse wayar yace "Farhan tashi muje wai Atif ne ya fad'i ko motsi bayayi"
"Innalillahi" suka furta shida Umma harda Shureim sannan suka fita cikin hanzari suka nufi gidan.
Har lokacin Mubinat tana ta faman kuka gaba d'aya ta gama rud'ewa. Jin k'aran horn d'in mota tare da bud'e gate da akayi ne yasa ta mik'e zuwa bud'e k'ofa dan tasan Abba ne.
Fitowa tayi da gudu ta k'arasa gunsu tana cewa "Muje Abba yana ciki" gaba d'aya idan ka ganta zaka tausaya mata,dan kota kan Farhan ma bata biya.
Abba da Farhan a tare suke duba shi suga ko yana numfashi, tabbas yana numfashi, hakan yasa Abba cewa "Mamana ki kwantar da hankalin ki insha Allah babu komai,Farhan d'agashi muje asibiti."
Ganin haka yasa Mubinat shigewa d'aki ta sako hijabinta dama k'ananan kayane a jikinta.
Abba ne zaune da Atif a baya,ita kuwa seta shige gaba Farhan ya jasu se hospital.
Suna isa babu b'ata lokaci doctor ya karb'esu dama doctor'n sune. Cikin sauri aka wuce dashi domin gwadashi.
Bayan gwaje-gwajen da doctor yayi ne ya tabbatar da cewa jininsa ne ya haura sosai da kuma fever da yake d'auke dashi.
Mamaki sosai Abba yayi,don tunda Atif ya dawo gidansa da zama bai tab'a yin wani ciwoba,se kuma gashi yau ance jininsa ya hau? "Tome yake damun Atif haka dahar zaisa jininsa yahau har haka?"
Ba Abba kad'ai ba, hatta ita Mubinat d'in da Farhan tunanin da sukeyi kenan a zuciyarsu.
"Kodai k'in amincewa da banyi dashi bane tun farkon aurenmu yasa shi cikin damuwa har ya janyo mishi hakan? Oh no Ya Atif i'm sorry." Take fad'a a zuciyarta yayinda take 'yar k'walla a fili.
"Sis Mubee,ki dena damuwa zai samu lafiya insha Allah." Cewar Farhan
Kunya sosai taji daya fahimci ta shiga damuwa. "Thankyou" tace dashi tare da komawa gefe ta zauna akan farin kujera tana tuna maganar Farhan. Ta lura dashi sam baya so yaganta cikin damuwa,duk da cewa tana auren Atif a yanzu, amma baya iya b'oye damuwarsa muddin ya ganta cikin damuwa.
"Mamana akwai wani abu da yake damun Atif ne a baya?" Abba ya tambaye ta.
"A'a babu komai Abba"
"To nayi mamaki da abinda doctor ya fad'a ne akan Atif."
Shuru tayi bata ce komai ba.
"Allah ya bashi lafiya" cewar Farhan.
Suka amsa da ameen dukkansu.
Fita Abba yayi waje yana amsa wayan Umma. A hankali Mubinat ta matso inda Atif yake kwance ta zauna a gefen sa.
Shi kuwa Farhan idanunsa suna kanta,baisan me yasa ya kasa d'aga idanunsa daga kanta ba.
  Hannunta takai kan na Atif tana rik'e dasu tare da matso da fuskarta ta tsunbaci gefen fuskarsa tace "Ya Atif please open your eye i'm here"
Farhan baiji komaiba yasan yadda Mubinat takeji da Ya Atif tun farko,dan haka se yayi murmushi tare da cewa "Bari na baku guri ina daga waje" sannan yayi hanyar fita.
Yana dai-dai k'ofa tace "Habibi?"
Ahankali ya tsaya tare da mamakin sunan dayaji ta kirashi dashi. Juyowa yayi suna kallon junansu, fuskarta babu ko  murmushi tace "Thankyou" tare dayin k'walla.
Murmushi ya sakar mata sannan yace da ita "It's nothing Sis Mubee,i will do anything for both of you."
K'wallanne yaci gaba da gangarowa daga idanunta zuwa jikinta. Farhan bazai iya jure ganin hakan ba,musamman ma daya san dalilin zubowar su,da sauri ya fice daga d'akin.
Jikinta ta manna akan na  Atif tana kuka wanda ita kad'ai tasan dalilin yinsu...

Cikin k'ank'anin lokaci 'yan gidansu Atif suka hallara a hospital d'in. Mahaifinsa yana Umrah dan haka yayyunsa ne suka zo da kuma Mum nashi da Aisha.
Cikin jin kunya Mubinat ta gaishe su sannan suka fita waje da Aisha.
"Mubee,me yake damun Ya Atif?" aisha ta tambaye ta.
"Doctor yace jinin sane ya hau da kuma fever."
"Jininsa ya hau,to me dalilin hakan?"
"Wlh nima abinda nake mamaki kenan Aisha, na kasa gane komai."
"Mubee,nasan dai bakya son Ya Atif a matsayin mijinki,kuma shi Ya Atif yana matuk'ar k'aunarki wanda kema kinsa da hakan,Mubee hakan zai iya sashi cikin damuwa wanda zai iya haifar mishi da hawan jinin tunda yana sonki."
"Please Mubee ki tausaya mishi,duk yadda k'awancenmu take ko kuma 'yan'uwan takarmu dake ina so kisan cewa ina matuk'ar k'aunar Ya Atif sosai amatsayin shi na Yayana wanda muka fito ciki d'aya,dan Allah ki sassauta mishi haka tunda kinga ga abinda ya fara janyo mishi wanda nasan kece sila."
  Aisha tana kaiwa nan ta wuce cikin d'akin tabar Mubinat a tsaye duk jikinta yayi sanyi dajin kalaman Aisha.
Tunda suke hakan bai tab'a faruwa a tsakaninsu ba,sannan ita kanta Mubinat tasan duk abinda Aisha ta fad'a gaskiyane dan bata bin bayan k'arya ko wani son kai.
Cikin sanyi jiki itama tabi bayan Aishan wanda yayi dai-dai da farkawan Atif yana binsu da kallo. Haka suka dinga mishi sannu har idanunsa suka zo kan Mubinat.
Murmushi ya sakar mata tare da mik'a mata hannunshi alamun tazo, cikin jin kunyan su Mum dasu Yaya Musty se tace "Ya jiki?"
"Da sauk'i" ya bata amsa yana mai cigaba da kallonta.
Ganin hakan yasa su Mum fita waje. Daga su se Aisha ne kad'ai a ciki.
"Sis Mubee?"
"Na'am" ta bashi amsa
"Zonan ki zauna kusa dani"
Ba musu taje ta zauna ya rik'o hannunta tare da tsunbatar su sannan ya kalli Aisha.
Murmushi tayi mishi tace "Ya Atif a baka da lafiyan ma?"
"Aisha kinfi kowa sanin yadda Sis Mubee take aguna,shiyasa koda yaushe nake son injita a kusa dani."
"Murmushi ta sakeyi tare da cewa "To Allah ya barku tare,ya k'ara soyayya."
"Ameen Sister,thanks for d prayer"
"Mention not,zan je gurin su Mum ina dawowa" sannan ta fice.
Mubinat tanata binta da kallo da kuma tuna abinda ta gaya mata. Atif ne ya katse mata tunani da cewa "Hey,are you okey?" Tare da juyo da fuskarta suna kallon juna.
"Yeah i'm fine" ta fad'a tare da had'e lips nata da nashi suna kissing d'in junansu cikin jin dad'i.
A hankali ta saki lips nashi tace "I love you my hubby" tana kallonshi da murmushi a fuskarta.
"Sis Mubee,kina nufin kin yafemin abinda na aikata?"
"Yes of cause,kama mance ka sanar dani wani labari makaman cin hakan."
Farin ciki ne fal akan fuskar shi,ya sake rik'o fuskarta da hannayen sa biyu yace "Can i get that sweet again?" Cikin zolaya.
"Nop" ta bashi amsa cikin zolayar itama.
"But why?"
"Because it belongs to some one."
"Nd who is that?"
"Emmm,i think is...Atif... Muhammad... Bakari right?"
Dariya sosai yayi tare da rungumeta sosai a jikin shi yana ci gaba dayin dariyan.
"I love you Sis Mubee,nd i will always love you."
Lips nata ta sake sawa a cikin nashi sukaci gaba da tsotsar junan su.
  Bud'e k'ofa sukaji anyi,Shureim ne tsaye yana kallonsu cikin mamaki sannan ya rufe da sauri ya tsaya daga waje.
"Shureim yaka tsaya kuma?" Farhan ya tambaye shi
"Ya Farhan,kiss naga sunayi,bari naje na dakatar da Umma."
Dariya sosai yabawa Farhan, kansa ya mara a hankali cikin wasa yace "To kai dama haka kashiga babu sallama?"
Murmushi Shureim yayi yace "Na manta ne,amma bari nayi yanzu."
Koda aka amsa musu sallamar har awannan lokacin dariyan sukeyi shida Farhan d'in.

Ita kuwa Sis Mubee kunya taji sosai dukda dai shi Farhan d'in bai gansu ba.
Umma ce ta biyosu a baya da sallama,bayan an gaisa ne ake d'an tab'a hira, Shureim se kallon Sis Mubee yakeyi yana dariya.
Farhan ya lura dasu,dan haka yace "Shureim lafiyanka kuwa?"
Da gudu Shureim ya fice waje yana dariya,da sauri Mubinat tabi bayanshi.
Umma tace "Shureim da tsiya,Farhan key yana hannun Shureim karfa yaje ya jefar"
"Ai bazai tab'a jefar waba" cewar Atif.
Wayan Farhan ne ta fara ringing, dan haka ya fita waje domin amsa Kiran.
Ita kuwa Mubinat tana ta tambayan Shureim "Wai dariyan me kake tayine?"
Shuru yayi baice komai ba yana k'ok'arin gudu tana tareshi.
Can ya hango Farhan ya gama waya yana tahowa inda suke ba tare da ita Mubinat ta sani ba taci gaba da tambayar Shureim.
"Ka gayawa Ya Farhan ko?"
Shi kuwa Farhan yaji abinda Mubinat take fad'a dan haka yace "Bai gaya min komai ba ki dena damuwa."
Da Sauri ta juyo bayanta suna kallon juna har cikin ido. Duk kanninsu sun kasa d'auke idanun su akan junansu dayake suna kusa sosai.
Duk wanda ya gansu yasan wani irin kallo suke yiwa junansu. Cikin dauriya Farhan ya sauke idanunsa ya wuce waje ya tsaya a jikin mota,wani sabon son tane yake shigarsa a hankali.
  Tunani ya shigayi lokacin daya gayawa Abba ra'ayinsa akan Mubinat, Abba yace "Bakomai Farhan Indai kun daidaita da ita shikenan Allah ya sanya alkhairi."
K'walla Farhan ya had'iya yace "Ya Allah ka yaye min k'aunar Mubinat a cikin zuciya ta..."


                                 Team #KNJ

KOMAI NISAN JIFAAOù les histoires vivent. Découvrez maintenant