63

438 29 1
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

      by maman shureim
             🌺sad-nas🌺

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
    ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛ'Ş

#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com




This page is your's Momyn Sulti❤thankyou so much 😘Allah yabar zumunci ameen💐



Page 63
Washe gari Farhan da Ahmad suka je duba Atif har gida,bayan sun gaisa dasu Mummy ne suka wuce d'akin sa kai tsaye.
"Assalam"
Wani zafi yaji zuciyarsa tayi da yaga Farhan,kamar bazai amsa sallamar ba,sai kuma yayi tunanin ladan da zai wuce shi dan haka yace "Wa'alai kumus salam"
Duk da dai baice dasu su zauna ba,sai suka samu guri suka zauna tare da mik'a masa hannun suka gaisa amma baiso ba.
Farhan yace "Atif nazo ne domin na baka hak'uri akan duk wasu abubuwa da suka faru a tsakanin mu,domin yana da kyau musulmi ya zama mai yafiya da kuma mance duk abinda aka mishi a rayuwa"
"Atif nasan kana da ilimi kasan abubuwa da dama mai kyau da mara kyau sai dai wani lokacin muna da mantuwa,idan baka manta ba a zamanin Annabi Muhammad (S A W) yana zaune da Sahabban sa yana musu nasiha,can sai yace "Ku saurara yanzu d'an Aljanna zai shigo"
Sahabbai suka juya suna kallon k'ofar shigowa domin suga waye wannan d'an Aljannan,sai suka ga wani Mutum yana rik'e da takalmansa a hannu gashi babu yadda yake ma'ana ba yadda suke tsammanin ganin sa ba suka gan shi.
Washe gari ma haka Manzon Allah (S A W) yana cikin musu wa'azi sai yace "Ku saurara d'an Aljanna zai shigo" nan suka zuba ido sai suka sake ganin wannan Mutumin jiyan ne. Washe gari ma haka ya sake faruwa gunka sau ukku kenan?
Bayan an gama wa'azin ne sai d'aya daga cikin Sahabban yace lallai ni yau saina bi wannan Mutumin gidan sa domin inga mai yake yi da kullum sai Annabi yace ga d'an Aljanna zai shigo.
Sahabi yabi Mutumin nan har gida suka gaisa sai yace "Bawan Allah laifi nayi wa Mahaifina shine yace inbar masa gida na tsawon kwana ukku baya son ganina dan Allah ka taimaka min in zauna tare da kai na wannan kwana ukkun?"
Mutumin yace "Ba komai ina maka maraba"
Cikin dare suna bacci amma shi Sahabi ba baccin yake ba idonsa biyu amma dai arufe suke kamar mai baccin gaskiya,a tunaninsa zai ji Mutumin nan ya tashi sallan dare ne amma sai gaya baccin sa kawai yake yi,mamaki ya kama Sahabi yace "To k'ila azumi yake yawan yi"
Da safe yaga ya kawo musu abinci sunci tare. Abin ya dad'a bawa Sahabi mamaki,haka dai sukayi wannan kwana ukkun babu abinda ya canja. Ran da ya cika kwana ukun ne sai yace "Bawan Allah maganar gaskiya dai babu abinda ya had'ani da Mahaifina,abin da yasa na biyoka shine kullum idan zaka shigo masallaci sai Annabi yace mana mu saurara ga d'an Aljanna zai shigo har sau uku,shine nace zanzo gidan ka domin inga wasu irin ayyuka  kake yi haka,sai kuma naga baka ma sallan dare bare azumi."
Shi kanshi Mutumin sai mamaki ya kama shi yace "To gaskiya dai abinda ka kani shine kullum nake yi"
Sahabi ya mishi sallama harya fara tafiya sai Mutumin ya kira shi yace "Idan akwai abinda nakeyi daban to shine tunda nake ban tab'a kwana da haushin waniba a zuciya na,tumma kafin mutum yamin laifi na riga dana yafe masa wannan shine sam bana rik'o."
Allahu akbar,yaku 'yan'uwana akwai wanda zai iya yin haka a yanzu kuwa? Inama ace yau ni Sadiya Tahir haka nake? Yau ace na tashi nayi niyan yafewa Mijina,Iyaye na,'Ya'yana,'Yan'uwa na,Mak'wabta na,Malamai na,D'alibai na dama dukkan sauran 'Yan'uwa musulmai harma da wa'inda ba musulmai ba,Allah ka shaida na yafe musu har abada. Kufa masu karatu?
Dan Allah mu zamanto masu tsarkakakkun zuciya ako wace irin hali muka samu kanmu Allah ka gafarta mana ka k'ara tsarkake mana zuciyoyummu ameen.
Haka Farhan yaci gaba da kawo k'issoshi daban-daban yana musu nasiha gaba d'ayan su wanda jikin Atif sai ya mutu murus,domin dama can akwai ragowar imanin musulunci a zuciyar sa.
Farhan yaci gaba da cewa "Dan Allah Atif kayi hak'uri ka yafe min duk abin da ya faru,ba wai dan Sis Mubee tamin magana bane yasa nazo,wlh dama can akwai wannan niyan a raina sai kuma naga ta damu sosai jiya take  min magana akan ka. Atif Sis Mubee tana sonka so na hak'ik'a kuma babu yadda na iya nima domin ba laifinta bane dama can haka Allah ya tsara sai kuma ya faru babu makawa,dan Allah kayi hak'uri."
Ba Atif kad'ai ba,shi kansa Ahmad jikinsa ya mutu dama akwai wanda suke gaba dan haka nan take ya yafe masa acikin zuciyar sa,ya kuma yi alk'awarin zaije ya same shi su yafi juna gaba d'aya.
Mik'ewa sukayi dukkan su biyu suka sake mishi sallama tare da fatan Allah ya bashi lafiya.
Har suka fita daga d'akin Atif baice dasu komai ba sai da suka fita ne sannan zafafan k'walla suka fara zubo masa yana cewa "Nagode Farhan,na gode sosai da Allah yasa muka had'a alak'a da kai,na yafe maka har abada wlh komai ya fita a raina da izinin Allah ina fata kuma zaka yafe min ni da Abokai na,Allah sarki Sis Mubee,nayi alk'awarin sanya ki farin ciki insha Allah."
Shi kansa wani dad'i yaji,ga kuma wata ni'ima da yake ji yana shigar sa a hankali harma baya so ya dena jinsa.

Su Abban Mubeenat kuwa ana ta shirye-shiryen biki,Dad d'in Atif yace aje a kwaso kayan Mubeenat da yake gidan Atif wanda za'ayi amfani dasu sai a barsu furnitures kuwa duk a sayar sai a cika ayi mata sabo.
Haka kuwa akayi,komai dai masha Allah,tana cikin farin ciki mara misaltuwa sai dai wani lokacin hankalinta na gun Ya Atif da yake basu ji komai daga gare saba har yanzu.
Tana zaune sai ga motar Atif dana Friends nashi har guda ukku.
Cikin sauri ta fito ta nufi gurin su fuskarta d'auke da murna "Ya Atif?"
A hankali ya fito da k'arfe d'aya a hannun sa yana d'an d'ingisawa tare dayi mata murmushi "Yes Sis Mubee ina Angon?"
"Yana can parlour'n Abba,ya jiki naga yanzu da k'arfe d'aya kake tafiya masha Allah,Allah ya k'ara lafiya Ya Atif" tana magana murna fal akan fuskar ta.
"Ameen Sis Mubee ina tabbatar miki da cewa kafin bikin ku zan ajiye wannan k'arfen ma domin zansha rawa sosai agurin dinner"
"Hhhh kai Ya Atif kadai bari ka samu lafiya sosai,sannun ku da zuwa bisimillah ku iso"
"Yawwa Sis Mubee mun gode" sannan suka wuce parlour'n Abba tana binsu da kallo har da k'wallan farin ciki.
Bayan sun gaisa da Abba ne sannan suka gaisa da Farhan. Daga nan suka fito dukkan su suka wuce side nasu inda dukkan su suka bawa Farhan hak'uri akan abin da suka mishi shi da Shureim.
"Dan Allah ku bari,ni dama ban yiwa kowa hiran ba,kuma ya wuce har abada Allah ya yafemu gaba d'aya sai dai ina neman alfarma agun ku?"
Atif yace "Name kenan?"
Farhan yace "Naga lokacin auren ka abokanka dewa,ni kuma kaga mu 8 ne har da kai,dan haka nake son kaban aron abokan ka"
"Hhhh" suka sa dariya Atif yace "Wannan ai mai sauk'i ne imma kana son k'ari fiye da haka zaka samu sai dai mud'in ba kamar ku mune b... Farhan ya katse shi da cewa "Damu daku duk d'aya ne,Allah ya shiryar damu baki d'aya"
Suka amsa da "Ameen" sannan suka tambaye shi programs na bikin yana musu bayani dalla-dalla suma kuma suka kawo nasu shawaran ya kuma amince musu...

Vote and comment

                        Team #Farbeen

KOMAI NISAN JIFAAHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin