61

491 31 12
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

      by maman shureim
             🌺sad-nas🌺



® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
    _ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛ'Ş_

#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com

Ina mik'a godiyata agareku 'yan'uwa,nagode sosai da kulawarku akan 'yata Suhailat wanda addu'oinku ya karb'u domin ta samu lafiya harma taje skul jiya😘 hakan yasa naga ya dace in muku godiya musamman 'yan 🌺SAD-NAS🌺NOVELS DA KUMA MIEMIEBEE👄NOVELS ina mik'a godiyata mara adadi a gareku Allah ya biya muku buk'atunku na alkhairi ameen...
        ❤OLKUT❤




Page 61
Mubeenat ce kwance a d'aki duk abin duniya ya dameta. Musamma yadda taga Ya Farhan ya fita harkanta abin na mata ciwo sosai,ita kuwa tayiwa kanta alk'awarin bazata sake kiran shi ba bare ma tayi tambaya akan shi.
Muryam Umma taji tana k'wala mata kira,cikin hanzari ta mik'e zuwa gareta "Gani Umma"
"Kije Abbanki yana kira"
"To" sannan ta wuce parlour'nsa da sallama ta samu guri ta zauna "Gani Abba"
"Mamana na kirakine domin in sanar dake cewa Farhan ya sake neman aurenki a karo na biyu,sai dai wannan karon ban nemi jin ra'ayinki ba na amsa musu cewa nabasu"
"Shin ko dai akwai wani da kike so daban?"
Wani farin cikine taji ya lullub'eta,fuskarta d'auke da murmushi tace "Ba kowa Abba bani da wani zab'i daya wuce wanda ka amsawa ayanzu,nagode Allah daya bani kai a matsayin Mahaifi Abbana Allah ya saka muku da gidan aljanna" tana kaiwa nan ta mik'e tare da barin parlour'n cikin jin kunya.
Shi kanshi Abban nata murmushi yakeyi dan yadda yaga 'yarsa ta nuna farin cikinta a fili,yasan duk duniya babu wanda Mubeenat take so sama da Farhan dan haka yayita musu fatan alkhairi a zuciyarsa yana mai jin farin cikin shima.
Mubeenat murna yak'i b'oyuwa,zuwa d'akin Ummanta tayi ta fad'a jikinta tana cewa "Haba Umma keda ya kamata kimin albishir kuma shine kikayi shuru,lallaima Ya Farhan Umma kinsan tunda ya tafi bai kirani ba,tun yana nan d'inma fita harkata fa yayi gabad'aya ya barni cikin damuwa,amma ba komai saina rama abinda ya mun wlh" ta k'arashe maganar tana murmushi.
"Kunji min rashin kunya ko,toke in banda abinki ba idda kike yiba,ko so kike yace yana sonki bayan kina iddan?"
Ai dai amma Umma sai muci gaba da mu'amala kamar yadda muke ada,bawai ya canja min haka ba,wlh zai dawo ya sameni saina rama Umma"
"Ni d'agani karki karya min k'afa mara kunya"
"Hhhhh haba Ummana idan ban gaya mikiba wa zan gaya wa? Allah ya barmun ku Ummana"
"Ameen,kije ki fara shiri kinama zama a cikin ruwan dana had'a miki kuwa?"
"Ina yi wlh ban tab'a fashi ba,Umma wlh ina tausayin Ya Atif idan har yaji zancen aurena"
"Abbanku zaije ya sameshi ai karki damu"
"To" sannan ta mik'e ta koma d'akinta ta kira Amal tana sanar da ita.
Dariya sosai Amal tayi tare da cewa "Sai yanzu kikaji labari? Aini tunkan ya tafi nasan komai,shi yace kar in sanar dake hhhh"
"Wlh Amal da kina kusa dani dakin sha dundu a bayan ki 'yar rainin hankali kinaga fa yadda na damu amma shine kika k'yaleni ko? Zamu had'u ai"
"Hhhhh our Habibty is back finally..."
"Yaushe zaku dawo?"
"Gaskiya dole sai Umma ta haihu,amma zamu zo  bikin ai"
"Amal kardai har ansa rana?"
"Hhhh Habibty-Habibty ansa mana this week zasu dawo satin sama kuma kuna soyewa wata k'ila ma harmun samu baby" ta k'arashe maganar cikin zolaya tana dariya.
Itama Mubeenat abun dariya ya bata tace "Ke bafa nason wulak'anci pls ki gaya mun"
"To wai ke Habibty nine Habibinki? Ki tambayesa mana jiki komai"
"Aini mun b'ata dashi ne dan wlh saina rama abinda yamin za kuma ki gani"
"Hhhh ana hubbuki Habibtyyy!"
"Zaki gane wlh kema idan kika shiga hannuna"
"Ke dai zaki gane idan kika shiga hannun Ya Farhan hhhh"
Takaici yasa Mubeenat katse wayar tana tunanin inama Amal tana kusa data sha dundu harda cizo.

Dad d'in Atif da Abban Mubeenat sun yiwa Atif nasiha suka bashi hak'uri akan ya d'au kaddara haka Allah ya tsara mishi.
Nasiha sosai suka mishi amma ya kasa cewa komai in banda k'walla da yake yi,tare dayin maganan zuci yana cewa "Sis Mubee meyasa zaki amince wa Farhan ki barni,ina alk'awarin mu na cewa bazaki barni ba? Da inga aurenki da Farhan gara min mutuwa ta Sis Mubee"
Haka suka gama mishi nasiha baice komai ba sai hawaye da yake bin fuskar sa.
Ayau su Farhan suka iso Nigeria,Ummi Abbi Kakansa shi da kuma Abdullahi sai abokansa guda biyar su goma cip suka iso.
Bayan an taro sune aka iso dasu gidan Abba inda ananne zasu ci abinci sannan su wuce can gidansu.
Wanka Mubeenat tayi tare da kwalliyarta d'an dai-dai tasa wani riga mai dogo hannu gold jikinsa d'auke da wani abubuwa d'igo-d'igo haka a mulmule sannan ta d'auki jan lapaya ta d'aura shi a kwankwasonta tare da wucewa dashi har saman kafad'arta kamar dai shigan indiya,sannan ta nad'a gyale black a kanta daya sha parking hannunta d'auke da black hand bag tayi kyau sosai.
Ta fito tana taku a hankali ga wani k'amshin turare da iska yake ta yawo dashi a harabar gurin.

 Ta fito tana taku a hankali ga wani k'amshin turare da iska yake ta yawo dashi a harabar gurin

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Duk suka zuba mata ido tun daga k'asa har sama suna kallon ta. Gun Ummi ta nufa kai tsaye inda Ummi ta fara cewa "Oh my Habibty come here lemme give you a hug please"
Murmushi cike da fuskarta ta k'arasa tare da rungume Ummi tana cewa "Wlcum Ummi,i'm so happy to see you again"
Farhan dai ya gama bushewa a tsaye ko k'yafta ido bayayi hakama friends nashi.
Bayan wannanne ta d'an rusuna tace "Abbi sannunku da hanya,sannu Kaka"
"Yawwa Mubeenat sannu" suka fad'a a tare sannan ta kalli su Ya Farhan tace "You are all wlcum"
"Thanks our Habibty" sukace da ita sannan ta sake kallonsu tace "Your Habibty? I'm not your Habibty, kar in barku a tsaye bisimillah ku k'arasa ciki nayi bak'one a waje zanje in dawo" ta k'arashe baganar tare da hararan Farhan.
Dariya suka sa suna kallon Farhan inda yayi saurin bin bayanta su kuwa suka wuce inda Ahmad yake musu jagora.
Mamaki sosai ya kama Farhan daya hango Mubeenat zaune a cikin wata mota ga kuma wani yana zaune a ciki.
Gun motar ya k'arasa yana nocking dayake glass d'in tin ne. Fitowa  tayi ba tare data bari ya kalli na cikin motar ba tace "Ya Farhan ina hira ne,amma yanzu zan shigo"
Kallonta yakeyi har cikin ido baisan lokacin daya ce mata "Waye shi?"
Murmushi tayi tace "Kamar ya waye shi kuma?"
"Ina nufin meya zo yi agurin matar da zan aura?"
"Matar da zaka aura? Kaima kace matar da zaka aura ai ba'a riga da an d'aura auren ba tukunna"
Cikin mamaki yake kallonta "Habibty what are you saying?"
"Please Ya Farhan kaje zan shigo yanzu"
"No bazai yuba,fito mu tafi"
"Kamar ya in fito bak'o nayi taya zaka ce in fito mu tafi shi kuma fa? Ko baka san cewa shine zan aura ba?"
"Shine zaki aura?" Da sauri ya zaga ta d'aya gefen ya bud'e motar ai sai yaga k'afar namiji sanye da takalma masu tsadan gaske hakama kayan jikinsa.
Fitowa yayi fuskarsa d'auke da murmushi ya mik'awa Farhan hannu tare dayi masa sallama,cikin rashin fahimta Farhan ya bashi hannu tare da amsa mishi sallama.
"Sunana Anwar wanda zai auri Mubeenat"
"Wanda zai aureta?" Ya maida kallonsa gun Mubeenat tayi saurin cewa "Ya Farhan shine wannan"
Kallonta yakeyi cikin rashin fahimta ita kuwa Anwar take yiwa murmushi.
Amal da Aisha dake zaune a bayan motar sai suka fashe da dariya tare da fitowa daga motar suna kallon Mubeenat.
Haushi ya kama Mubeenat ta tsaya hararansu su kuwa suka nufi gun Ya Farhan suna dariya tare da cewa "Ya Farhan sannunku da isowa,shima Anwar dariya yayi tare da dafa kafad'ar Farhan yace "Haba Ango kardai ace ka karaya ne? Ni dai sunana Anwar wanda zai auri Aisha ne ba Mubeenat ba karka kaimin duka please"
Dariya suka sa dukkansu inda haushi ya kama Mubeenat ta wuce cikin gida tana hararan Amal da Aisha da suka kopsa mata...

Vote and comment

                         Team #KNJ

KOMAI NISAN JIFAAWhere stories live. Discover now