28

288 25 2
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

     by maman shureim
            🌺sad-nas🌺

*©Pure Momment Of Life Writers*
           We don't just entertain and educate,we also touch the heart of the readers

      
            🎂🍾🎂🍾🎂🍾
*_Happy birthday dear SADNAF,yau ranace da zamuyi rawa muyi juyi a P•M•L💕dan murnan zagayowar shekarunki😍_*
    🕯🌷🕯🌷🕯🌷
     *_Wish you a very_*
    _HAPPY BIRTHDAY_
🎂🌹🎂🌹🎂🌹🎂🌹
_May life lead you to great happiness,success and hope that all your wishes comes true!🌺_
         🎈🎈🎈🎈🎈🎈
         *Enjoy your day.*
                ❤❤❤



Page 28
Zaune yake yanayiwa Ya Musty bayani ba tare daya b'oye masa komai ba.
Shikansa Ya Musty ya tausayawa k'anin nasa,shuru yayi yama kasa cewa komai.
"Yanzu kana nufin taci gaba da zama a gida krnan har tsawon lokacin da Doctor ya fad'a?"
"Hakane shine abinda ya dace Ya Musty,dan inhar muka ci gaba da zama yare to tabbas bazan iya dakatar da kaina agareta ba."
Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa "Shikenan tashi kaje,zanje gurin Abban yanzu"
Cikin sanyi jiki da damuwa daya nuna a tattare dashi ya shiga motarsa ya tafi gun Mum nashi Ya Musty yana binshi da kallo tare da mamakin "Atif kuma da H i V yau?"
Motarsa ya shige shima ya nufi gidan Abba. Kai tsaye ya nufi parlour inda suke zaune Umma tana tambayarta "Yau kuma meya sake had'aku,kodai yau d'inma baki san komai babe?"
Cikin kuka tace "Umma bari yazo zai gayamuku."
"Ki dakata yace Mustapha zaizo ya gayamana komai dan haka tashi kije Mamana" cewar Abba.
Ta mik'e zata fita kenan sega motar Ya Musty,hakan yasa ta koma parlour zata zauna se Abba yace da ita "Jeki ciki Mamana."
Bayan ta gaishe shine seta wuce ciki.
Bayan an sake gaisawane yace "Abba ba wani abu bane yasa nazo sedan Atif da Mubinat" nan dai ya zayyana musu komai kamar dai yadda Atif yama mubinat bayani bai b'oye musu komaiba.
Yace gaba da cewa "Wannan shine dalilin sakin daya mata na farko,sannan yanzu kuma shawaran da Doctor ya bashi kenan shiyasa ya dawo da ita gida harse lokacin da aka gama mata test nata mukaga sakamako kafin yasan matakin d'auka."
"Dan Allah Abba kuyi hak'uri?"
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un,aibani ya kamata kaba hak'uriba se Atif,yanzu dukba ita ta sashi a wannan halinba,mutum da matarsa amma kik'i amincewa dashi,wlh zata gane kurenta yau."
"Abba ayi hak'uri,ni wlh banga laifin Mubinat ba Abba,saboda bata sonshi amma haka akayi aurennan,shiyasa ake hana iyaye yiwa 'ya'yansu auren dole,saboda yaran yanzu ba kamar na da bane,ka haifesune baka haifi halinsuba,kuma wlh dama ni Abba kasan banso wannan bikinba,Hajiya ce tace lallai se'anyi to yanzu gashi ai ta jefa jikanta a cikin wani hali,wlh duk laifintane Abba kayi hak'uri bawai cin fiska nake makaba amma wlh Hajiyace ta cuci Atif,dan asalima Atif bayi da niyan auren 'yar k'asarnan tamu,Hajiyace ta cusa mishi son Mubinat kuma dama da yake duk cikin k'annensa yafi son Mubinat da Aisha shiyasa ma kawai ya amince a lokaci guda."
"Dukda haka dai itama Mubinat d'in da nata laifi,sekace bare aka aura mata,to yanzu wa gari ya waya shiyasa naganta jikinta a sanyaye dukta birkice" cewar Umma.
"Umma wlh Mubinat bata da laifin komai,nisam banga laifinta tunda dama kowa shaida ne bata son Atif a matsayin miji,yanzu dai Abba kuyi hak'uri gara tayi zamanta anan d'in har lokacin da komai zaizo k'arshe,fatanmu shine Allah yasa yadda na farko ya gwada bata d'auke dashi to sauranma duk muga alkhairi,shi kuma Allah ya bashi lafiya" cewar Ya Musty kenan.
Shuru sukayi duk hankalinsu a tashe yake musamman ma Abba daya rasa abun fad'e...

Farhan kuwa bacci yaketayi tun bayan dawowarsu harse 4:10pm ya farka.
Toilet ya wuce yayi alwala yazo ya gabatar da sallolinsa sannan yayi wanka ya fito,lokacin Abba ya fita dan haka ya wuce parlour'n Umma da sallama.
Shureim a zaune yana kallo yana cin abinci,juyowa yayi yana kallon Farhan "Ya Farhan ka tashi,ya jikin naka?"
"Alhandulillah Shureim bazakayi karatuba se kallo ko,ina Umma?"
"Taje unguwa daga ni se kai se kuma Sis Mubee agidan."
Mamaki sosai Farhan yayi "Sis Mubee kuma?"
"Eh tana bacci a d'aki d'azu Abba ya daketa naje in gaya maka naga kanata bacci shiyasa ban tashe kaba maigadine yazo yake taba Abba hak'uri kafin ya barta."
Farhan ya zauna tare da mamaki sosai shidai tunda yazo gidan bai tab'a ganin Abba yayiwa Mubee koda fad'a bane amma kuma yau harda duka?
"Ya Farhan kasan me,wai Ya Atif ya dawo da ita ta zauna har tsawon wata tara a gidannan idan ta haihu seta koma gidansa,dama tana da ciki ne?"
Dariya sosai Farhan yayi dajin maganar Shureim,amma azuciyarsa yasan ba lafiya ba. "Yanzu Sis Mubee tana kwance a d'aki kenan?" Ya tambayi Shureim
"Eh tana bacci,tace min kanta yana ciwo shine Umma ta bata magabi tasha daganan take bacci har yanzu bata tashiba,wlh bana son abinda zai tab'a Sis Mubee Ya Farhan,shiyasa naso ka aureta ka tafi da ita can Madina harda nima."
Kamo Shureim yayi ya shafi kansa "Ka dena damuwa Shureim nida Atif aiduk d'ayane kaidai kayita mata addu'a kaji?"
"To" sannan ya kamo hannun Shureim d'in suka fita zuwa waje,a nanne mai gadi yake sanarwa Farhan da abinda yake faruwa game da Atif da kuma Mubinat dan Abba ya gaya masa komai dake tsohone kuma yana da kirki sosai ga iya rik'e sirri.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" Farhan ya furta hankalinsa a tashe.
"Yanzu dama maganar ta tabbata kenan,ya salam Habibty Allah yasa baki dashi,lallai inhar baki dashi toya kamata Atif ya bani ke inhar zaimin adalci,you will come back to me Habibty." A cikin zuciyarsa yake fad'in hakan.

Bayan isha Atif yazo gun Mubee se Farhan ya tsai dashi daga waje suna magana.
"Atif i'm sorry for what happen,wlh banji dad'i hakanba ko kad'an."
"Hmm Farhan meka maidanine wai,sakarai ko? To wlh inma kana tunanin Sis Mubee zata dawo garekane tokayi kuskure,bazan tab'a baka itaba ko a wani irin haline kasa hakan a ranka."
"Haba Atif,wani irin maganane wannan? Meyasa ka fassarani wani iri,Atif ina cikin hankalina akayi aurenku da Sis Mubee a lokacin ban dakatarba se a yanzu?"
"Baka cikin hankalinka Farhan,dan baa ma san wacece Mubee ba a wannan lokacin,shine yanzu kake murna da abinda ya sameni ko,to ina so kasa a ranka cewa Sis Mubee ta kubce maka kenan ba kuma zaka iya kamo taba."
Murmushi Farhan yayi tare da cewa "Allah ya baka hak'uri ko so d'aya ban tab'a fatan wani abu a samu aurenkuba Atif,danna yarda kaddara dama can Mubee ba matata bace,amma bazan maka k'aryan cewa har abada k'aunarta yana dashe a zuciyata babu kuma wanda zai cire wannan se wanda ya dasa min." Yana kaiwa nan ya wuce zai tafi amma se Atif ya kamo rigarsa dan yadda kalaman Farhan suka mishi zafi yayi magana cikin b'acin rai "Wlh sena sake mayar dakai yadda kake ada karka ga cewa ka samu lafiya yanzu zan iya yin komai ga duk wanda yayi k'ok'arin shiga tsakanina da Sis Mubee!
Juyowa Farhan yayi cikin mamaki yace "What! Me kace Atif?"
"I say it and i mean it"
Ya wuce ciki gun Mubee yabar Farhan tsaye yana mamakin jin furucin Atif.
"Lallai zan nuna maka wanene Farhan Abdullahi Taimoor,dole ne Habibty ta dawo gurina koda kuwa tana d'auke da cutar ne,seka d'and'ani abinda na d'and'ana Atif you will pay for what you have done Atif...! Ya k'arashe maganar da k'arfi wanda seda su Abba suka fito zuwa waje dan jin ihun Farhan...

To masu karatu,anan zan tsaya da labarin semu tsunduma cikin asalin labarin domin in warware muku k'ullin cikinsa ta yadda zakufi gane tushen labarin. Ko kuma ina jiran ra'ayoyinku akan haka,shin mu shiga zuwa asalin labarinne kodai muci gaba da tafiya a hakan???
  Se naji ra'ayoyinku



                                Team #KNJ

KOMAI NISAN JIFAADonde viven las historias. Descúbrelo ahora