40

276 22 0
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

      by maman shureim
             🌺sad-nas🌺

*©Pure Momment Of Life Writers*
        We don't just entertain and educate,we also touch the hearts of the readers❤






Page 40
Abu kamar wasa k'aramar magana ta zama babba. Ko ina akaje babu labarin Mahaifiyar Amal.
Atif ne ya d'auki wayar shi ya kira Sis Mubee,lokacin tayi wanka harta shirya ta fito parlour suna zaune dukkansu tana zuba musu d'anwaken data dafa musu wanda ta yanka dafaffen k'wai nata ta yanka su slide ga tumatur ga cabage da lemun tsami.
Jin ringing na wayar tane yasa ta duba,sunan Sweet Bro ta gani a rubuce. Seda ta gama had'awa kowa nashi sannan ta zauna tare dakai wayan kunnenta "Hello Ya Atif"
"Sis Mubee kun tashi lfy"
"Lafiya lau Ya Atif ya kake yasu Umma ina Shureim?"
"They are all fine,Sis Mubee ko Umman Amal tazo tagun ku?"
Farhan dai ahankali yake bin Mubeenat da kallo,su kuwa Ummi se santin d'anwaken sukeyi waiya musu dad'i gobema shi zata musu. Sunata hiransu ita kuwa tana wayarta "Umman Amal kuma,bata zoba"
Shima kanshi Atif yadai tambaya ne kawai amma yasan batama san gidan ba.
"Ikon Allah" cewar Atif.
"Ya Atif meya faru ne?"
"Shikenan Sis Mubee ba komai se anjuma"
"No please wait Ya Atif" cikin sauri Farhan ya kalleta ya kasa d'auke idanunsa akanta. "Me yake faruwa ne Ya Atif dan Allah ka gaya min idan akwai wani abu"
"Sis Mubee Umman Amal ce ake nema tun d'azu tabar gida batare da ta gayawa kowaba har yanzu nemanta ake duk inda akaje babu ita,ki dai tayamu da addu'a byee."
Take idanun Mubee ya kad'a "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" ta furta sannan sauran suka amsa suka k'arasa atare.
"Mubeenat lafiya?" Abbi ya tambaya
Cikin sanyi murya tace "Lafiya Uncle" sannan tayi saurin cewa "Ya Atif yanzu ina Amal?"
"Tana gun Umma se kuka takeyi wlh"
Take k'wallan da Mubeenat ta b'oyesu a idanunta suka gangaro zuwa fuskarta "Ya Atif dan Allah ka rarrasheta nima zanzo yanzu"
"Ok byee." Ya katse wayar.
A sanyin jiki ta ajiye wayar tana share k'walla "Uncle ina so inje gida gun Amal,tun safe Mahaifiyarta ta fita daga gida kuma bata sanar da kowa zata fitaba tun d'azun ake neman ta har yanzu babu labarinta"
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" suka furta dukkansu
"Uncle Amal tana cikin damuwa ina so inje in zauna da ita"
"Ok Mubeenat ki zauna kici abinci semu tafi tare kinji?"
Bazata iya mishi musu ba dan haka ta zauna amma sam ta kasa cin abincin.
Farhan kuwa duk idonsa akanta yake,inda su kuma suketa tattaunawa akan maganar.
"Sis Mubeenat" Farhan ya kira sunanta.
A hankali ta d'ago ta kalleshi batare datayi magana ba.
"Eat your food okay?"
Mik'ewa tayi tare da d'aukan wayarta tace "I'm not hungry" sannan ta wuce d'aki yana bin plate d'in d'anwaken nata da kallo.
D'auka yayi ya zuba mata kayan had'in d'an dai-dai sannan ya siyayi madara mai sanyi wanda suka taho dashi daga Madina ya d'auka ya bita dashi d'akin Ummin sa.
Da sallama ya shiga tana zaune tana wani sabon hawayen.
Agefenta ya ajiye abincin sannan ya rik'e madaran a hannunsa yana kallon fuskarta "Sis Mubeenat" ta d'ago ta kalleshi "please eat"
"I'm not hungry Ya Farhan"
"I don't believe you,beside you are the one that coked and it's so sweet please eat,or do you wamme to say Habibty Mubeenat please eat?"
Kallonsa tayi har cikin ido shima kuma ita yake kallo tare da lumshe mata kyawawan idanuwansa yana mata murmushi.
"No thanks" ta fad'a tare da sunkuyar da kanta k'asa.
"Alright lemme feed you" ya fad'a yana k'ok'arin ajiye cup d'in madaran,ganin dagaske yakeyine yasata cewa "No Ya Farhan"
"Alright then eat" ya tsareta da ido.
A hankali ta d'auki spoon d'in takai bakinta tana ci kamar wata mara lafiya.
"Habibty tell me what you want"
D'agowa tayi da Sauri tana kallonsa "Take me home please?"
"Naji but sekin ci"
Ba musu taci kamar spoon biyar sannan tace dashi "I'm full now"
Madaran hannun shi yayi niyan kaiwa bakinta se kuma ya tuna da cewa bafa k'anwar sa bace ta Madina,nan ya fasa tare da ce mata "Take"
Karb'a tayi tahau sha tas ta shanye dan dad'in madaran dataji.
Cikin jin kunyarsa tace "Thankyou"
Murmushi yayi mata kawai sannan ya mik'e,itama mik'ewar tayi tare da d'auka plate da cup d'in da niyan fita dasu "Where are you going?"
"I will take it out"
"No let me" ya karb'a batare data soba ya fice tana binshi da kallo.
Gaskiyan Amal ne Farhan kyakkyawan gaskene gashi da tsawo ga wani k'amshi mai dad'i dake fitowa data jikinsa.
Murmushi tayi tace "Habibty kuma?"

Bayan duk sun gamane Abbi yace da Faran ya kira Mubeenat su tafi.
Tana zaune tana kiran number'n Amal amma ba'a d'agawa sam.
"Slm Habibty let's go" ya fad'a batare daya bud'e k'ofar ba.
"Ok" tace dashi sannan ta fito rik'e da wayanta a hannu. Kallon junansu sukayi tayi saurin sunkuyar da kanta k'asa shi kuwa murmushi yayi sannan yayi gaba tana binshi a baya.
Abbi ne ke driving Abadullahi yana gaba,Farhan da Mubeenat kuma suna baya yana ta kallon chartn d'in da takeyi kamar haka.
_"Slm"_
_"Wslm waye ne?"_
_"Wani masoyinkine"_
_"To nagode"_ sannan tayi blocking nashi duk akan idon Farhan dama Abbi nashi ya koma masa hausa da kuma karatun hausa dukya iya.
Wayarsa yasa a silent sannan yace da ita "Let me see your phone Sis Mubeenat"
Ba musu ta sauk'a a whatsapp d'in sannan ta mik'a mishi.
Yana karb'a yayi dailing number'n shi ai kuwa seya katse sannan yayi deleting number'n shi daga wayarta ya mik'a mata tare da cewa "Thanks"
Murmushi ta mishi tare da mamakin to meyayi da wayan nata dan ko dak'ik'ai biyu baiyiba a hannunsa ya bata.
Shi kuwa saving number'nta yayi da suna *HABIBTY MUBEENAT*
Har suka iso gida babu wanda ya sake yin magana a cikinsu,suna isa Amal ta fito da gudu,ta d'auka ko Abba ne tare da Abbanta suka dawo,ganin bak'uwar motace yasata sake fashewa da kuka.
Cikin sauri Mubeenat ta fito daga motar taje da gudu suka rungume junansu suna kuwa tare da wucewa ciki.
Atif ne yayi musu jagora har zuwa parlour'n Abba,sannan yazo ya sanar da Umma taje suka gaisa.
"Ashe kuma abinda aka tashi dashi kenan?" Cewar Abbi.
"Eh wlh,abu kamar wasa har yanzu dai shuru wlh" cewar Umma.
Nan dai ta bashi labari tun lokacin da Umman Amal d'in tace da Amal ta kira mata Umma.
"Ikon Allah,kuma babu wanda yaga fitarta?"
"Eh Maigadi yace yaga fitarta wlh,sedai baiyi tunanin wani abu ba shiyasama bai damu da yaga ta ina zata biba"
"Ikon Allah,to Allah yasa dai lafiya Allah ya bayyanata"
"Ameen" suka amsa gaba d'ayansu sannan su Farhan suka gaisheta cikin girmamawa.
"Bari a kawo muku abinci" cewar Umman Mubeenat.
"A'a wlh Alhamdulillah Mubeenat ta mana d'anwake ai Alhamdulillah wlh"
Dariya Umma tayi "D'anwake kuma,Farhan kun iya ci kuwa?"
Murmushi yayi "Munci sosai Umma ai yayi dad'i"
Nan dai sukai ta hira cikin dariya sannan Umma ta fito.
Fitarta bada jimawaba sega su Abba sun dawo,kowa ya fito cikin sauri dan jin ko an ganta amma sam ba'a ganta ba.
Hankalin Amal ya sake tashi fiye dana da,ba Amal kad'aiba duk wanda yake tsaye agun seda yaji wani iri kowa da iri tunanin da yakeyi a cikin ransa.

Abu kamar wasa yau kusan kwana uku kenan aketa faman nemanta harda gidan TV tare da nuna hotonta amma sam babu wanda yace ya ganta.
Amal ta rame bata da aiki se kuka,kullum idan Mubeenat ta gama abinci se su Farhan su kawota ta yini har dare kafin su dawo su d'auketa.
Yau sati kenan da b'atan Umman Amal amma haryau babu wani labari akanta. Su Samira kuwa suna gidan suna kukan munafurci tare da nuna damuwarsu sosai akan ta.
Lokacin taron bud'e company yayi hidima sosai akayi base na zaiyana muku komaiba, inda Mubeenat tace da Ummi zata mata kwalliya,ba musu ta amince dan yadda take k'aunar Mubeenat har cikin ranta.
Kwalliya d'an dai-dai tayi mata bamai yawa ba Farhan se yabawa yake da kyawun da Mahaifiyarsa tayi hakama Abbi nashi.
Soyayya sosai sukeyi ko agaban wayene basa kunya da yake haka suke dama su larabawa.
Kowa yayi kyau Amal nedai sam bata cikin walwala kuma dukkanmu munsan dalilin hakan,a haka aka nufi gun taron kowa Ummin Farhan yake kallo tare dasu Farahan da kakansu anata yaba irin kyawunsu ana cewa ai sune masu company d'in dama ba 'yan k'asarnan bane su...

Drop your vote and comment for each page pls

                           Team #KNJ

KOMAI NISAN JIFAATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang