54

283 31 1
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

     by maman shureim
            🌺sad-nas🌺

*©Pure Momment Of Life Writers*
        We don't only entertain and educate,but we also touch the heart of the readers❤

#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com






Page 54
  "Habibty bata d'auke da HIV? Alhamdulillah na tayaki murna Habibty,kai kuma Atif Allah ya baka lafiya" cewar Farhan sannan yaja motarsa ya fice daga gidan.
Atif bai bar gidansu Mubeenat ba har saida ta tabbatar mishi da cewa *tana tare dashi* sunan book d'in *miemie bee*.
Ta tabbatar mishi da cewa bazata tab'a rabuwa dashi ba inhar zai iya zama da ita batare da wani abu ya sake shiga tsakaninsu ba,shi kuwa ya amince mata da hakan.
Bayan sallan isha ne Dad d'in Atif yazo gidan domin susan meya kamata ayi akan maganan su.
Duk ana zaune a parlour ana sauraron Atif inda yaketa magiyan kar'a raba shi da Sis Mubee d'insa yayi alk'awarin zama da ita haka koda wani abu bazai shiga tsakaninsu ba tunda itama ta amince.
Abban Mubeenat dai yama rasa mai zaice gaba d'aya tausayin Atif ya kamasu dukkansu harda Farhan.
Dad d'insa ne yayi gyaran murya ya fara magana "Atif kayi hak'uri ka d'au kaddaran da Allah ya d'ora maka,babu yadda za'ayi abarka da Mubeenat kuci gaba da zama bayan ga halin da kake ciki,dole ne a raba wannan auren koda kuwa kak'i sakinta."
"Dad wlh muna son junanmu kuma ai ta amince da yadda muka tsara abunmu ko Sis Mubee? Ki gayawa Dad please karki bari a raba mu dan Allah?"
Cikin muryar kuka take magana "Dad,Abba wlh na amince zan zauna dashi ako wani irin hali ne,amma dan Allah karku rabamu."
"Mubeenat ku dena wannan shirmen daga ke har shi,babu yadda za'ayi ku zauna a haka koda kuwa kin amince saboda akwai zalinci,dan haka Atif karka fara abinda kai kanka kasan bazai yuba kawai ka d'au hak'uri" cewar Ya Musty.
"Haba Ya Musty kai da kanka kake fad'in hakan?"
"K'warai kuwa Atif,kasan dai ina sonka kuma ina so inci gaba da ganinka tare da Mubeenat,amma hakan bamai yuwuwa bane kayi hakuri."
"Abba dan Allah ku barmu,wlh zan zauna dashi a hakan sai muyita zamanmu kamar yadda muke dah a matsayin Yaya da K'anwa" cewar Mubeenat.
"Mubeenat kin kasa ganewa ne,duk baku fahimci inda maganar take ba babu amfanin zamanku ai tunda babu riba,sannan musulunci ma bata yadda da hakan ba sabida zaki cutu,kaga Atif nafa gaya maka komai tun a gida dan haka karku b'ata mana lokaci."
"Haba Ya Musty,Hajiya Kaka kiyi wani abu dan Allah?"
"Da akwai abinda zanyi danayi Atif kai kanka kasan da hakan,duk abinda suka gaya maka shine gaskiya,ka d'au hak'uri dama can Mubeenat ba matar da zaka k'are rayuwa tare da ita bane,Allah yasa hakan shine mafi alkhairi kayi hak'uri Atif."
"Ni a ganina a d'an bashi lokaci dan a yanzu yana cikin wani irin hali ne,a d'an bashi lokaci kar ayi mishi gaggawa" cewar Abba.
"Babu wani lokaci da za'a bashi,dan abinda shaid'an yake jira kenan,bazan so ace an samu wata matsala ba dan haka kayi abinda ya dace inhar kana son  Mubeenat Atif" cewar Ya Musty.
Juyowa yayi suna kallon juna inda suketa hawaye "Sis Mubee?" Ya kira sunan ta.
D'agowa tayi tana kallonsa "Dan Allah karka cemin komai Ya Atif please?"
"Ke kanki kinsan Atif bazai tab'a aikata miki hakan ba, amma ya zama dole Sis Mubee,kaicona da mai hali irin nawa dama duk mai wani mummunan hali to dolene kaga sakayyan Ubangiji ko'a kanka ko'a kan 'Ya'yanka ko Yayyun ka ko K'annenka ko kuma wani naka na jini, ni gashi sai Allah ya jarabceni da sonki Sis Mubee, na kuma mallakeki a matsayin matata amma kuma ina? Ina ji ina gani dole in rabu dake koda kuwa zan mutu ne"
"Dan Allah kayi shuru Ya Atif ka dena fad'an hakan,ai muna tare"
"Sis Mubee na sauke igiyar aurena dake kanki dan Allah kiyi hak'uri."
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" duk 'yan parlour'n suka furta,sannan Atif ya mik'e kamar wani mara lafiya yana tafiya ahankali kamar wanda babu jini a jikinsa yayi waje.
Mubeenat kuwa kuka ta fashe dashi tare da tasowa zata bishi zuwa waje,sai Ya Musty ya dakatar da ita ta hanyar cewa "Koma ki zauna" sannan yabi bayan Atif d'in inda Mubeenat ta fad'a jikin Ummanta tanata kuka mai tsuma zuciya.
"Abba dan Allah kuyi wani abu akai,wlh ni kad'ai nasan waye Ya Atif,ina tsoron irin halin dazai shiga dan Allah Dad kubarmu tare ad'an bashi lokaci Umma kiyi magana dan Allah?"
"Ki dena kuka Mubeenat,ai magana ta riga data k'are kuma yanzu" cewar Hajiya Kaka.
"Wlh bai k'are ba Hajiya Kaka saki biyu kenan har dana dah kinga har yanzu da sauran aurenmu,dan Allah ku taimaka wlh zan zauna dashi a hakan kodan in kula dashan maganinsa imba hakaba bazai shaba wlh nasan halin Ya Atif dan Allah Abbana ka taimaka min ku tausayawa Ya Atif."
Dukkansu jikinsu ya mutu murus summa rasa abun cewa dan haka Dad d'in Atif yayi magana "Mubeenat kiyi hak'uri mu tayashi da addu'a kawai,Allah ya miki albarka"
Mik'ewa Abba yayi domin ya raka Yayansa inda Mubeenat take ta rusa kuka da gaske,Umma da Hajiya Kakane suke bata hak'uri,shima Farhan yabi bayansu zuwa waje...

Vote and comment please

                    Team #KNJ

KOMAI NISAN JIFAAWhere stories live. Discover now