27

294 17 2
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

     by maman shureim
            🌺sad-nas🌺

*©Pure Momment Of Life Writers*
          We don't just entertain and educate,we also touch the hearts of the readers💐






Page 27
Koba komai Mubee ta tausaya wa Atif sosai,amma se tace "Ka dena cewa laifinane Ya Atif saboda kai kanka kasan bason aurenmu nake yiba dan haka koma me nayi banyi tunanin zaka zargeni ba."
"Ya Atif kai kanka ka sani ko a musulunce an hana aure dole danni wlh auren dole aka min da kai,yanzu ina amfanin auren dolen? Iyaye da dama suna wannan kuskuren akan 'ya'yansu wasu dan kwad'ayin abin duniya wasu kuma dan hangen wani abu amma ni ina ganin alhakin Ya Farhan ne ya kamamu sabida sam ba'a mishi adalci ba wlh,nizan tafi gida." Ta k'arashe maganar tana kuka sosai itama.
"Please Sis Mubee karki min haka please,naji duk abinda kikace kuma hakane amma yanzu kizo muje zan kaiki gida da kaina please Sis Mubee?"
Tausaya mishi tayi dan haka yana r'ike da hannunta ta bishi har gun motan ya bud'e ta shiga sannan shima ya shige suka tafi.
Tambayan shi takeyi "Wai ina zamu jene Ya Atif?"
"Kiyi hak'uri Sis Mubee gun Doctor zamuje domin ya gwadaki,addu'ata shine naki ya kasance negetive idan hakan ya faru zan barki kije ki auri Farhan tunda shine zab'inki."
Hawayene masu zafi suke bin kumatun sa yayinda yake gogewa da hannunsa yana driving cikin tashin hankali.
Mubinat ta rikice gabad'aya dajin kalamansa,koda wasa bata tab'a tunanin Atif zai fad'a mata hakaba.

Farhan kuwa bayan an dubashi ne aka bashi magani sannan Doctor yace "Ka dena yawan sa damuwa a ranka,dan inba hakaba zai haifar maka da babban matsala na ciwon zuciya."
Kamar zasuyi tambaya akan Atif dayake Family Doctor'n sune se kuma sukayi shuru suka wuce.

  Sun tafi bada jimawaba sega su Atif,kai tsaye suka wuce ciki babu b'ata lokaci Doctor ya d'ibi jinin Mubee ya fita.
Atif ya kasa zama yanata yawo a tsakiyan office tare da shafar sumar kansa.
Ita kuwa Mubee bazata iya daurewaba,dan haka ta tashi taje har inda yake "Ya Atif?" Ta kira sunanshi a hankali
Juyowa yayi yana kallonta batare daya ce mata komaiba. Shigewa jikinsa tayi tana kuka "I'm sorry Ya Atif,kayi hak'uri da abubuwan dana gaya maka d'azu rainane ya b'aci shiyasa."
Idanunsa ya goge sannan ya kamata da hannayensa biyu "Bakomai Sis Mubee,har abada bazaki tab'a yin laifiba a gurina komai kikayi ni agurina dai-dai ne,ban saniba ko k'aunar da nake mikine ya janyo hakan."
Kuka sosai kalaman sa suka k'ara sata,dan haka ta kasa cewa komai tana kwance a jikinsa yayinda ya rungumeta sosai yana k'walla.

Farhan ne d'auke da waya ya kira Abdullahi yana cewa "Abdullahi ina so ka nemamin yarinya dai-dai ni ko kuma ince kamar Habibty,hakan shi zaisa tunani ya ragu a zuciyata,dan Doctor ya tabbatar min da cewa ina dab da samun ciwon zuciya wanda nasan k'aunar Habibty ne ya janyomin hakan."
"Kana nufin ka shirya yin aure kenan?" Cewar Abdaullahi
"Haka nake tunani nima,inaga yin hakanne zai ragemin k'aunar Habibty,sedai ban saniba ko ita yarinyar zata samu hankalina a matsayina na mijin ta?"
"Please camn down Farhan,everything will fine okay?"
"I hope so too,byee."
Koda farhan ya katse wayan tunani ya shigayi wata rana shida Mubee tana kwance a parlour Umma tana bacci ya shigo da sallamarsa amma seyaji shuru.
Yana shiga ya hango wani abu farin kipe akan k'irjinta,a hankali yasa wayansa ya d'an turo farin abun batare daya tab'a jikintaba abun ya fad'o a k'asa,kodaya duba se yaga hoton sane.
Mamaki sosai yayi da ganin hakan dan a wannan lokacin basu fara soyayya ba. Motsin dayaga tayine yasashi komawa can bakin k'ofa tare da b'oye hoton a bayansa.
Tambayar kansa yakeyi "Ya akayi Sister Mubee ta samo hotona?"
Bud'e ido tayi tare da mik'ewa tsaye tana goge ido "Ya Farhan sannu da zuwa"
"Yawwa Shureim fa?"
"Kafin inyi bacci dai na barshi yana game anan."
"Ok tose anjuma"
"Yawwa Ya Farhan an bani sak'o daga Islamiyya akace in baka"
"Ok ina sak'on?"
D'aki ta shige sannan ta d'auko wasik'an ta mik'a mishi.
"Base na karb'a ba,ki karanta ina sauraron ki"
Ahankali ta bud'e ta fara kararu kamar haka.

_Assalamu Alaikum Malam Farhan,da fatan kana lfy?_
_Agaskiya Malam Allah ya jarabceni da k'aunarka ta yadda bazan iya misaltashiba,ina fatan zan samu amsa mai dad'i daga gareka._
_Na barka lfy,daga masoyiyarka Khadija Abbas..._

Mubinat tana gamawa ta kalli Farhan,shima kuma ita yake kallo.
"Ya Farhan sak'on kenan."
"Ok,tona gode amma kibata hak'uri domin yau na samu matar da zan aura"
"To yanzu dai mezan ce mata?"
"Abinda na gaya miki,da sak'onta yazo kafin minti biyar dana amince mata,amma ta makara domin kuwa wata ta rigata" ya k'arasa maganar yana dariya.
"Amma fa Ya Farhan nace mata baka da budurwa anan garin sedai ko'a can Madina shine ban saniba"
"Eh gaskiya kika gaya mata ai,nima bai wuce minti biyar da suka wuce bane na samu matar aure,Iyayenta kawai zan sanar sannan in sanar da ita yarinyar"
"To Allah ya sanya alkhairi na tayaka murna"
"Ameen thankyou." Sannan ya wuce ya barta a tsaye tana tunanin wace yarinya ce kuma Ya Farhan ya samu? To Allah dai ya sanya alkhairi koma wacece.
Shi kuwa Farhan d'aki ya dawo Shureim yana kwance,ganin shigowar shine ya mik'e
"Ya Farhan kaga hoton ko?"
"Na gani,amma yaushe Sisyer Mubee ta shigo d'akina harta d'auka min hoto?"
"Ai tana gyara muku d'aki inaga anan ta d'auka"
Ajiye hoton yayi sannan ya wuce toilet.
Shureim yayi tsalle yace "Na had'a soyayya, soyayya, soyayyaaa..."

K'walla Farhan ya share daga idanunsa bayan ya dawo daga tunani.
Ahmad ya shafi kafad'arsa yace "Haba Abokina ka daure mana"
"Tunba yauba abinda naketa k'ok'arin yi kenen Ahamad,amma inaga bazan iya bane."
Amal dai shuru tayi tana saura ronsu batace komaiba har suka iso gida.

Doctor ne ya shigo da peper a hannunsa,kunya sosai Mubee taji dan yadda yazo ya tatdasu rungume da juna.
Shi kuwa Atif ko'a jikinsa yana rik'e da hannunta suka taho gun Doctor.
"Doctor me result d'in Mubee ya nuna?" Cewar Atif hankalinsa a tashe.
"Atif result nata ya nuna negetive ne a yanzu,but na gaya maka baza muyi murnaba harse anyi mata test sau uku kuma duk bayan 3month ne zakuzo ayi,idan result d'in k'arshe ya nuna negetive tose muyi murna kamar dai yadda na maka bayani."
"Bakomai Doctor mungode sosai,insha Allah sauranma duk negative zai zama,yanzu babu wani magani da zaka bata kenan?"
"Eh gaskiya babu harse munga result munsan me take ciki,amma please kaikam ka tabbatar kana shan naka maganin don yana taimakawa sosai."
"Hmm,mungode Doctor amma ai nagaya maka cewa shan maganina bayi da amfani,muje Sis Mubee."
Doctor ya kalli Mubee yace "Ki tabbatar da yana shan maganinsa akan kari,dan yace bazai sha maganiba tunda hakan ya faru dashi,a tunaninsa zaki gujesane dan haka yake ganin cewa rayuwarsa bata da amfani indai baya tare dake."
K'walla ta farayi tare da cewa "Thankyou Doctor,kuma insha Allah zaisha maganinsa mun gode sosai." Sannan tayi saurin bin bayan Atif danya dad'e da ficewa waje.
Zaune yake cikin mota ya had'a kai ta siteri duk abin duniya ta dameshi.
Bayan ta shiga ta zauna ne ta kam'o hannunshi "Ya Atif,kayi hak'uri dan Allah,ka manta da alk'awarin dana maka? Ako wace irin haline bazan tab'a rabuwa dakai ba muna nan a tare."
Murmushi yayi tare da share hawayensa yace "Thanyou Sis Mubee" sannan ya ja mota se gidansu.
Kallonsa takeyi tare da tambayarsa "Meyasa ka kawomu gidan Abba kuma?"
"Sis Mubee yana da kyau in sanar dasu Abba halin da nake ciki kafin mu koma gidanmu."
Yana kaiwa nan ya fice daga motar Abba yana kallo a parlour tare da Umma.
Bayan yayi sallama sun gaisa ne yace "Abba ga Sis Mubee zataci gaba da zamanta anan har tsawon wata tara kafin insan me nake ciki,Abba karka tambayeni dalilin hakan Ya Musty zaizo yayi muku bayani anjuma." Yana kaiwa nan ya fice lokacin Mubee tana k'ok'arin shigowa parlour se suka had'u a bakin k'ofa.
"Ina zakaje Ya Atif?"
"Zanje in duba Farhan ne ki shiga ina zuwa."
Babu musu ta shiga jikinta a sanyaye. Ganin ta shigene yasashi yin sauri ya shige motarsa tare da barin cikin gidan...


                               Team #KNJ

KOMAI NISAN JIFAAWhere stories live. Discover now