42

307 20 0
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

      by maman shureim
             🌺sad-nas🌺

*©Pure Momment Of Life Writers*
         We don't just entertain and educate,we also touch the hearts of the readers❤






Page 42
  Tana kwance taji wayarta ya fara k'ara,koda ta duba bak'uwar number ta gani,ta d'auka tare da cewa "Hello"
Wani daddad'ar murya taji yayi magana a hankali "Habibty"
Cikin mamaki taji muryan Farhan,to a ina ya samu number na kuma? Katse mata tunanin yayi da cewa "Kince bana miki hira kamar Atif?"
"Eh mana Ya Farhan"
"Uhum me kike so ince miki to?"
"Babu kawai dai ka saki jiki dani tunda nima k'anwarka ce"
"Ok zanyi k'ok'arin hakan"
"Gaskiya ya kamata kagafa tare zamu zauna yanzu idan su Ummi suka tafi"
"You know what Habibty?"
Cikin sonji me zai fad'a tace "Seka fad'a"
"I will gonna miss them Habibty,i love my parent so much and i don't wanna miss them serioursly."
"Eyyah dama haka rayuwa take Ya Farhan,yau ina Umman Amal? Koda wasa bamu tab'a kawo hakan zai faruba,amma dayake rayuwace kowa da yadda Allah ya tsara mishi yau an nemeta an sara..."
Jin shuru da Mubeenat tayi ta kasa k'arasa maganar saboda k'walla daya zo mata yasa Farhan yayi saurin gane cewa kuka takeyi,hankalinsa a tashe yayi magana cikin rarrashi "Habibty are you craying? Pls stop it i don wanna see you craying and i don't know why"
"Habibty,please ans me okay?"
Cikin jin dad'in yadda ya nuna kulawarsa a gareta ta share k'wallan tare da cewa "It's okay i'm fine now"
"Are you sure?"
"Umhum" ta bashi ansa.
"You know what Habibty? When ever i'm talking to you i'm just so happy and kuma bansan dalili ba?"
Murmushi tayi mai d'an sauti "Yaya Farhan kenan,wato dai kana so in dena kuka shiyasa ka gayamin haka ko?"
"Uhum,is not like that Habibty i'm serious"
Bata san me zatace dashi ba dan haka tayi shuru tana murmushi a b'oye.
"Habibty are you there?"
"Yeah"
"Then meyasa kikayi shuru,kodai kin fara jin bacci ne?"
"A'a kawai dai bansan me zance maka bane"
"To shikenan,kince bana magana sosai shiyasa na kiraki dan in miki hira,ina fatan kinji dad'in hiran namu duk dadai nasan ban iya kamar Atif ba but i try ai ko?"
"Hhhhh sosai ma kuwa ai gara hakan"
Murmushi yayi mai sauti sannan yace "Alright Habibty,na miki hira nizan kwanta ma'assalam"
"To nagode sosai bissalam"
"Kinji Abdullahi ko? Wai dawa nake hira haka?"
"Hhh ina jinshi"
"Bari in bashi seki bashi amsa"
"Ok" ta fad'a tana dariya.
"Habibty?" Dariya Mubeenat tasa tare dayin magana cikin harcen turanci "Ya Abdullahi harda kai?"
"Ok kina nufin shi kad'ai ne zai kiraki da Habibty?"
"Rufa min asiri ba haka nake nufiba,shima ai a bakin Ummi yaji"
"To indai hakane shi meyasa baki mishi tambayar da kika min ba?"
"Hahhh haba Ya Abdullahi karka min wata fassara daban please" tana dariya.
"Ai nama yi miki..." karb'an wayar Farhan yayi yasa a kunne a lokacin Mubeenat tanata dariya tare da cewa "A'a kayi hak'uri kaima ka kirani da Habibty'n shikenan?"
Murmushi Farhan yayi tare da cewa "Nidai ban amince maka da hakanba ka kirata da sunanta koba haka bane Habibty?"
Dariya Mubeenat tasakeyi "Ya Farhan karka had'ani da shi fa nidai ba ruwana"
Shima dariyan yayi tare da cewa "Ok Habibty good night"
"Good night" sannan ta ajiye wayar tana dariya.

Washe gari da safe kuwa ana zaune ana breakfast gabad'aya hankalin Farhan akan Mubeenat yake,ita kuwa abincinta kawai takeci.
"Habibi yaya dai,bangane makaba kwana biyunnan fa" Cewar Abbi.
Dukkanninsu suka maida dubansu kan Farhan,murmushi kawai tayi tare da cewa "I'm fine Abbi"
Kallonsa kawai Mubeenat tayi sannan tace "Abbi duk damuwarsa shine zaku tafi ku barshi anan shi kad'ai right Ya Farhan?"
Kallonta yayi tare da cewa "Yeah it's true" yana mata murmushi itama haka. Kallonta ta mayar dashi gun Ummi tare da cewa "Amma ai Abbana ma a matsayin Abban shi yake hakama kuma Ummana ko Ummi?"
"Kinyi gaskiya Habibty,sannan gashi da aboki Atif ga kuma k'anne har biyu Ke da Shureim"
"Ehen Ummi gaya mishi dai,harma da Amal kinga mu ukku ma kenan" ta k'arashe maganar cikin zolaya.
"Keba K'anwarsa bace kawai Mubeenat,burina shine in had'a zuriya da Aminina wato Mahaifinki"
Kunya sosai mubeenat taji da maganar Abbi dan haka d'aki ta nufa cikin jin kunyarsu.
Farhan ya kalli Abbi nashi sannan ya kalli Ummi se yayi murmushi.
Kakansu kuwa magana yayi cikin zolaya "Idan kuma Farhan d'in baya so se'a bawa Abdullahi kafin mu koma se'a tsayar da maganan aure kawai."
Cikin zolaya Abdullahi yace shikenan kuwa Abbi dama yace min baya sonta."
Da sauri Farhan ya juyo yana kallon Abdullahi,su Ummi kuwa se dariya suke mishi.
Mik'ewa yayi tare da jan kunne Abdullahi yace "I lost my apatite" sannan ya koma parlour ya zauna sunata dariyan shi.

Abbin Farhan da Abban Mubeenat ne zaune suna hira inda Abbin Farhan yake gaya mishi burinsa shine ya had'a Farhan da Mubeenat aure inhar hakan zai yuwu.
"Nayiwa Farhan magana akan hakan,amma dai baice komaiba tukunna inaga mud'an bashi lokaci kafinnan sun sake shak'uwa da ita Mubeenat d'in nasan wata rana da kanshi zaizo min da zancen."
"Ba komai Aminina Allah ya tabbatar da alkhairi ya kuma had'a kawunansu" cewar Abban Mubeenat.
"Ameen" sannan sukaci gaba dayin hirarsu.

Gidansu Amal kuwa bayan Samira ta d'aga hankalinta ne ta nuna lallai da gaske zasu tafi shine Abban Amal yace da ita ta zauna zai aureta domin ya maye gurbin Umman Amal da ita.
Murna agun Samira ba'a cewa komai,nan Abban Amal yajewa Abban Mubeenat da zancen aurensa da Samira.
Abban Mubeenat baiyi mamakiba saboda maganganu da suke yawo a gari kan cewa da hannunsu Samira akan b'atan Umman Amal,sannan ga maganar da Amininsa wato Abbin Farhan ya sanar dashi kamar dai yadda Kakan Farhan ya gaya mishi cewa akwai asiri a tattare da Abban Amal dan haka a dage mishi da addu'oi.
Tun daga lokacin Abban Amal yana iyakan k'ok'arinsa na mishi addu'oi da kuma karya sihiri na ganyen magarya da akeyi,wanda ko an mishi aka bashi ruwan a gora indai yakai gida tozai gayawa Samira komai da aka gaya mishi a waje,ita kuwa seta ce to Abban Amal aise a gwada.
Amma yana barin gurin zata zubar da wannan maganin da aka bashi setayi dabara ta d'ura wani ruwan maganin da Malam na gura ya basu.
Shiyasa abun nashi yaketa gaba2 har'i zuwa yanzu dayazo musu da maganar auren Samira.
Babu yadda suka iya dashi tunda baya d'aukan shawaran kowa sena Samiran,dan haka aka zuba mishi ido ana tayashi da addu'a.

Yaune su Ummi suka koma k'asar Madina,inda suka bar Farhan cikin kewa sosai.
Kafin su tafi sunje Company sau biyu suna ganin yadda ayyuka suke gudana.
Abbi nashi yace lallai yaba Mubeenat babban matsayi ata gunshi dukda dai secondary skul kawai ta gama a yanzu. Haka kuwa akayi yace ba damuwa amma har yau bata fara zuwaba kuma ta nemi alfarma agun Abbanta daya nemawa Amal ma sesu dinga tafiya tare kota d'an samu sauk'in b'acin rai da take fama dashi a gida.
Yau ne Farhan ya dawo gidansu Mubeenat da zama gaba d'aya,dan seda yayi kwana biyu acan kafin yau ya dawo.
Mubeenat da Shureim ne suka k'arasa gun motar da murnansu "Ya Farhan sannu da dawowa"
"Thankyou Habibty" sannan ya kalli Shureim tare da d'aukan shi sama "Atif ya tafi ko?"
"Eh sun tafi tunda sassafe" cewar Shureim.
"To Allah ya kaisu lafiya"
"Ameen" suka amsa dukkansu sannan Mubeenat ta kamo kit nashi tana ja.
"Habibty stop please" cak ta tsaya tana jiran mezai ce. Sauk'e Shureim yayi yaje ya karb'i kit d'in a hannunta "Is too heavy Habibty take this" ya bata k'aramin kit d'in sannan Shureim ma ya d'auki wani kayan suna tafiya can side d'in su Ya Atif d'in.
Dama Mubeenat ta gyara komai a d'akin yayi tas gashi se k'amshine kawai yake tashi. Shiya karb'i kayan ya kai har zuwa ma'ajiyarsa wato walldrop dake d'akin babbane sosai gashi fari tas.
Mik'ewa tayi tare da cewa "Bari naje na kawo maka abinci"
"No Habibty i'm okay"
"A ina kaci abincin kenan?"
"Mun fita da Ahmad d'azu munci abinci"
"Waye kuma Ahmad Ya Farhan,har kayi abokai kenan?"
"Hhhh Habibty wanda kikace muje mu sayi mota agunsu ne,mun d'an saba dashi Ahmad d'in shine dai abokina a yanzu"
Murmushi tayi tare da cewa "A hankali zaka zama d'an gari,toni zan koma ciki me za'a dafa maka zuwa anjuma?"
"Anything Habibty" ya fad'a yana mata murmushi.
"Ok kad'an huta yanzu to,Shureim muje ko?"
"Kibarmun shi mana yamin hira"
"To shikenan,se anjuma" sannan ta fice yana binta da kallo dan kayan da Ummin shi ta kawo mata ne a jikinta yayi mata kyau sosai doguwar rigar...

                       Team #KNJ

KOMAI NISAN JIFAAWhere stories live. Discover now