36

254 20 0
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

     by maman shureim
            🌺sad-nas🌺

*©Pure Momment Of Life Writers*
        We don't just entertain and educate,we also touch the hearts of the readers❤






Page 36
Tun daga wannan rana Atif yaci gaba da zama a gidansu Mubeenat har'i zuwa yanzu.
Shine mai kaisu makaranta ya kuma d'auko su,hakan baisa yabar Aisha ba duk haka yake hidima dasu tare da nuna musu k'auna sosai.
Haka kuwa zai kaita gidan friends nata koda biki akeyi ko wani hidima duk shine komai nata a yanzu,hakan yasanya Mubeenat sakewa da Atif kuma sabon shak'uwa ya k'aru a tsakaninsu wanda ita Umma harta fara tunanin ko soyayya ce,se daga baya ta gane cewa kawai soyayyace ta Yaya da K'anwa.

Gidan su Amal kuwa yau kusan sati biyu kenan amma Samira batayi batun tafiya ba,kuma Umman Amal ta samawa Sagir aiki yana samun kud'i har yayi clean.
Duk wani shiga da fice da Abban Amal yakeyi a wannan gidan akan idon Samira,har tana sha'awan inama da itace take auransa,dan gidan da tayi aure daga farko sam bataji dad'i ba.
Wata rana suna hira da k'anin nata Sagir inda yake cewa "Toke yanzu yaushe zaki tafi kiyi aure?"
"Kai dalla rufe min baki,kana nufin zan bar nan ne?"
"To dama anan zakici gaba da zama?"
"Wlh babu inda zani kana gani muna cin bulus mun huta da biyan haya ganka fa yadda kayi fresh ai wlh Sagir bank'i ace Abban Amal ya aureniba tunda dama mu k'awayene kaga shikenan zamuyi zaman lafiya kaima kuma ci gaba zata sameka kome ka gani?"
"Tabd'i! Lallai baki da hankali,yanzu har kina tunanin Mijin k'awarki zai aureki?"
"Eh mana inda rabo wlh sekaga abu ya yuwu"
"Hhhhh wlh kinban dariya,ki ganshifa ki kuma kalli k'awarki da 'yarta duk sun fimu da komai."
"Kaifa har yanzu baka gama wayewa ba Sagiru,ai inda kud'i ya zauna wlh duk clean zamuyi harma mufi 'yan gidan,kuma kaima base ayi na gidaba da Amal gata kyakkyawa mai kama da mamanta"
Nanne Sagir ya washe baki "Amma fa kince wani abu,sedai kuma ni nfi son k'awarta Mubeenat kinga ita iyayenta masu kud'i ne sosai se muyi auren jari"
"Kai rufa min baki gara muyi dai-dai ruwa dai-dai tsaki ina kai ina wannan Mubeena take ko Mubeenata,wannan Yayan nata ma kad'ai ya isheka wlh kanaga koda yaushe suna tare karma ka fara ka rufa mana asiri Amal d'inma ai tafi k'arfinka dandai muna gida."
Haka dai sukaita hirarsu suna tsara yadda za'ayi, "Sagir yace indai zan auri Amal kibar komai a hannuna sekin zama Amarya a gidan nan wlh"
"Yawwa d'an uwa shiyasa ai bana son rabuwa da kai duk lalacewa gara muna tare"
"Wannan haka yake,yanzu wani Malami zamu samu dazai mana komai cikin sauk'i"
"Kasha kuruminka ai dole ka koma k'auyenmu gun Malam na ruga kamishi bayanin komai sannan ka ajiye mishi kud'i shikenan an gama"
"Wlh kamar kina raina,gobe zanyi sammako inje in dawo da wuri,amma fa kema zaki kawo wani abu yanzu agurin ki"
"Karka damu mu had'u da daddare zan baka,ai kasan Abban amal d'in akwai kyauta hakama ita k'awar tawa duk tara kud'in da suke bani nake yi"
"Yawwa tose daren kenan."
Haka suka rabu da wannan shawaran nasu washe gari da safe kuwa ya d'au hanya se gun Malam na ruga.
Bayan ya gama yiwa Malam na ruga bayanin komai shine Malam yace "Wannan abu ne mai sauk'i mazargin wandonsa kawai nake so ka kawo min akwai abinda zanyi dashi idan ya kwana d'aya aguna seka mayar ka kuma tabbata ba'a wanke mazarginba kafin yasa."
"Bakomai dama tunda mukaje gidan nace ya dena kai wanki zan dinga mishi harda gugama ni nake mishi,dan haka zanje in kawo maka yau d'innan."

Sagir yana dawowa gida ya tambayi Umman Amal "Aunty nace kayan Alhaji bai taru bane in wanke?"
"Haba Sagir ka dinga hutawa mana"
"Ai dayake yau d'in ina hutu ne nace gara in rage wankin"
"To shikenan bari na fito maka dasu"
"To Aunty" sannan ta wuce ta d'ibo mishi kala biyar ne ta zuba a k'asa ya kwashe yayi gaba.
Seda ya gama wankin tas ya shanya sannan ya faki ido babu kowa atsakar gida ya zaro mazargin wando d'aya ya nufi k'auye segun Malam na ruga.
"Gashi Malam anyi dace"
"To shikenan kaje se gobe da yamma ka dawo"
"To Malam nagode"

Washe gari da yamma ya koma ya k'arb'o inda Malam yace "Ka lura dakyau duk randa yasa wannan kayan to a wannan ranan zakaga aiki tashi kaje"
"To Malam godiya muke sena sake dawowa."
Sagir yana dawowa ya kwaso kayan yasa mazargin daya ciran sannan ya gogesu tas da dutsen guga yaje ya kaiwa Umman Amal,inda tace Amal ta karb'i kayan takai d'akin Abbanta.
  Bayan sati biyu dayin hakan kenan Abban Amal baisa kayan ba.
  
Acikin sati na Ukkun ne Abbi d'in Farhan da Ummin shi da Abdullahi d'an Yayan mamanshi se kuma Kakansu dashi kanshi Farhan d'in suka sauka a garin Abuja,daga nan kuma suka sake shiga jirgi zuwa Gobme inda su Abban Mubeenat da Yaya Musty da kuma Atif da Shureim sukaje tarar su.
Umman Mubeenat kuwa se kici-ciki sukeyi a kichine ita da Mubeenat da Amal suna had'a musu abinci wasu a parlour'n Umma akan daining wasu kuma acan parlour'n Abba.
Bayan sun gama kimtsa komaine suka wuce shiryawa dan duk sunyi wanka dama,Amal ma gida ta wuce taje ta shirya sannan ta dawo suna zaman jiran isowar bak'i.
"Wai haka zaku bar fuska fari sol babu ko kwalli?" Cewar Umma.
Dariya kawai sukayi batare da sunce komai ba suka wuce d'akin Mubeenat suna dariya.
"Nidai wlh bazanyi wani kwalliya ba sekace zamuje biki" cewar Mubeenat.
Amal ma dariya take "Dama nikam kunce natural face na yafi min kyau dan haka ke sekiyi d'an ado"
"Wlh babu abinda zansa" suna dariya se sukaji sallamar Aisha.
"Bak'in basu iso bane har yanzu?"
"Eh anje d'aukosu dai"
"Ina Umma?"
"Tana ciki"
"To bari naje mu gaisa tukunna karku isheni da surutu banje na gaisheta ba."

Sauk'ansu kenan suka fito inda su Abba suka hangosu tun daga nesa,Shureim yace "Ya Atif wa'incan turawanne bak'in namu?"
"Hhhh ba Turawa bane Larabawane su."
Da sauri su Abba suka nufesu cike da Murna suma kuma haka.
Tun daga nesa Farhan ya hango Shureim yana rik'e da hannun Atif,a hankali ya fara mishi murmushi tare da cewa "Shureim right?"
Murmushi Atif yayi tare da cewa "Yeah it's him,you'r all wlcume"
"Thanks" cewar Farhan sannan ya kamo hannun Shureim yana mishi magana cikin harcen turanci,shi kuwa Shureim se bashi amsa yakeyi tare da k'ura mishi ido kamar zai had'iye shi.
Sanda sukayi musu sannu da zuwa sannan suka nufi gun moto suka wuce zuwa gida.

Gidansu Amal kuwa yau dai wannan kayan Abbanta yasa.
Kuma tunda yasa kayan se yaji wani iri kaha a jikinsa "Hajiya"
"Na'am Abba Amal harka shirya zaka fita kenan?"
"Eh zan fita ina Samira fa?"
"Samira kuma?" Ta tambaye shi.
"Eh ya kamata na ganta ai kafin na fita"
Mamakine sosai ya kama Umman Amal dajin abida yake fitowa daga bakin mijinta.
"To muje zuwa waje sena mata ganaga ko?" Cewar Umman Amal.
Nan ya fara washe baki yana cewa "To,to shikenan muje"
Haka suka fito tana gaba yana biye da ita a baya "Samira" Umman Amal ta k'wala mata kira.
"Na'am gani"
Nan Umman Amal ta kalli Mijinta "To gata nan Abban Amal"
Yaci gaba da washe baki "Dama cewa nayi a kiraki muyi sallama nizan fita"
Daga ita har Umman Amal mamakin jin kalamansa sukayi,amma acikin zuciyarta cewa tayi "Lallai aikin Malam na gura yayi kyau" a fili kuma se tace "To Abban Amal Allah ya kare,sannan ta mik'e ta wuce ciki yanata binta da kallo,ita kuwa Umman Amal aka barta da kallon mamaki "Tofa miye kuma hakan kenan ni Zainabu...?"


                               Team #KNJ

KOMAI NISAN JIFAADonde viven las historias. Descúbrelo ahora