20

358 23 0
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

     by maman shureim
           🌺sad-nas🌺

*©Pure Momment Of Life Writers*
        We don'nt just entertain and educate,we also touch the heart of the readers

Wannan page d'in nakune Aisha Ali Garkuwa tare da Billylosh Amarsu😜ina maraba da dawowar ki.
        I LOVE YOU BOTH
                ❤❤❤



Page 20
Su Umma sun dad'e sosai kafin suka tafi.
Atif ya d'an samu sauk'i ba laifi,dan haka ya nemi da a sallamesu amma se Doctor yak'i.
Lokacin da Abba yazo ne Atif ya sake dagewa lallai shi bazai kwana a asibitiba sabida yaji sauk'i,haka Doctor ya sallame su.
Ruwan d'umi ta had'a mishi yayi wanka bayan sun dawo gida.
Sun gama komai nasu sukayi shirin bacci kamar dai yadda suka saba,sedai yau Mubinat shiri na musam man tayiwa Atif domin karb'ansa a matsayin mijinta.
Yayi mamakin ganin rigar baccin data sa,tun a lokacin ya shiga wani irin yanayi bare kuma data zo jikin shi.
Mubinat ta dad'e tana tuna kalaman Aisha,dan haka ita da kanta ta fara shige masa tunda dama can sun saba wasan ninsu. Shi kuwa Atif baya jin k'arfi a jikinsa kamar dai yadda yake da,dan haka yace da ita "Sis Mebee"
"Na'am" tace dashi
Cikin siyasa yayi magana "Inaga banda k'arfi sosai a jikina,kuma bana so ki rainani,shiyasa nake ganin gara mu bari ko zuwa gobe indai hakan ba matsala."
A cikin ranta dad'in maganar sa taji,amma a fili seta ce "Haba Ya Atif yanzu har kana tunanin akwai raini a tsakanina da kai?"
"Ba haka nake nufiba,ina nufin kar in kasa gamsar dake amatsayin ki na amarya ta." Ya k'arashe maganar cikin zolaya.
"Hhhhhh Ya Atif kenan,to shikenan ai dayau da goben duk d'ayane,Allah ya kaimu Allah kuma ya baka lafiya."
"Ameen" yace da ita yana shafar kanta kamar wata baby.
"Jikinka yana min kyau sosai Ya Atif,tun ada har ina gayawa Amal tace min kodai sonka nake,nace mata haba ke kuwa babu hali ince wani abu akan ya Atif se ina sonshi? Tace eh mana."
"Hhh oh Sis Mubee kinban dariya"
"Serious wlh"
"To ai gashi gabad'aya nama na zama mallakinki ba jikina kad'ai ba."
"Hmm to ai shine nima nake wannan tunanin yanzu."
Haka dai sukaita hiransu suna soyayya har sukai bacci.

Washe gari bayan sunyi breakfast ne wayan Atif ya fara ringing,d'auka yayi tare da cewa "Hello Doctor,wlh jiki da sauk'i sosai,ameen nagode,ok toba damuwa insha Allah." Sannan ya katse ya kalli Mubinat tare da janyota yace "Doctor ne ya kira yaji yaya jikin nawa."
"Ok" tace dashi sannan suka jiyo ana nocking tare da sallama.
Atif ne yaje ya duba,Farhan ne a tsaye yana sanye da farin suite yayi matuk'ar kyau sosai.
"Ah Farhan,sannu da zuwa bisimillah mana."
"A'a ba jumawa zanyi sosai ba,nazo ganinkane amma bari mu gaisa da Sis Mubee idan yaso semuje daga waje."
"Ok hope dai lafiya ko?"
"Eh lafiya lau"
Muryan Mubinat ce tana cewa "Ya Atif kaida waye?"
Atare suka shigo,tun daga nesa ta hango Farhan.
"Laa Ya Farhan sannu da zuwa" sannan tayi saurin shigewa d'aki dan riga da wando ne a jikinta babu ko d'ankwali tayi adon safiya tsaf da ita.
Sanye da himar ta fito ta zauna kusa da Atif tace "Ya Farhan ina kwana"
"Lafiya, ya mai jiki?"
"Alhamdulillah jiki yayi sauk'i ko Ya Atif?"
"Kallonta yayi sannan yayi mutmushi yace "Eh alhamdulillahi zamuce"
"To Allah ya k'ara lfy nizan wuce"
"Da sauri haka Ya Farhan,ka tsaya mana koda coffee ne seka sha"
"Thankyou ak'oshe nake" yana murmushi
"To shikenan,mun gode a gaida su Umma da Shureim"
"Zasuji"
Sannan suka fita shida Atif tanata binsu da kallo.

"Atif dama ranan da aka d'auke Sis Mubee akwai wanda na kama na damk'ashi a hannun su Ahmad,sun bincikesa sosai shine yake gaya musu cewa wanine mai suna Mujahid ya turosu tun daga garin kaduna."
"Dama mun b'oyewa su Abbane dan gudun kar..."Yanzu kana nufin Mujahid ne ya turosu?" Atif ya tambaye shi cikin mamaki
"Yes abinda ya gaya musu kenan,Atif please ina so in nemi wata alfarma agareka,dan Allah ka kiyaye duk wani abu daka san bai halattaba,kodon d'aurewan zaman lafiya tsakaninka da Sis Mubee da kuma su Abba."
"Yana da kyau ka rik'eta kodon mutunta su Abba please,shine kawai dama abinda ya kawoni,nizan tafi."
Jikin Atif yayi sanyi dan ya fahimci cewa sunsan komai kenan dan yasan dole mutumin zai gaya musu abinda ya had'ashi da Mujahid harya turosu garin nan,kuma ya fahimci maganga nun Farhan sosai. Dan haka yace "Nagode sosai Farhan,nagode da irin rufamin asiri dakayi wajen b'oyewa su Abba, dan badan hakanba da sunsan abinda na aikata a baya wanda zasuga kamar laifinane d'auke Sis Mubee da akayi."
"Sannan insha Allah zan kiyaye bazan tab'a cutar da Sis Mubee ba,zan rik'eta da amana insha Allah nagode sosai."
"To Alhamdulillah nabarku lafiya,yawwa inaga bai daceba ta dinga kiranka da Ya Atif,saboda kai mijintane a yanzu,kaima kuma bai halatta ka kirata da Sis Mubee ba,hakan bai halattaba a musulunce."
"Ok,zamu gyara mungode."
Yana tsaye har Farhan yabar cikin gidan sannan ya dawo ciki yace da Mubinat zai fita.
"To amma kafin ka fita,hiran me kukeyi da Ya Farhan?"
"Don't worry,idan na dawo zan gaya miki"
"To wai ma ina zakaje ne?"
"Kin manta yauni ango mai jiran gado ne,kedai ki jirani bazan dad'eba ai my love." Ya manna mata kiss sannan ya fice tana binshi da dariya...

Shuru shuru Atif bai dawoba har bayan sallan isha,sannan kota kira number'n shi baya d'auka. Hankalinta ya tashi sosai.
  11:15pm tajiyo horn nashi,da sauri ta fito tsakar gidan tana tsaye zaman jiransa.
Ko daya tsaya da motan amma shuru bai fito daga ciki ba,da sauri ta k'arasa ta bud'e zaune yake kansa bisa siterin motan.
Kansa ta d'ago "Ya Atif lafiya,jikin nakane ya tashi kuma,ina ka shiga haka naketa kiranka baka d'auka,me yake faruwa ne?"
Hawaye ne cab'e-cab'e akan fuskarsa kaman bana miji ba. Hankalin Mubinat ya sake tashi fiye dana dah.
Kan ta sake ce wani abu ya wuceta idanunsa jajawur ya shige ciki batare daya kalleta ba.
Rufe motar tayi ta biyo bayanshi,koda ta shigo d'akin shi kuwa yana wanka a toilet.
Fitowa yayi yana goge jiki,rungumesa tayi tana cewa "Ya Atif me yake faruwa ne,me yake damunka please kayi  magana mana."
Kallonta kawai yakeyi sega k'walla yana zubowa. Turashi tayi zuwa gado tare da kashe wutan d'akin ta cire kayan jikinta sannan ta janye tawul nashi ta fara nuna mishi irin son da take mishi inma hakan shine matsalar sa.
Tun baya biye mata har suka shagalta sosai dukkansu. Kuka taji Atif yanayi da murya sosai wanda ya d'aga mata hankali,shine daga samanta tana jin yadda hawayen sa suke zuba a fuskarta har zuwa wuyanta.
"I'm sorry Sis Mubee,i'm so sorry,please forgive me." Shine abinda ya furta sannan ya fice zuwa d'akinsa yasa key.
Binsa tayi tanata magiya amma sam yak'i kulatama bare ya bud'e mata k'ofan.
Mubinat tafi awa uku a tsaye agun tana buga k'ofan amma duk a banza,kukansa kawai takeji tare da surutai da yakeyi wanda bata san mema yake fad'a ba.
A haka ta wuce d'akinta ta kwanta har bacci yayi gaba da ita batare data saniba.

Da asuba ta mik'e ta nufi toilet bayan ta fito ta gabatar da sallah sannan ta nufi d'akin Atif.
Bugawa sau d'aya kawai tayi yazo ya bud'e mata k'ofa tare da saurin rungumeta.
"Sis Mubee i'm sorry for what happen yesterday night,kije ki shirya zamuje wani guri ne yanzu."
Mamakine fal a fuskarta "Ina zamuje da asuba haka,sannan baka min bayanin abinda ke faruwa ba na jiya."
"Zan gaya miki komai,but pls kije ki shirya mu tafi."
Ba musu taje ta shirya ta fito,lokacin yana sa wani farin peper a aljihunsa.
Rungumeta ya sakeyi sosai yana juyi da ita da 'yar k'walla a idonsa sannan ya rik'o hanunta suka fita hargun mota.
Tafiya sukeyi tanata bin hanyan da kallo,shi kuwa ko kallon gefenta yak'iyi bare yace da ita wani abu,dan haka itama  shuru tayi tana kallon shi sosai yayinda taga yana horn a k'ofar gidan su.
"Ya Atif lafiya kuwa,meya faru a gidan namu ne,me kake b'oyemin Ya Atif?"
"Kiyi hak'uri aimun iso"
Kallon gidan nasu ta shigayi amma bataga  wani abu daban ba.
A tare suka fito suka nufi parlour'n Abba,ana zaune kamar yadda suka saba da an dawo daga masallaci se'a zauna gaba d'aya ayita hira.
Su kansu Abba sunyi mamakin ganin su Atif da asuba haka. Bayan an gaisane Atif ya fara magana kamar haka
"Abba dan Allah kuyi hak'uri dani da kuma abinda nazo dashi."
Duk sukayi shuru suna sauraronsa da maida hankalinsu zuwa gareshi.
Shi kuwa Farhan ya d'auka Atif zai fad'awa Abba abinda ya farune tsakaninsu da Mujahid.
Atif yaci gaba da cewa "Abba ga Sis mubee nazo da ita,dan Allah kuyi hak'uri,Sis Mubee gashi"
Juyowa tayi tana kallonshi tare da k'arewa abinda yake mik'a mata kallo,farin peper ce dan haka tasa hannu ta karb'a tana kallonshi.
"Sis Mubee,na sakeki saki d'aya,dan Allah kiyi hak'uri ki yafemin."
Yana kaiwa nan ya mik'e da sauri ya fice,akabar su Abba da Innalillahi,ita kuwa Mubinat da gudu tabi bayanshi tana kuka tana cewa "Ya Atif saki fa kace,mena maka dan Allah da zaka sakami da saki? Please Ya Atif kayi hak'uri ka mai dani wlh ina sonka please kace ka mai dani mu koma gidanmu Ya Atif.......😔


                                    Team #KNJ

KOMAI NISAN JIFAAWhere stories live. Discover now