62

463 27 0
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

      by maman shureim
            🌺sad-nas🌺

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
    ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛ'Ş

#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com





Page 62
Bayan sun gaisa ne Farhan yace da Anwar "To bissimillah mana mu k'arasa ciki"
Amal da Aisha suka wuce ciki su Farhan kuwa suna biye dasu a baya.
Mubeenat suka hango ita da Shureim sai fama kai abinci suke yi zuwa side d'in su Ya Farhan,ganin hakanne yasa sukayi saurin k'arasawa gurin ta tare da cewa "Amarsu da kanki? Ayi mana afuwa kije ki huta"
Wani wawan harara ta bisu dasu tare da mik'a musu suna mata dariya.
Juyowar da zatayi danta koma ciki sai taga Farhan da Anwar,dariya yazo mata amma saita wayance tare dasa hannunta ta kare bakin ta.
Ta gefen inda take ya k'araso yana kallonta "I'm sorry Habibty"
Wani irin kallo ta watsa mishi tare da cewa "Sorry? Hmmm!"
Shirin wucewa take yayi saurin tareta tare da cewa "Ooh come on Habibty so kike Anwar yamin dariya?"
Anwar dake tsaya yana jiransa yace "Ai ina kanyin dariya kam"
Kallon Anwar d'in tayi sannan ta sake kallon Farhan tayi magana cikin shagwab'a "I'm happy to see you Habibi"
Dad'i yaji sosai "Thankyou Habibty,kinsa naji dad'i"
"Zan iya wucewa?"
"Sure" sannan ya matsa gefe ta wuce Anwar yana mata dariya.
Tana isa ciki gun Ummi ta wuce sai shagwab'a ta Ummi take,Umma tana musu dariya tare da cewa Mubeenat "Wai ke bakya jin kunya ne god'ai-gid'ai dake a kan  k'afar ta?"
"Kunyan me zata ji kuma,ni bana son irin wannan kunyan gara ta saki jikinta dani ta d'aukeni tamkar ke"
Haka dai sukaita hira bayan su Amal sun magane Mubeenat ta koma d'akinta suma suna nasu bidirin acan.
Bayan magrib su Ummi suka koma gidan su dasu Farhan dukka dama Farhan yabar komai a hannun Ahmad an sake gyara ko ina agidan dukda dai dama bayi da wani matsala.
Side d'in su suka nufa harda Anwar d'in anata hira bayan isha Anwar da Ahmad sukace zasu tafi Farhan yace "Bari in kira Habibty idan tana son ganina saina biku"
Wayarsa ya d'auka ya kirata sunata hira dasu Aisha ganin kiran sane yasa ta dakata tare da d'aukan wayar "Slm"
"Wslm Habibty me kikeyi?"
"Ba komai,hira muke dasu Aisha"
"Kina son ganina ne?"
"Karka damu nasan ka gaji dan haka ka huta kawai"
"Are you sure?"
"Yes"
"Alright i will call you later"
"Okay byee"
"Byee Habibty" sannan ya katse tare da ce musu "Muje in rakaku"
"Yi zamanka ai mu biyu ne" cewar Ahmad.
"To shikenan Anwar mun gode sosai fa"
"Don't mention Ango" ya fad'a suna dariya suka wuce.
Hiransu kawai sukeyi cikin harcen larabci gwanin ban sha'awa har kusan 10:22pm sannan kowa ya hau net yana damuwar sa,shi kuwa Farhan ya kira Mubeenat suna hira.
"Ni kayiwa haka ko Ya Farhan?"
"Habibty i'm sorry iddah fa kikeyi kuma aduk lokacin dana ganki ji nake kamar in sake furta miki cewa ina sonki,kuma kinga hakan bai daceba a musulunce shiyasa kawai nayi hakan,but ke kinsan ai bazan miki haka ba ko? sai da dalili"
"Hmmm nidai nayi fushi"
"Haba Habibtyna,i'm sorry for the second time,infact zanyi ta baki hak'uri har sai kin hak'ura"
"To ka shirya bani hak'uri dan ba yanzu zan hak'ura ba"
"Haba Habibty kina so ki hanani bacci ne? I'm so sorry please forgive me?"
"Nak'i d'in"
"Okay tell me,me zanyi ki min hak'uri?"
"Wak'a zaka min mai dad'i kuma da hausa"
"What?! Please ki canja Habibty ban iya wak'a ba i swear"
"Hhhh nidai sai kamin kafin in hak'ura"
"Habibty...?"
"Yes"
"Alright then"
         🎼🎼🎼🎼
In ina tafiya inna ganki zan duk'aa... In ina bacci inna jiki zan farka, bani fatan in kalleki kina yin kukaa... mai tab'a min ke nizann yimai duka, ni jarumine ni k'arfina zanyi rik'aa... sam karkiji komai sam karr kiyo shakka, rabuwa bamu yowa alk'awarii rik'ewaa... Yaaa salam Habibtyna karki barni...

"Hhhhhh lallai Ya Farhan a ina kaji wannan wak'ar harka haddace?"
"Habibty you are too much,i can't believe wai nina miki wak'a fa"
"Hhhh saura uku ma ai"
"No Habibty wannan ma a bakin Ahmad nakeji yana yiwa Amal shine nayi sata"
"Oooh to ban yadda ba copy-copy,nima kamin nawa daban"
"Haba my Habibty banyi k'ok'ariba kenan yanzu?"
"I'm just kidding Habibi wannan d'inma ban zata zaka yiba wlh dan nasan baka iya ba,amma fa kayi k'ok'ari kamar dama can kai kayi wak'an"
"Hhhh Habibty keba? Ina Amal?"
"Tana can parlour suna kallo a zee world"
"Ok but karfa ki gaya mata na miki wak'a"
"Ai harma nayi recording zan kuma sa mata taji"
"Habibty please?"
"Nak'i" ta amsa shi cikin zolaya"
"Ni kike yiwa haka ko? Ba damuwa nagode"
"Yawwa Ya Farhan?"
"Ahaan"
"Please ina neman wani alfarma a gareka"
"Ina jinki"
"Akan Ya Atif ne,gaba d'aya ya fita harka ta baya ma son ganina,sannan ya dena shan magungunansa please Habibi kaje kayi masa nasiha wata k'ila zai d'auka"
Shuru Farhan yayi na d'an wani lokaci sannan yace "I will do that tomorrow insha Allah Habibty ki dena damuwa"
"Thankyou so much"
"Always Habibty,sai kuma me?"
"Shikenan"
"Idan akwai wani buk'atun let me know please?"
"Babu Ya Farhan dama shi d'inne kawai, kuma na gode daka fahimce ni"
"Habibty can i ask you?"
"Yes ina jin ka"
"Kina son Ya Atif ne?"
Mamakin tambayan nashi taji sosai "Haba Ya Farhan,a tunanina kaine mutum na farko wanda ya sanni fiye da kowa ashe dai ba haka yake ba"
"No Habibty bawai dan abinda kika gaya min yanzu bane yasa nace haka,kawai dai tambaya ce,amma idan bakiji dad'in shiba mubar maganar and i'm sorry"
"Ba komai Ya Farhan,ai kana da daman yimin ko wace irin tambaya,gaskiya Ya Farhan ni ban tab'a son Ya Atif a matsayin mijina ba,sai dai a matsayin Yayana wanda na shak'u dashi nafi ji dashi kuma akan sauran Yayyuna,sai dai zaman da mukayi dashi na d'an watanni yasa shak'uwar mu tafi na dah wanda inaga shiyasa kuke min kallo kona fara sonshi ne."
Mubeenat taci gaba da cewa "Ya Farhan bazan b'oye maka ba,ina matuk'ar ji da Ya Atif yadda baka tunani domin ya kasance kanar soul mate d'ina ne,amma zuciyata mutum d'aya tak take k'aunar ya shige cikinta ya zamo abokin shawararta daga duniya har lahira wanda ba kowa bane wannan mutumin illa Farhan Abdulhali Taimoor,Ina k'aunar ka fiye da yadda nake k'aunar kaina Ya Farhan i love you,i love you so verry much kai kad'ai ne mutumin da zuciyata take son kasan cewa dashi kazamo Uba ga 'ya'yan da zan haifa,Ya Farhan ka jingine duk wani tunaninka a gefe domin addu'arka ta gama karb'uwa a kaina,ka riga daka gama dani shiyasa duk abinda Ya Atif yayi bana ganin laifinsa domin soyayya babu abinda bata sawa dukda dai akwai nashi kuskuren,dan Allah Ya Farhan ka rik'eni da amana please?"
Shuru Farhan yayi dan tunda Mubeenat ta fara bayani ji yake kamar ana busa masa sarewa mai dad'i wanda hakan yasa duk wani fanni na jikinsa sai daya tashi dan farin cikin jin kalaman ta,ita kuwa k'walla ne yake bin fuskarta wanda itama bata san da fitowar saba.
Farhan baisan sanda muryarsa ta canja ba yace "Habibty zaki kasheni ai irin wannan kalamai naki duk kin rikitani wlh nama rasa abinda zan ce miki"
Itama shuru tayi tana sauraron yadda taji muryarsa ya sauya gaba d'aya. Katseta yayi da cewa "Habibty i love you more than you do,a yanzu Farhan kamar sabon jaririn da aka haife shi yake,yadda kika renesa haka zai kasance miki farin cikina,insha Allah baza kiyi kuka dani ba Habibty ki kwantar da hankalin ki my Habibty"
"Good night" shine kawai abinda ta iya furta mishi sannan ta katse wayar.
Rufe idanu Farhan yayi tare da kwanciya akan gado yana mai jin wani farin ciki a ransa tare da lasan lips nashi yace "Habibty kin kasheni"
Muryar Abdullahi yaji yana cewa "Ta sumar da kai dai,ba kisa ba"
Tashi yayi zaune yace "Gaskiya love yayi Abdullahi,ashe dai da can cutan kaina nake tayi"
"Hhhh Farhan" sukaita hira daga nan suka kwanta bacci.

Vote and comment

                     Team #FARBEEN

KOMAI NISAN JIFAAWhere stories live. Discover now