15

344 31 0
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

       by maman shureim
             🌺sad-nas🌺

©Pure Momment Of Life Writers







Page 15
Gudu suke sosai da motar kaman zasu tashi sama. Sunyi tafiya na tsawon minti goma kenan sai ga wani yaro akan keke saura kad'an su bugesa amma Allah ya kare. Jin yadda motar ta taka birki ne yasa Mubinat ta farka tare da binsu da kallo.
Salatep d'in bakinta suka cire tace "Dan Allah mena muku,kuyi hak'uri ku mai dani gida dan Allah?"
"Hmm ki dena b'ata bakinki zamu rabu dake inhar mun sami abinda muke so."
Gefen glass take kallo ko zata gane ta inda suke tafiyan amma sam bata gane ko inaba.
Hakan yasa ta fara yin kuka tanata kalle-kalle,ai kuwa seta ga Almajirinsu Musa akan keke. Dabara ne yazo mata dan duk glass d'in motan arufe yake kota kirashi bazai jita ba. Rufe baki tayi kaman maijin amai tana cewa "Um um" tare da nuna musu bakinta da hannunta. Hakan yasa suka gane tare da sauke glass d'in motan na gefen baya.
Tana d'an fitar da kanta tayi saurin yin magana da k'arfi tace "Musa Mubinat ce dan Allah ka taimakeni d'aukeni suka...!
Rufe mata baki sukayi tare da shigo da ita suka manna mata salatep d'in suna cewa "Wato mu zaki mannawa hauka ko,zaki gane kurenki kuwa.
Tabbas Musa yaji muryan Mubinat kuma yaji wasu kalamanta wasu kuma baiji ba. Ko daya kalli motan seya hango ta tana ta faman d'aga mishi hannu bakinta arufe. Su kuwa sun kasa gane wanene Musan,dan lokacin data kirashi mutane sunkai biyar agun manya uku k'anana biyu ne,sannan basuyi tunanin yaro bane wanda Mubinat ta kira. Shiyasa sam basuyi zaton keken Musa su yake biba dan sun ganshi k'aramin yaro ne.
  Shi kuwa Musa seyama dena kallon motarsu dan karsu zarge shi, yabi ta wata hanya daba kan titi bane amma yana kallon duk inda motarsu take bi.
Ita kuwa Mubinat sun kwantar da ita yayinda wani daga cikinsu yake shafe kan k'irjinta yace "Muma bari mud'an more kafin muje Oga ya tab'aki, d'ayan yace gaskiyane fa" sannan shima ya fara shafar d'aya b'angaren k'irjin nata suna dariya suna cewa "kaji laushi kaman auduga."
Haka sukayita matse bubs d'inta harda sa hannu acikin rigarta sukayi suna matsewa.
Kuka sosai Mubinat takeyi tare da fad'in "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" acikin ranta dan bakinta a manne yake, sannan sun d'aure hannayen ta da kafafuwa ta yadda bazata iya yin komai ba sedai ta juya dama da hagu shima kuma babu hali dan sun takurata sosai. Hakan yasa taketa hawaye masu zafi tana kiran Allah a ranta. Cak kuwa taji sun d'auke hannayen su daga kan k'irjinta sakamakon isowa inda zasu tsaya.
Musa yana lab'e daga cikin ciyawi yaga sun fito da ita tana bisa kafad'an d'aya daga cikinsu sukayi ciki da ita.
  Aguje Musa ya d'auki kekensa yayi bakin titi,isarsa kenan ya samu keke nape,daga shi har kekensa suka shige ciki.

Atif ne ke dawowa motar sa cike take da tsaraba kala daban-daban wa Sis Mubinat,dan sun gama meeting d'in da wuri sosai.
Isar shi gate kenan maigadi ya bud'e k'aramin k'ofa cikin tashin hankali da tsoro yana cewa "Yallab'ai,wasu sunzo sun d'auke matar gidan sun tafi da ita"
  "What!" Ya fad'a cikin tsawa yana k'arewa maigadi kallo. Da ganinsa kasan an dakeshi ne har rigan sa ta yage.
  Yaci gaba da cewa "Wlh nayi iya k'ok'arina amma ina,sunfi karfina kayi sauri ka bisu sunkai minti sha biyar da fita babu waya a hannuna domin sun kwace alokacin dana so in sanar dakai."
"Oh my God"
"Waye su?"
"Kuma su nawa ne?"
"Sannan wace irin mota  and what is d colour gaya min!"
Cikin tashin hankali yake jero wad'an nan tambayoyin wa maigadi.
"Farar mota ce bus haka babba Yallab'ai."
A 360 Atif ya d'ibi mota batare daya san inda zaije ba. Tunani yake aransa "To waye zai min haka,babu wadda nama laifin da zaimin haka ai,koma wanene shi he will pay for it wlh."
"He will pay for it!" Ya fad'a a tsawace.
"Nasan zaku kirani tunda kuka d'auke min mata,toku kirani manaa! Me kuke mata haka tsawon 15 minits da d'au kanta amma baku kirani ba har yanzu?
"Oh Sis Mubi,Allah ya kare min ke aduk inda kike,ya Allah ina zan samu Sis Mubi nah?" Ya fad'a yana hawayen da baisan sun fito ba...

"Ya Farhan ka tsaya ga can Musa almajirin mu yana biyomu aguje da keke kuma mu yake biyowa" cewar Shureim.
Take Farhan ya tsaya suna jiran isowar sa. Tun keken nashi bata gama tsayawa ba ya yarda ita tare da k'arasowa da gudu yana haki yace "Ya farhan, Sister Mubi nagani cikin wata mota  tana cikin had'ari domin naga bakinta a d'aure tanata d'aga min hannu shine nayita bin motarsu har naga inda motar ta tsaya."
  Yaci gaba da cewa "Maza ne kusan su hud'u suke d'auke da ita se wutsil-wutsil take da k'afafun ta, lallai tana cikin had'ari Ya Farhan..."Musa ka tabbatar da abinda kake fad'a kuwa? Ka tabbata ita ka gani?"
"Eh wlh ita ce,kanta ko d'anwali babu,kuma harta kira sunana ma Ya Farhan muje inkaika gun."
Farhan ya kalli Shureim, take Shureim ya fara kuka yana cewa "Koma ba ita bace muje Ya Farhan banaso wani abu ya sami Sister Mubi dan Allah muje."
Waya Farhan ya ciro ya kira Atif,amma ba'a d'auka ba,seya tuna da cewa yau su Atif suna meeting. "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, hakan yana nufin bayan fitan Atif ne aka d'auke ta?"
Gudu sosai Farhan yakeyi tare dabin kwatan cen da  Musa yake mishi. Cikin zuciyarsa kuwa addu'oi yake tayi na nema mata kariya aduk inda take.

Koda suka iso gurin,se Farhan yace su zauna acikin mota, sannan ya kira Ahmad ya sanar dashi komai da kuma inda zasu same su sannan ya shiga cikin ginin.
  Sanye yake da suite bak'i ajikinsa da kuma bak'in eye glss a fiskarsa da wani k'aramin kwalba a hannun sa wanda bansan kona menene ba.
Shigar Farhan baiga komai ba, a hankali yake taku tare da k'arewa gurin kallo, babban gini ne sosai wanda babu rufin kwano a saman.
Shi kansa ya tsorata da yadda gurin yake da girma sosai, bai san ta inda zai fara dubata ba, dan haka seya fara kiran sunan ta
"Sis mubi!"
"Sis mubi!!"
"Sis mubi!!!"
Ita kuwa tana kwance a k'asa haihuwar uwarta babu komai a jikinta duk sun rabata da kayan dake jikinta sun d'aure mata k'afafu da hannaye  sannan an manne bakin da salatep babu halin yin magana.
Tabbas taji muryan Ya Farhan kuma ta tabbatar da cewa lallai shi d'inne.
Hakan yasa taji d'an sanyi a ranta, amma kuma data tuna da cewa  babu komai a jikinta se taci gaba da kukan data dad'e tana yin shi.
D'aya daga cikinsu yace "Muryan wani nake jifa."
Ogan nasu yayi magana "Kuje ku duba, kafin nan na more da wannan sura da yake neman haukata ni"
Cikin sauri suka fito...ido hud'u sukayi da Farhan,nan suka nufo kansa da niyan fad'a amma seya zille musu yayi saurin bin hanyar da yaga sun fito. Me zai gani, Sis Mubi ce kwance ba komai a jikinta yayin da wani saurayi yake k'ok'arin yimata fyad'e.
Cikin tafasan zuci ya jefesa da kwalban dake hannun sa a dai-dai k'eyar kansa.
Su kuwa na bayan Farhan d'in suka masa taron dangi kowa da inda yake kai masa duka, d'ayan kuwa wani ice ya d'auka ya bugawa Farhan akai, Mubinat kuwa tana ganin haka seta fara cewa "umm-umm" tana ta girgiza kai tana kuka wanda baya fita...

   Don't forget to drop your vote and comment for each page please

                              Team #KNJ

KOMAI NISAN JIFAAWhere stories live. Discover now