16

348 24 0
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

       by maman shureim
             🌺sad-nas🌺

*©Pure Momment Of Life Writers*





Page 16
    Duk da cewa sun mishi rauni a bayan kunnen sa wanda har jini yana fitowa, amma hakan baisa ya karaya ba, d'aya bayan d'aya yake fad'a dasu harya gama dasu ko kuma ince sukayi guduwan ceton rayukan su.
Shidai babban nasu yak'i guduwa suna ta fama shida Mubinat. Farhan kuwa ya dira a kansa sannan ya janyo shi har zuwa tsakiyar gurin yana tambayar sa "Waya turo ku,me tayi muku da har zaku je gidanta ku d'auketa? Ina kuka kai mata kayanta!"
Shuru yayi ya kasa amsa tambayan Farhan saboda mummunan kamu da Farhan yayi masa.
"Kayi hak'uri wlh kayanta mun riga damun k'ona su,sannan wlh babu wanda ya turo mu,bayani datayi ne ranan akan mata shine muka had'a kai akan mu sato ta domin kowan nen mu ya tab'a yaji...Farhan bai bari ya k'arasa ba,ya had'e hannayen sa guri d'aya ya murd'e su sannan yace "Ku tab'ata kuji me? Lallai zaka san ka tab'o wa kanka wahala a rayuwar ka." Wayar sa yasa a kunne "Hello Ahmad,ok ina fitowa. Yana gama wayan ya kamoshi, shi kuwa se hak'uri yake baiwa Farhan yanata magiya,amma sam Farhan bai saurare saba ya fita dashi ya damk'a shi agun su Ahmad. Tun daga gun su Ahmad suke cin Ubansa sannan suka sashi a motarsu sukayi gaba dashi bayan sunyi magana da Ahmad a sirrance, sannan Farhan d'in ya koma ciki amma da baya ya shiga, dan baya so ya sake ganin Sis Mubinat a halin da take ciki babu sutura.

"Ita kuwa Sis Mubee tana kwance babu wani abu da zata iyayi dole se'an taimaka mata."
"Farhan ya gama bin gurin da kallo amma sam babu alamun kayanta agun,sannan babu komai agun wanda zai rufe mata jikin ta dashi.
Hakan yasa ya cire wandon suite dake jikinsa da kuma shirt d'in cikin farin, yana takowa dabaya-dabaya harya iso inda take sannan ya durk'usa yakai hannun sa dai-dai saitin bakinta ya b'are salatep d'in da suka manna mata sannan yayi k'ok'ari ya kunce mata hannu d'ayan yace "Kiyi hak'uri kisa wad'an nan kayan nawa mutafi gida, saboda babu wani abu anan da zaki saka,wannan shine kawai abinda zan iya baki ."
   "Kukane mai k'arfi yazo mata,amma yanzu ba lokacin kuka bane, hakan yasa tayi k'ok'ari ta kunce d'aya hannun sannan ta kunce k'afafun tayi saurin d'aukan rigan nashi ta rufe k'irjinta,sannan tayi sauri tasa k'afarta cikin wandon nashi,inda shi kuwa yake k'ok'arin mik'ewa yabar gurin sega Atif ya shigo a gigice yana fad'i "Sis Mubee"
"Subhanalillahi,me nake gani haka?"
Da sauri ta mik'e tsaye tare da jan wandon sama sosai dan ya mata tsawo sosai sannan tasa rigan.
Da gudu Atif ya k'araso inda take ya rungume ta, ita kuwa kuka sosai takeyi gashin kanta duk k'asa gashi ta had'a zufa se kuka takeyi sosai.
"I'm sorry Sis Mubi,Meya faru? Me suka miki,ina fatan basu miki komai ba? Yi magana mana,ina kayan ki?" Duk Atif ne yake jero mata tambayoyin nan. Gefe ta hankad'a shi cikin b'acin rai take magana "Su waye wad'annan mutanen Ya Atif,me kuma alak'arka dasu,me yake faruwa a tsakanin ku,dan wlh ban yarda dakai ba kawai ka gayamin gaskiya,me yasa suke son yimin fyad'e Ya Atif ka sanar dani gaskiya!
Cikin rud'ewa Atif yake bayani "Haba Sis Mubi,me yasa kike tuhu mata haka,wlh bansan suba ban kuma san komai game dasu ba wlh...Kamin shuru Ya Atif,wlh ban yarda dakai ba,su waye suke kiranka a waya tunba yauba kake k'in d'auka,yauma kafin ka fita sun kiraka kuma baka d'auka ba,wlh bazan koma gidan kaba harse ka gayamin gaski." Tana kaiwa nan tasa kuka mai k'arfi tayi waje da gudu.
Farhan dake tsaye agun tun d'azu ya basu baya yana sauraran duk abinda sukeyi,wanda shi kanshi tunanin da yakeyi kenan.
Atif ya juyo se yaga Farhan tsaye daga shi se rigan suite da gajeren wando. Haushi ne ya sake tokararsa a zuciyar sa, kuma ya tuna da yadda yazo ya sami Mubinat ba kaya a jikinta sannan Farhan yana sunkuye a kusa da ita.
Muryan Abba sukaji yace  "Farhan?" Da sauri suka juyo a tare suna kallonshi.
Farhan zaiyi magana kenan Atif yakai mishi duka yana cewa "Dama kaine ka d'auke min mata? Awani dalili kenan, Abba kagani ko,kadai gani da idonka har yunk'urin fyad'e yake da niyan mata,duk shi ya had'a wannan shirin tunda shi kad'ai yazo nan kuma ace ya kasa kama koda mutum d'aya?"
Mubinat dake jikin Abbanta cikin kuka tace "Haba Ya Atif,me kake cewa ne,yanzu kaida kanka kake fad'in hakan akan Ya Farhan?
  Abba ne yace "Dukku dakata,wai me yake faruwa ne Farhan?"
Atif yayi saurin cewa Abba har kana tambayar sa? Babu kaya ajikin Sis Mubee nazo na sameta kuma yana kusa da ita, sannan abba kalli jikinshi dagashi se gajeren wando da rigannan fa,me kayanshi yakeyi a jikinta Abba? Wlh ban yarda da Farhan ba!
"Tasss" kakejin sauk'ar mari da Farhan ya sakewa Atif a fiskar shi.  "Ka gyara kalaman ka Atif, ka gaya min duk abinda kake so amma banda ambatona a matsayin fasik'i domin ni bazan tab'a zamowa kaiba ka gane ko?"
A fusace Atif ya nufo shi yana cewa "Yau kaine ka mareni Farhan? Lallai bakasan me kake yiba,ai take guri ya kaure da fad'an jarumai biyu. Da kyar Abba da Sis Mubee suka raba. Rungume Atif tayi tana cewa dan Allah ka bari Ya Atif kazo mu tafi, "No, sena koya mishi hankali wlh" waya ya ciro ya kira Police cikin 'yan dak'ik'ai suka iso, ran Farhan ya gama b'aci sosai.
Abba kuwa mamaki yakeyi ya kuma rasa mema zaiyi awannan lokacin,shi kuwa Atif magana yake ba sassauci yace lallai atafi da Farhan. Hannu Farhan ya mik'awa police take suka sashi a gaba.
  Kuka sosai Mubinat takeyi tana cewa "Ya Atif wlh bayi da laifin komai ka saurare ni pls."
   Bin Farhan takeyi da gudu ta durk'usa a gabansa tana cewa "Pls Ya Farhan kayi bayani,wlh Abba Ya farhan cetona yazo yi.....
Farhan yace "Hakane abinda Atif yafad'a shine dai-dai.
  Ido ta zaro tace "Me nakeji a bakinka Ya Farhan? Dan Allah ka gaya musu gaskiya wlh cetona yazoyi Abba kafi kowa sanin halin Ya Farhan bazai tab'a aikata abinda Ya Atif yake fad'a ba kuskure aka samu.
Farhan yace "Abba kayi hakuri, zuciya ce ta d'ibeni harna biyewa Atif mukayi abinda nake dana sani..."Kai karka raina min hankali fa, tunba yau ba ina ganin duk wani abu da kake yiwa Sis Mubee...Farhan bai bari Atif ya gama magana ba ya bashi amsa cikin b'acin rai da d'aga murya "Kai Atif na aikata hakan se me?!
"Ku tafi dashi nace!"
Inji Atif, take suka wuce dashi, dai-dai k'ofar fita yace "Sis Mubee key d'in mota yana aljihun wandon ki,nabar Shureim da Musa Almajiri a cikin mota karku manta dasu" yana kaiwa nan yaci gaba da tafiya.
  Durk'ushewa Mubeenat tayi a k'asa tana rusa kuka kamar ranta zai fita tana kiran "Ya Farhaaannn, Ya Atif wlh bayi da laifin komai,Abba dan Allah ka dakatar dasu baimin komaiba fa wlh shine wanda ya fara zuwa domin cetona,da bai zoba da sun lalata min rayuwa ta. Abba dubi bayan kunnen sa jini ne yake fitowa sakamakon sanda da suka buga mishi a lokacin da yake fad'a dasu, kuma babu kayana anan saboda k'onawa sukayi hakan yasa Ya Farhan cire kayan jikinsa ya bani domin babu wani abu anan dazan suturce jikina dashi, lokacin daya tsuguna ya bani kayan a lokacin ne Ya Atif ya shigo shine yayi zargin wani abu daban. Wlh bazan koma gidan kaba Ya Atif muddin aka tafi dashi! A guje ta fita waje tana kuka yayin da Atif yabi bayanta da dugu. Abba ne yayiwa Police d'in magana suka sake Ya Farhan inda Abba yaketa bashi hak'uri...k'arar taka birkin mota suka jiyo mai rikitarwa,da gudu Farhan ya wuce Abba zuwa waje. Mubinat ce ke gudu a tsakiyan titi Atif yana biye da ita, k'atuwar mota ce a gaban ta irin masu d'iban yashin nan. Dai-dai nan su Ahmad suka iso kowa "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" yake furtawa, dai-dai inda Atif yayi saurin capke tane shi kuwa Farhan ya gama rud'ewa kawai se yace "Habibty nooo" wanda yayi dai-dai da kamota da Atif yayi suka fad'a gefen titi mai motan yana ta faman zagin su.
Ganin Allah ya kare ne yasa kowa yin hamdala aka maida kallon kuma kan Farhan akan sunan da akaji ya kira Sis Mubee dashi. "Habibty?" Hakan yana nufin memory'nsa ya dawo normal kenan...?

  

                              Team #KNJ

KOMAI NISAN JIFAAWhere stories live. Discover now