5

462 46 0
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

     by maman shureim
            🌺sad-nas🌺

*©Pure Moment Of Life Writers*



Page 5
Atif ne ya dawo gida domin d'aukawa mubina indomie. Duk wani abincin dasu umma sukakai mata sam tak'ici tace aje a kawo mata indomi,hakan yasa atif ya tafi gida cikin hanzari.
Sun gama komai dan haka suka shirya kayansu da komai suka biyo ati zuwa hospital.
Kwance take ansa mata drip na ruwa,su abba harsun koma anbar iyaye mata su umma da kuma iyayen atif.
Tana kwance su atif suka shigo dasu amal. Atif ya kasa sakewa agunsu umma dan haka ya ajiye malt peak milk da su fruit daya sayo sannan ya fita. Amal ce ta zuba mata indomie tace sannu mubinat taso kici,da taimakon amal ta tashi zaune,sannan ta ajiye mata plate d'in.
"Inbanda ke mubinat yanzumafa doctor yace ulcer ce ke damunki,kuma shine zakice kese abu mai yaji?"
"Umma tunda an samu zataci ai gara abarta taci koda kad'anne inyaso se'a had'a mata maltina da peak tasha,cewar amal"
Haka kuwa akayi,taci ba laifi sannan tasha ta kwanta se bacci dama tana jin baccin sosai.

12:00 su umma suka tafi dan har wannan lokacin bacci mubinat takeyi. Amal tace zata zauna da ita,aisha kuwa tabi 'yan gidansu suka tafi.
Bayan anyi sallan azahar atif ya dawo lokacin amal tana sallah. Kusa da mubinat ya zauna akan gadon tare da tab'a jikinta yaji yayi sanyi.
Nanma k'amshin turarensane ya tasheta daga bacci. Ahankali ta bud'e ido ta kalleshi,gabad'aya shima ya rame sosai dan shima babu kwanciyan hankali atare dashi tunda aka fara zancen bikinsu. Murmushi yamata tare da rik'e hannunta,se tausayinshi ya kamata,koma komai Atif yayantane kuma duk cikin yayyunta yafiji da ita hakama kuma ita d'in,tana k'aunarshi sosai fiye da sauran yayyunta.
"Murmushin itama ta mayar mishi tare da cewa Ya atif ina Ya farhan?"
"Farhan ya wuce abuja d'azu da safe harma ya sauka lfy,ya kumace ingaisheki da jiki."
Sam bataji dad'iba,amma seta nuna kamar bakomai tace "nagode."
"Ya jikin naki,meyake miki ciwo yanzu?"
"Bakomai,k'irjinane kawai"
"Sorry,amma yakamata kidena cin yaji tunda k'irjinki na ciwo,cin yaji zai k'arasa miki ciwonne kinji?"
Gyara kwanciyarta tayi tace "to"
Hannunta ya kalla ashe ruwan ya k'are harya far jan jininta,aida sauri ya cire mata ya goge mata hannu.
"Thankyou" tace dashi
"Bana buk'atar godiya daga gareki"
Hmm Ya atif ashe dai kaima doctor ne,cewar amal.
"Eh to nima dai yaune na fara koyo akan sis mubi"
Dariya sukayi,ita kuwa sis mubi tayi d'an murmushi.
"Inaso inje inyi alwala"
"Ok muje inkaiki toilet d'in"
"Aizan iya zuwa dakaina kazauna kaci abinci."

Amal ta zuba mishi abincin dasu umma suka kawo. Atif yaci sosai sannan yasha maltina da ruwa seya jingina ajikin gadon har mubinat ta idar da sallah sannan ya bata guri ta kwanta.

Mubinat tasamu sauk'i ba laifi,ruwa leda uku tasha,Atif yaso a sallamesu amma doctor yace sedai zuwa gobe da safe dan se'an k'arasa mata drip nata da allurai.
Abba sun tafi da amal bayan isha,inda akabar Atif da matarsa kad'ai.
Nanma ba laifi taci abincin kad'an sannan tasha kunun gyad'a da umma tayi mata. Bayan ya tabbatar data k'oshine shima seyaci,yanaci friends nashi sukazo su 7.
Sun dad'e suna hira ita dai mubinat bata cewa komai se kusa 10 suka tafi.
Wayar atif ne tayi k'ara ya d'auka tare da cewa "Farhan"dad'i mubinat taji dajin sunan,dan haka ta kasa kunne dan taji mezaice. Alhamdulillah da sauk'i sosai wlh gobema za'a sallamemu insha Allah. Ok gatanan,sannan ya mik'awa mubinat.
"Hello"
"Sis mubinat"
"Ina wuni,ka isa lfy"
"Alhamdulillah ya jikin naki?"
"Dasauk'i"
"To Allah yabaki lfy"
"Ameen nagode"
"Bakomai seda safe zan sake kira"
"To" sannan ta mik'awa Atif ya karb'a suka gama magana sannan sukayi sallama.
Atif yace kiyi baccinki idan ruwan ya k'are zan kirasu kinji?
"Kanta ta d'aga alaman to" sannan ta fara bacci shikuwa se kallonta yakeyi...
Damisalin 1:7 ruwan ya k'are,dan haka ya cire mata dama seda asuba za'a sa na k'arshen. Dan haka yahau kan gadon kusa da ita ya kwanta tare da rufesu da bargo daya kawo musu yana manne da ita ajikinsa.
Atif ya gaji ga bacci dayake damunsa,dan haka yake baccinsa hankali kwance. Koda mubinat ta farka tajita manne da mutum seta tsorata,arazane ta tashi tana cewa waye kai?
Hakan yasa atif ya farka ido duk bacci yace "it's me Atif sis mubi,kwanta kiyi bacci bakomai" bamusu ta koma ta kwanta shuru,shikuwa sake kamota yayi ya manna da jikinsa suka koma bacci.
Da asuba doctor yayi nocking,Mubinat ce ta fara farkawa sannan ta tab'a Atif,kashi doctor yazo. Da salati ya farka tare da shafar kanta yace "ya jikin?"
"Da sauk'i"
"Kiyi hak'uri natakuraki ko"
"Bakomai doctor yana nocking"
"Ok bari inje in bud'e mishi k'ofan danna rufe."
Bayan ya bud'e ne Doctor yace "yamai jikin?"
"Da sauk'i sosai"inji Atif
"Ok kuyi salla senazo nasa mata ruwan daya ragen"
"Ok toh"

   Bayan sunyi sallah ne Doctor yazo yasa mata ruwan. Ta lura da cewa bacci bai isheshiba,dan haa tace "nifa zama zanyi kazo ka kwanta anan"
"Karki damu zuwa anjuma za'a sallamemu idan muka koma gida zanyi baccin"
Kallonsa kawai tayi bata sake cewa komaiba.

Sallamar su ummane ya katse mishi kallonta dayakeyi. Bayan an gaisane amal ta zubawa mubinat abinci,sannan ta zubawa Ya Atif shureim yakai mishi can waje cikin motarsa,yana ci suna hira.
k'arfe goma aka sallamesu,tare da magunguna da kuma shawarwari da Doctor yabasu. Nan sukayi sallama,mubinat wai sam sedai su koma da amal amma umma tak'i tace "kema kinsan bazaiyuba mubinat,itama ita kad'aice agidansu kin kuma san komai basena sake gayamikiba. Haka sukayi sallama suka tafi,shima Atif ya d'auketa suka tafi gidansu.
Suna isa ta wuce d'akinta agyare tas,tasan aikinsu amal ne,dan haka ta wuce toilet tayi wanka sannan ta fito ta shirya cikin wata doguwar riga pink seta kwanta.
Shima Atif wankan yayi yasa kayan ball nashi ya fesa turare sannan yazo gunta tana kwance yasameta.
"Bacci zakiyi?"
"Eh"
"To bari inzo intayi zaifi dad'i koh?"
"Silent"
"Bakice komaiba"
Daidai nan ya kunna a/c tare da jan bargon dake shinfid'e akan gado yarufesu. Shuru tayi kamar ba mutum agun,ganinshi tayi ya matso kusa da ita yana kallonta.
Mezai faru taji yana kissing na lips nata cikin wani irin yanayi,kaucar da kanta tayi zuwa gefe tace
"Nifa bana so"
Murmushi yayi yace
"To aini ina so"
"Da gaske nake fa wlh bana so"
"Tonaji,but pls kibarni for d second time"
"Silent"
Hakan yasa ya k'arayi kusan 2mint sannan ta janye jikinta tare da juya masa baya.
Ajiyar zuciya ya sauke,sanan ya matso inda take ya rungumeta ta baya tare da cewa "Ok let's sleep"
But bazaki dinga hanani lips nakiba sis mubinat,kin amince?
"Eh" na amince indai bazaka nemi wani abunba bayanshi.
  Shuru yayi kamar mai d'an nazari sannan yace "yeah,na amince tunda hakan kike so"
Dad'i taji aranta tace "thankyou"
"Anything for you sis mubinat, i will do anything just to make you happy, koda kuwa nizai zamemin damuwa.
Shuru tayi tana nazarin kalamansa,shikuwa ya matseta ajikinsa yana shak'an k'amshin dake jikinta yace "i love you."
Ahaka dai sukayi bacci basu suka tashiba se  4:10pm


Vote please
                             Team KNJ

KOMAI NISAN JIFAAWhere stories live. Discover now