38

251 19 0
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

      maman shureim
        🌺sad-nas🌺

*©Pure Momment Of Life Writers*
          We don't just entertain and educate,we also touch the hearts of the readers❤



ZANYI AMFANI DA WANNAN DAMAN IN MIK'A SAK'ON GODIYATA A GAREKU DA IRIN ADDU'OINKU A GAREMU,ALLAH YA BADA LADA YA BAR ZUMUNCI.
          ❤❤❤❤❤❤
              ONE LOVE



Page 38
"Samira inaganin Sagir ne bayi da gaskya,dan tunda nake dasu anan Atif bai tab'a fad'a da kowaba se yau wlh"
"Ina ganin ya dena shiga hidimar Mubeenat kwata-kwata dan inhar ya shiga hidimarta to wlh Atif bazai bar shiba sunyita samun sab'ani kenan,dan basa son duk wani abu dazai tab'ata wlh tunda itama ba shiga hidimarsa takeyi ba."
"Kiyi hak'uri dan Allah insha Allah zuwa gobema zamu tafi wlh."
"Haba Samira hakan yana nufin fushi kikayi kenan? Wlh kowa zaiyi shaidan su Mubeenat a unguwannan bata da rashin kunya,basa shiga hidimar kowa zaman lafiya mukeyi dasu,amma yau gashi harda fad'a?"
"Kidaiyi hak'uri tunda shi bayida aiki se neman magana gara mu koma dukda dai bamu da gurin zama amma duniya tana da fad'i ba komai."
Bayan ta fice ne ta wuce d'akin ta.
Shi kuwa Abba Amal masifa ya shiga yiwa Umman Amal ta inda yake shiga bata nan yake fita ba. Tass ya wanketa da fad'a sannan ya fita yaje gurin Sagir yana bashi hak'uri tare da cewa ya rarrashi 'yarsa karya yarda su tafi.
Jin haka yasa Sagir jin dad'i sosai tare da niyan gobe da safe zai koma gun Malam na ruga domin ya sanar dashi aiki yayi kyau sosai.

Washe gari da safe bayan anyi sallan asuba Umma da Mubeenat suka shige kichine sunata aikin abin karyawa na bak'i.
Zuwa k'arfe bakwai sun gama komai kowa ya wuce yayi wanka.
  Shirinta tayi cikin doguwar riga tas da ita babu ado a fuskarta ta nufi parlour'n Abba inda takejin muryansu suna hira.
"Slm Abba ina kwana?"
"Mamana an tashi lfy,ban gankiba da asuba"
"Eh Abba mun shiga kichine ne da Umma"
"To madallah"
"Ya Atif ina kwananku?"
"Duk suka amsa da lfy" sannan akaci gaba da gaisawa anata hira.
"Abba girman Mubeenat yaban mamaki gaskiya" cewar Farhan.
"Ai Mamana tana da gab'an girma ne sosai"
Kunya taji dan haka ta mik'e ta fice suna mata dariya. Harta fara tafiya se kuma ta dawo ta tsaya daga bakin k'ofa tace "Ya Atif wai inji Umma wai an gama abinci azo akaiwa su Ummi"
"Ok" sannan ya mik'e suka wuce tare da Mubeenat.
  Dama an shirya musu nasu akan daining d'in Umma,dan haka ya kira su Farhan suka ci abinci suna santin girkin su Umma sannan aka fito dana iyayen Farhan zuwa gun motan Abban.
  Atif ne ke driving Abba yana gaba,daga tsakiya kuma Farhan ne da Abdullahi,baya kuma Mubeenat da Shureim sannan suka tafi.

Sagir ya nunawa Malam na ruga farin cikinsa sosai inda ya k'ara masa kud'i masu yawa.
"Malam so nake ayi abun cikin sauri kar wani abu ya biyo baya."
"An gama me kuke so ayi yanzu?"
"Tabar gidan kawai ta shiga duniya a rasa gane inda take,sannan ya auri Yayata Samira"
"Hahaha! Tashi kaje an gama gobe komai zai wakana kaje ku zuba ido kawai"
"Nagode Malam seka sake ganina,dan dolene inzo godiya idan aiki ya sake yin kyau kamar yadda na farko yayi."

Su Abba suna isa aka sake gaisawa aka zauna hira kuma.
Ummi ta kalli Mubeenat tace ta taso ta dawo kusa da ita.
Haka kuwa akayi anan taci abincinta Ummi kam.
  Bayan tsarabobinsu da aka basu masu yawan gaske sukaita godiya sanna suka fito waje domin rakiya.
Farhan ne ya janyo Umminsa yana tambayar ta "Ummi kina son Mubeenat sosai fa harna fara kishi"
"Ooh Habibi aikai daban ne,haka kawai naji yarinyar ta shiga raina wlh"
Murmushi yayi "Kina nufin kina son ta?"
"Na'aam Habibi,kodai zakayi aure anan Nigeria ne?"
Cikin jin mamaki ya dubi Mahaifiyarsa "Ummi aure daga zuwanmu,kuma ni ai bansa aure a gabana yanzu ba,sannan kuma wa kike nufi Mubeenat?"
"Na'aam Habibi tun jiya muke wannan zancen da Abbinka,sedai bamu san ra'ayinka akan hakan ba,amma karka sa damuwa a ranka zab'inka shine namu karka b'oye min inhar zab'inmu bai maka ba."
"Ummi naga ai maganar bud'e company ne ya kawomu ba wannan zancen ba"
"Hakane Habibi,amma kai bakaga yadda ta girma bane,sannan yarinya ce mai hankali ga nutsuwa gata 'yar Aminin Abbinka inaga hakan zai k'ara dank'on zumunci a tsakaninsu kuma shi Abbi naka ne yazo min da zance dayaji ina yaba girmanta jiya da dare bayan dawowarmu"
Shuru Farhan yayi kamar mayin nazari sannan yace "Ummi please mubar maganan yanzu zuwa wani lokaci"
"Dama na gaya maka ai,wannan namu tunaninne amma farin cikinka ai shine namu Habibi" ta shafi fuskarsa tana murmushi.
Shima murmushin yayi tare da cewa "I will think about it Ummi"
"Take your time Habibi,karkayi gaggawa sannan kabi zab'inka ba namu ba okay?"
"Sure Ummi" sannan ya rungumeta suka nufo gun mota.
Duk abinda sukeyi akan idon Mubeenat da Shureim.
"Sis Mubee,wai shine d'an autan ta?"
"Hhhh kai Shureim,shi kad'ai ne d'ansu bayan shi babu wani,sannan kasan larabawa suna k'aunar yaransu sosai komai girmansu a matsayin yara suke d'aukansu sabar k'aunarsu da suke yi."
"Oh gaskiya abun ya burgeni sosai wlh"
"Hhhh ya isa haka shige mota"
Ba musu ya shige,zata shige kenan Abbin Farhan yace "Mubeenat bazaki zauna mana ba?"
Murmushi tayi "Uncle zan dawo anjuma da rana"
"To shikenan sekun dawo"
"Amma idan kika dawo kwana zaki mana,kinga seki koya min abincin k'asarku" cewar Ummi.
"Hhhh to Ummi bakomai" sannan ta wuce ciki suka wuce.

Tunanin maganan Umminshi kawai yakeyi a hanya har suka iso gida.
Anan suka tarar da Umman Amal da Amal sun shigo gaisawa da bak'i,nan aka sake gaisuwa sannan aka tab'a hira kowa ya kama gaban sa.
Hira sosai Umman Amal sukai da Umman Mubeenat inda take gaya mata irin abubuwan da Abban Amal yakeyi akan Samira abun ya fara damun ta.
Mamaki,sosai Umman Mubeenat tayi "To ai inaga gara ki sallamesu tun wuri,yanzu ai duniya ta lalace halin mutum se Allah."
"Wlh kuwa,Allah dai ya rufa asiri kawai."
"Ameen" sannan sukaci gaba da hira daga baya ta wuce gida tabar Amal.

Sagir kuwa ya gayawa Samira komai dan haka take zaman jira,Allah ya kaimu gobe susha kallo.
Da wuri su Umma suka gama abincin rana,inda Abba yace Mubeenat ta had'a kayanta taje gidan bayan anyi taro seta dawo.
Dama kuma su Farhan ma yaune zasu koma gidan,dan dama karane kawai sukayi suka kwana musu d'aya.
Atif ne zaune a parlour'n Umma suna magana da Mubeenat "Ya Atif dan Allah zaka dinga zuwa?"
"Insha Allah bayan na dawo amma"
"Ina kuma zaka je?"
"Zamuje yin wasa a waje,kuma jibi ne tafiyar tawa bana tunanin ina nan ma za'a bud'e company d'innan."
"Eyyah Ya Atif zanyi missing naka wlh"
"Don't worry 1week ne kawai zamuyi mu dawo,aiga wani Yaya ma kin sake samu na gaya mishi ya kulamin dake ina mugun sonki."
Murmushi tayi "But zanzo jibin muyi sallama kafin ka tafi,kuma semunje yawo ka yadda?"
"Yeah bakomai"
"Thanks Ya Atif ka kulamin da Shureim fa"
"Baki da matsala sam"
"Thanks" sannan suka fito da abincin rana.
"Ya Atif bari naje gun Amal muyi sallama dan bata san zanje ba"
"Ok" cikin sauri ta wuce dan duk suna cikin mota.

Amal zanje gidan bak'innan da suka zo mana,zand'an yi kwanaki acan kafin in dawo,but jibi ma zanzo muyi sallama da Ya Atif zai tafi wasa a waje"
"Tofa,kice zaki koyo larabci kafin ki dawo,kije ki koyo muma kizo ki koya mana"
"Kedai akwai ki da shirme,ina Umma?"
"Tana sallah"
"Wlh gashi ni suke jira idan ta fito kiyi mata sallama please"
"Ok amma tsaya,ina larabawan biyu?"
"Kai Amal dukda su zamu tafi suma can zasu koma"
"Eyye,abun zaiyi kyau zamuyi suruki kwanan nan kenan" ta k'arasa maganar cikin zolaya.
Kafad'arta Mubeenat ta daka sannan ta wuce "Nina tafi kyaji dashi ai" tana dariya.
Abdullahi da Shurim ne a gaba,yayinda Farahan ke zaune a baya,haka ta wuce ta shiga dan a motar Atif zasu tafi kuma motar one door ce.
Babu wanda yace komai in banda Atif da yake amsa wayarsa.
Farhan kuwa wayansa yake dannawa yayinda Abdullahi yake hirarsa da Shureim cikin harcen turanci.
"Sis Mubee zanyi missing naki wlh" cewar Atif
"Kana so ka sani kuka ne ko Ya Atif?"
"A'a maganar gaskiya nake miki,musamman da dare yau Shureim ne kad'ai abokin hiran nawa"
"Ai zanzo jibi da wuri muyita hira"
"To Allah ya kaimu jibin"
"Ameen" tun daga nan babu wanda yace komai har suka isa.
Bayan Atif sun gaisa dasu ne yayi musu sallama shida Shureim sannan Mubeenat ta rakosu ita da Farhan hargun mota sannan suka tafi.
Tsaye take tana bin motarsu da kallo tak'i shigewa ciki.
"Mubeenat,or let me say Sis Mubeenat right?"
Murmushi tayi tare da d'aga mishi kai alamun "Eh"
"Ok muje ciki ko?"
"To" tace sannan suka tafi ciki a tare...

                            Team #KNJ

KOMAI NISAN JIFAAWhere stories live. Discover now