52

250 15 0
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

     by maman shureim
            🌺sad-nas🌺

*©Pure Momment Of Life Writers*
        We don't only entertain and educate,but we also touch the heart of the readers❤

#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com






        Page 52
  Can b'angaren Umman Amal kuwa shekaru biyu kenan tana zaune agun Malam Buba kuma har yau babu wani labari akanta.
  Dan haka ya nuna sha'awarsa nason auranta. Ita kuwa ta amince mishi da dukkan zuciyarta saboda har a yanzu bata san ko wacece itaba sakamakon asiri da yayi tasiri akanta.
Sadakinsa ya bayar naira dubu ashirin aka nemo shaidu aka d'aura musu aure. Dama can ya tab'ayin auren yaransa uku sai Allah yayiwa Matarsa rasuwa,tun bayan rasuwarta bai sake wani aurenba sai yanzu.
*Hmmm! Wannan shine ake kira kaddara,dama can Allah ya kaddara sai Malam Buba ya auri Umman Amal,Allah kasa mu dace ameen.*

Atif bai wuce da Mubeenat gida ba,sai ya wuce dasu can gidansu.
"Ya Atif ya naga ka kawomu nan kuma?"
"Sis Mubee kince min duk lokacin da nake cikin damuwa nason tarayyar aure dake to in sanar dake zakibi ta wata hanyar ki gamsar dani,na kawomu nanne dan bazan iya yin hakan a gun su Umma ba."
Zuciyarta sai bugawa yakeyi "Amma Ya Atif ni gaskiya ina tsoro,nan fa daga ni sai kai idan kuma ka kasa hak'ura fa?"
Fuskarta ya shafa "Ki dena damuwa Sis Mubee bazan tab'a cutar dake ba,kawai dai nayi kewar kine sosai"
Jiki sanyaye suka shige ciki ta zauna a takure daga kan kujera.
Kamota yayi ya mik'ar da ita tsaye tare da runguneta yana magana cikin wata irin murya mai tab'a zuciya.
"Sis Mubee ki yarda dani wlh bazan cutar dake ba,kawai dai so nake mu kwanta a gado d'aya ina jin numfashinki a kusa dani har muyi bacci koda na awa uku ne sannan mu koma gida,kinsan nayi missing d'in bacci tare dake kinji?"
Cikin rashin yarda dashi tace "To amma su Umma zasu jimu shuru ai"
"Ok toki sanar da ita cewa munbi wani gurin amma zuwa anjuma zamu dawo"
Toh tace dashi sannan ta kira Umma ta sanar da ita.
Wayan nata ya karb'a ya ajiye a gefe tare da sake rik'ota "Shikenan zamu iya kwanciya?"
Murmushi kawai tayi mishi tare da zame jikinta daga nashi ta koma kan gadon da zauna.
Ganin ta kasa sakin jikintane yasa shi cire kayan jikin shi amma dogon wandon shi na jikinsa ya kwanta tare da cewa "Tunda naga kamar baki yadda daniba to kije kiyi kallo ko kuma ki dafa mana abinshi idan kika gama saiki tasheni,kawai so nake yau mu zauna guri d'aya" yana kaiwa nan ya juya tare da kashe wutan d'akin.
Ganin kamar da gaske baccin yakeji yasa itama mik'ewa daga gefensa bayan ta cire doguwar rigan dake jikinta ya rage daga ita sai legis black da kuma farin bra nata.
Koda ta kwanta bargo taja ta rufe jikinta,shi kuwa ko juyowa baiyiba.
Kusan 30minits babu wanda ya sake motsi acikinsu dan haka ta tabbatar da cewa yayi bacci ne,hakan yasata baccin ita ma.

2:20pm Atif ya farka daga bacci tare da juyi sai yaji mutum kusa dashi,nan ya tuna da cewa Mubeenat ce dan haka ya matso dab da ita ya rungumeta tsam a jikinshi tare da kai hannayensa kan k'irjinta.
Hakan yasa ta farka tare dayin mik'a tana salati,muryarsa taji yana magana cikin rud'ewa "I'm sorry for waking you up Mubee"
Hannunta tasa akan nashi "Pls Ya Atif ka bari,karka tayar wa kanka da hankali"
"Please let me Sis Mubee,hakan zaisa naji dad'i a raina"
Shuru tayi bata sake cewa komaiba tana jin yadda yake mata tare da tausaya mishi matuk'a.
Tsawon minti talatin kenan yake abu d'aya dan haka ta juyo ta yadda zasuna fuskantar junansu
"Lokacin sallah harya wuce,kaje kayi alwala nima nayi sai muyi sallah" tana shafar fuskar shi.
"Kije kiyi alwalan,danni kam sai nayi wanka"
Dariya tasa mishi tare da k'wace kanta ta wuce toilet. Koda ta shiga itama wankan tayi sannan ta fito d'aure da towel duk kunya ya kamata.
Tun daga k'asa yake kallonta har gashin kanta daya ganshi a jik'e. Ahankali ya k'araso inda take tsaye yana mata dariyan shima ita kuwa kanta a sunkuye dan kunyansa dataji.
Bakinsa ya kawo kusa da kunnenta yayi maganar a hankali "Dama kema ashe sai kinyi wankan shine har kike min dariya? Kinyi missing d'inane?"
Wucewa tayi da gudu ta rufe jikinta da bargo tana murmushi,sannan ya shige toilet d'in shima.
Cikin sauri ta mik'e ta bud'e hand bag nata tasa pant nata a ciki sannan ta mayar da legis d'inta jikinta tasa kaya tana zaman jiransa tare da cewa "Niba missing d'inka nayiba Ya Atif,acikin bacci nane nayi mafarkin wani abu ya faru tsakanina da Ya Farhan,kuma ko dana tashi sai naga har pant d'ina ya b'aci,wannan shine dalilin dayasa nayi wanka ba yadda kai kake tunani bane."
_Hmmmm su Sis Mubee keda kike tare da Mijinki meya kaiki mafarkin Farhan kuma? Inji sad-nas._
Bayan sunyi sallah ne tace "Nifa yunwa nake ji dan haka mu tafi gida"
"Baza ki tafi gida da yunwa ba,zomuje muci abinci sannan mu wuce gida"
Ba musu suka wuce,Atif sai farin ciki yakeji acikin ranshi,a nashi wautar gani yake Mubeenat tayi kewarsa ne sosai.

Bayan wata uku kenan da auren Malam Buba da Umman Amal, yau sai ta tashi da rashin lafiya na ciwon mara.
Mota ya nemo suka tafi asibiti,inda aka tabbatar mishi da cewa matarsa tana d'auke da ciki. Nan dai sukaita murna shida ita daga nan suka dawo gida duk wani aiki yace ta dena yinsa yaransa zasu dinga yi tunda dama can sun iya.
Su Mubeenat kuwa yaune ranar komawa gun doctor bayan wata uku kenan,dan haka suka shirya suka tafi...

Hmmm! Koya sakamakon result d'in k'arshen zai kasance oho kuci gaba da biyoni masoyana


                    Team KNJ

KOMAI NISAN JIFAAWhere stories live. Discover now