50

310 19 0
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

     by maman shureim
            🌺sad-nas🌺

*©Pure Momment Of Life Writers*
        We don't only entertain and educate,but we also touch the heart of the readers❤

#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com






    Page 50
Washe gari da sauri Mubeenat ta gama had'a musu abinci ta shirya tana jiran Abba ya fito su tafi.
"Mamana kin gama komai?"
"Eh na gama Abba"
"To fito mu tafi"
Fitowa tayi ta shige mota suka tafi.
Alokacin Farhan ya farka sunan Shureim kawai yake furtawa cikin razana.
Ya Musty da Atif suna ta mishi sannu amma kallonsu kawai yake kamar hoto,ganin hakanne yasa Atif tafiya kiran Doctor suka hau gwada shi kota ina tare da tambayar shi inane yake mishi ciwo?"
"A ina nake,sannan ku su waye? Dan Allah Shureim fa,ina Shureim yake? Ina fata babu abinda ya same shi ko?"
Mamaki ya kama Ya Musty danji Farhan yana tambayan waye su,cikin nitsuwa yayi magana "Farhan baka ganemu bane?"
"Eh suwa ku?"
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un,Doctor akwai matsala ya za'ayi yace bai ganemu ba?"
Nan Atif ya matso shima yace Farhan amma ni ka ganeni ai ko?"
Kallonsa Farhan yakeyi ya sake cewa "Atif?"
Nanne Atif yaji sanyi a ransa tare da cewa inaga ya kamata a barshi yad'an sake samun hutu tukunna.

Zuwan su Abba ne duk aka shiga tare dasu Umma dayake Shureim yanata bacci.
Nan dai suketa mishi sannu yana binsu da kallo har yazo kan Mubeenat.
Ita kuwa hawaye ya gama cika a idanunta,Atif ya kamo hannun Mubeenat yace Farhan ka gane wannan?"
Kallon Mubeenat yakeyi itama kuma haka amma sai yace "Ban santa ba,who is she?"
D'ago da fuska tayi tana kallonsa cikin mamakin jin abinda ya fad'a.
Abba yayi magana "Farhan baka gane Mamana ba?"
Atif yayi saurin cewa "Sis Mubee ce Habibty?"
Rufe idanunsa yayi yana juya kansa sannan ya bud'e "Ban gane taba wlh"
Nan Doctor suka fahimci cewa akwai matsala,dan haka akace duksu fito abarshi ya sake hutawa.
Hankalin kowa ya tashi da ganin yanayin Farhan,kowa tunaninsa shine kardai ya samu cutar mantau ne? Dan ba kowa yake ganewa ba.
Bayan awa hud'u kenan dayi mishi alluran bacci sai yanzu ya farka.
Ya Musty ya sake gani agun yana mishi "Sannu Farhan"
Nanma sake kalloshi yayi tare da cewa "Yawwa ina Shureim ne?"
"Shureim lafiyanshi lau yana bacci a d'aya d'akin"
"Baiji ciwo badai ko?"
"Eh ya samu karaya ne a hannu da k'afa"
"Farhan ka gane ni yanzu?"
"A'a waye kai ina Ummi da Abbi?"
Ya Musty yace "Suna hanya basu iso ba tukunna"
"Basu iso ba daga ina?"
Nan dai Ya Musty yasan akwai matsala sosai dan haka yaje ya kira Doctors sukazo suka sashi cikin wata na'ura ta gwada k'wak'walwa,a nanne aka gano cewa akwai wani guri da jini ya shiga acikin kansa wanda hakan shine dalilin dayasa baya iya gane kowa.
Ya Musty yace "Amma Doctor ita Mubeenat fa itace wanda zai aura a ganina tafi kowa zama sosai acikin zuciyarsa taya zai mance da ita?"
"Eh ai basonshi bane hakan,zai dawo dai-dai insha Allah aci gaba da mishi addu'a,sannan ga magunguna zamu bashi yana sha cikin ikon Allah se kuga nanda wata uku ma ya dawo yadda yake adah"
Jikin kowa yayi sanyi dajin halinda Farhan ya samu kansa aciki,wanda haka sukaita jinyarsa kwanansu biyu a asibiti Iyayensa suka iso.
Bazan iya gaya muku halin da suka shigaba da sukaga d'an nasu,Ummi da Abdullahi sai kuka sukeyi. Kuma cikin ikon Allah dukya ganesu, amma anan Nigeria ne ya gane rabi bai gane rabi ba.
Farhan ya kasa gane wacece Mubeenat a rayuwarsa dukda su Umminsa sunyi iya bakin k'ok'arinsu na fahimtar dashi amma ina,bai ganeta ba, bai gane Ya Musty ba, bai kuma gane Dad d'in su Atif ba da kuma Amal,Abba ma daga bayane ya gane shi.

Satin su d'aya aka sallamesu suka koma gida inda akaci gaba da mishi jinya.
Gidan su Ummi Mubeenat ta koma da zama itace take musu abinci koda zai gano ta da wuri, amma sam baya ma shiga harkarta kwata-kwata.
Tun abun baya damunta har ya fara damunta kullum cikin kuka take Abdullahi yayi ta bata hak'uri tare da cewa muci gaba dayi mishi addu'a Mubeenat insha Allah zai samu lafiya dan Allah karki sa komai a ranki?"
"Abdullahi dole ne in damu fa,wai ya mance ni gaba d'aya baima san wacece niba acikin rayuwarsa,sannan ina k'ok'arin fahimtar dashi amma sam bayama bani wannan damar"
Haka sukaita bata hak'uri dashi da dasu Ummi,dan su shaida ne a yadda yake k'aunar Habibty'n shi.
Kakansa kuwa cewa yayi lallai saidai su koma can k'asarsu ayita mishi jinyan acan dan bai gamsu da nan d'inba.
Babu yadda suka iya haka Abbi ya sanar dasu Abba sannan aka shirya tafi.

KOMAI NISAN JIFAANơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ