4

468 36 0
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

      by maman shureim
            🌺sad-nas🌺

*©Pure Momment Of Life Writers*




Page 4
Lips d'in nata taketa tab'awa da yatsun hannunta tare da juyawa ta kalli su aisha wanda sun dad'e dayin bacci,ahankali ta kwanta amma sam bacci yakasa d'aukanta farhan kawai take tunawa.

Da asuba bayan anfito daga masallacine farhan ya wuce gun abba bayan sun gaisa da umm ne yake sanar musu da tfyansa madina gun mahaifiyarsa. Abba yasan da zance tunda mahaifin farhan ya gaya mishi tun a dare jiya,dan haka suka mishi addu'oi tare da fatan Allah ya kaishi lfy.
"Idan ka tafi yaushe zaka dawo ya farhan?"cewar shureim. "Karka damu bazan dad'e sosai wannan karon 2month zanyi indawo"
"Har wata biyu ya farhan,toni dawa zaka barni kenan babu sis mubi kuma babu ya atif"
"Ai zan dinga kiranka a waya muna hira,kaga zan d'ebe maka kewa koh?" Ya shafi kansa tare da cewa muje ka tayani shirya kayana,bamusu ya mik'e suka fita atare yayin da iyayen mubinat suke binsu da kallo.
"Hmmm rayuwa kenan" kewar umma,yanzu abban mubinat shikenan farhan ya rabu da mubinat? "Haba hajiya meyasa kike son dawo da hannun agogo bayane,kinsan dai yanzu mubinat ta zama matar atif,kuma ai da atif da farhan duk d'ayane.
  "Hakane alhaji amma ai ita mubinat takasa gane hakan,wlh ni tausayinta nakeji acikin 'yan kwanakinnan ta dena cin abinci kar wani cutar ta kamata alhaji,kuma mubinat bazata tab'a sakewa da atif ba musamman ma idan farhan yana raye."
   "To hajiya yanzu dai abinda ya dace damuyimata shine addu'a,Allah ya daidaitasu yabasu zaman lafiya" amenn cewar umma.

8:00am ahamad yazo kai farhan airport,harda shureim akayi rakiyan dan rigima dayaketa musu.
Suna isa farhan yayi musu sallama sukuwa suka dawo gida.

Can gidan amare kuwa,bayan sunyi sallan asuba suka sake komawa bacci abinsu.
Shikuwa atif wanka yayi ya shirya cikin galila ash wanda tasha aikin yayi masa kyau sosai seya kira number'n amal. Tunda tayi sallah ta bud'e wayan yanata ringing,da sauri ta farka tare da dubawa taga atif ne. "Hello ya atif ina kwana"
"Lfy amal kun tashi lfy?"
"Lfy lau wlh"
"Em sis mubinat fa?"
"Tana bacci"
"Ok toshikenan dama zan fitane ko akwai abunda kuke buk'ata?"
"Eh zanso akawo mana indomie da kuma kayan miya na tabbata sis mubi zataci idan na girka dan tana son indomie musamman idan yaji attarugu."
"Ok badamu,akwai komai a kichine kayan miyanne dai babu bari inje inkawo muku dame dame kenan?"
"Tattasai albasa attarugu da carrot"
"Done,idan ta tashi kisanar da ita cewa nafita pls"
"Insha Allah zataji."
"Em amal nace ba,wayanta baya kusa da ita ne?"
"Yeah mun mantashi a gida cikin walldrop nata ne"
"Ok thanks"

Amal ta ajiye wayan tare da juyawa ta kalli inda sis mubinat take,baccinta kawai takeyi,hannunta takai kan mubinat aisetaji jikinta da zafi sosai.
"Subhanalillah,mubinat zazzab'i kikeji koh?" Hakan yasa mubinat da aisha farkawa suna mik'a.
"Dan Allah kubarni bacci nakeji"
"Mubinat ba bacci kikejiba zazzab'ine yake damunji kinji jikinta kuwa cewa amal."
Aisha tasa hannu a yuwanta aikuwa seta cire da sauri tace "to ai dole a sanar da ya atif"
Wayarta ta d'auka ta kirashi,kamar yana jira kuwa ya d'auka hello aisha yadai?
"Ya atif sis mubinat ce jikinta zafi kamar wuta alamun dai zazzab'ine yake son kamata"
"Subhanallah,toshikenan ina dawowa yanzu"
"To"
  Hankalinsa atashe ya gama yimusu sayayya sannan ya dawo cikin sauri.
D'akin ya nufa da sallama,suka amsa tare da mik'ewa bayan sun gaisheshine se suka fita zuwa kichine.
  Ahankali ya zauna gefen gadon kusa da ita tare da d'aura hannunsa akan wuyanta. Motsa jikinta tayi ahankali tare da bud'e idanunta saboda k'amshin turarensa dataji,ido hud'u sukayi dashi yace "sis mubi tashi muje inkaiki muga doctor"
"Uhm uhm babu abinda yake damuna bacci kawai nakeji fa"
"Yazakice haka bayan gashi jikinki yayi zafi,sannan kalli yadda kike mik'an zazzab'i pls tashi muje kinji?"
"Ya atif bazanje ko inaba zansha magani kawai anan"
"Ina aka tab'a yin haka sweetheart,kiyi hak'uri muje yanzu zamu dawo sekiyi baccinki kinji?"
"Nifa bazanjeba"
   Hulan kansa ya cire tare da d'agota ya ajiye akan cinyoyinsa kamar wata k'aramar yarinya "wlh dolene muje kiga doctor dan gaskya bakida lfy tashi muje"
Kanta ta kwantar ajikinsa tayi magana ahankali "ya atif dan Allah ka barni in kwanta wlh bacci nakeji"
Kanta ya shafa ahankali tare da mata kiss yace "kekike ganin kamar baccine sis mubi amma wlh baki da lfyne,kuma kinsan dole semunje kinga doctor ina gyalen doguwar rigan naki?
"Nifa bazanje ko inaba karabu dani"
Ajiyeta yayi ta koma ta kwanta,shikuwa ya dubo gyalen da himar nata,tunkan ya k'araso ta mik'e da sauri zuwa toilet ta dinga kwaro amai sosai wanda kusan ruwane kawai take amarwan,se kuma wani green yawu haka.
Atif ya rikice sosai ya nufi inda take sunkuye rik'e da cikinta tana juyi. "Sorry sis mubi" yafirta cikin murya mai ban tausayi yana rik'e da ita.
Shiya kurkure mata baki tare da wanke mata fiska sannan suka dawo,d'ankwalin ya d'aura mata sannan yasa mata himar fari ya d'auki hulansa ya rik'ota "muje"
"Kin tafiya tayi tana tsaye"
"Sis mubi karmu fara haka dake fa,idan kink'ifa zan d'aukeki wlh" tasan zai rina,dan haka ta fara takawa a hankali yana rik'e da ita.
"Amal"
"Na'am ya atif"
"Zankai mubina hospital semun dawo"
"To,itace mukajiyo tana amai?"
"Eh semun dawo"
"To Allah ya sauwak'a,suka furta atare"
"Ameen."

Tunda suke tfy yaketa mata magana amma batace dashi komaiba yana rik'e da hannunta yana kuma driving.
Suna isa aka mishi komai shap shap suka wuce gun doctor. Atif ne yayiwa doctor bayanin komai,inda yace kusan sati kenan batacin wani abinci.
Bayan doctor ya gama dubatane yace lallai za'a bata gado, dan za'a samata drip ga kuma allurai da za'a mata suna dewa.
Daga atif har mubinat seda sukai mamaki akan hakan,doctor ya sake cewa "when last kikayi period naki?"
Kai ta d'aga ta kalli atif,murmushi ya mata sannan ya dubi doctor yace "em babu abunda kake tunani doctor,dan jiya aka d'aura mana aure"
Hahah atif kenan,ai ciki yana iya shiga cikin dare d'ayama.
"Nasan haka doctor,amma babu abinda ya faru tukunna."
"Ok,tomuje in nuna muku d'akinku cewar doctor."

Atif ya kira abban mubinat da kuma iyayensa ya sanar dasu cewa anba mubinat gado,dukkansu seda hankalinsu ya tashi sosai. Cikin hanzari umma ta shirya tare da abincinsu suka tafi.

Da misalin 10:12am farhan ya kira ahmad yace ina abuja. Ananne ahmad yake sanar dashi cewa ankai sister mubinat hospital harma an bata gado.
"What! Mekake cewa ahmad?"
"Tana hospital,nima can zan tafi kenan yanzu haka."
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" ooh noo habibti, i'm so sorry habibti cewar farhan...

              
Vote and comment

                               Team KNJ

KOMAI NISAN JIFAAWhere stories live. Discover now