46

349 20 0
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

     by maman shureim
            🌺sad-nas🌺

*©Pure Momment Of Life Writers*
        we don't only entertain and educate,but we also touch the heart of the readers❤


Ina mai farin cikin sanar daku cewar k'ungiyarmu wato P•M•L ta samu wata gagarumar cigaba sosai sedai muyi wa Allah godiya tare da jinjinawa FATY AXLAND❤Allah yabar mana ke ameen.

#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com




  Page 46
Washe gari Umma ta zaunar da Mubeenat tana gaya mata ra'ayin Farhan a kanta. "Dan yayi wa Abbanku magana,yanzu ke dama akwai wanda kike sone kodai babu?"
Cikin jin kunya tace "Babu Umma,amma dai ina so ad'an bani koda kwana biyu ne."
"Ba damuwa kije kiyi tunani,amma ni senake ganin kamar kinyi babbar sa'a idan kika zab'i Farhan a matsayin miji dan Yaron akwai nitsuwa ga addini bayi da matsala sam gashi kuma na gida an san kowa nashi."
"To Umma nagode" sannan ta mik'e ta fice.
  Atif ne zaune a parlour Umma shida Mubeenat "Ina jinki Sis Mubee gayamun"
"Ya Atif dama Ya Farhan ne yazo min da wani batu wai yana sona kuma da aure."
Hannunta ya rik'o "Da gaske kikeyi? Indai gaskiyane to lallai na tayaki murna sis Mubeen,Farhan cikakken mutum ne wanda yasan yakamata gaskiya kinyi dace dan haka na amince dashi 100% kema kice kin amince kinji?"
Dad'i taji sosai "Da gaske kake Ya Atif?"
"Yes, i'm serious wlh ai samun miji irin Farhan abune mai wahala a rayuwarmu ta yau."
Nan Atif ya fara tunanin wata rana daya cewa Farhan suje yawo mana danshi yana da wata budurwa duk randa buk'atarsa ya tashi to gurinta yake zuwa ta biya mishi buk'ata kaima idan kana so sena nema maka d'aya. Amma sam Farhan seya nuna mishi shifa ba irin wannan samarin yake ba,tun daga lokacinne alak'arsu tad'an ja baya sosai,yafi jin dad'in alak'arsa da Ahmad dan shima baya irin wannan harkar banzan wanda a zamanin yanzu da k'yar ne mace ta samu saurayi wanda kwata-kwata a rayuwarsa bai tab'a yin zinaba gaskiya yana wahala sosai,dan acikin kashi d'ari toda k'yar ne a samu kashi d'aya yana matuk'ar wuya sedai muci gaba da Addu'a Allah ya k'ara shiryar mana da Mazajenmu,Yayyunmu da kuma k'annemmu ameen.
Bayan Atif ya gama wannan tunaninne yayi ta yabawa Mubeenat Farhan sosai,dan haka taji dad'i tare dayi masa godiya.

A islamiyya Farhan yana yiwa matan aure darasi acikin littafin *ZADUZ-ZAUZAINI* inda yake musu bayani akan ana auren mace dan abubuwa guda hud'u ne.

_Limaliha: dan dukiyarta_
_Walhasabiha: dan nasabarta_
_Wal jamaliha: dan kyanta_
_Wal diniha: dan addininta_
_Fasfar bizatitdeen: kurabauta da ma'abociyar addini._

Karatu yake musu dalla-dalla ta yadda zasu gane. Bayan ya gamane yake tambayarsu "Menene aure?"
Nan dai kowa ya fara bada amsa da cewa kafin ayi aure ana buk'atar abu hud'u

-Mata da miji
-Waliyai
-Sadaki
-Shaidu

Idan aka samu wa'innan to aure yayi Malam.
Shuru Farhan yayi kamar maiyin wani nazari sannan yace dasu "Eh to wannan ai kunmin bayanine akan d'aurin aure,amma me ake nufi da ita AURE?"
Nan kowa yake bada amsar shi da cewa Malam aure dai shine Sadaki don idan babu sadaki toba aure.
Murmushi Farhan yayi tare da cewa "Dukfa ajin nan zallan matan aure ne,amma ace babu wacce tasan ma'anar kalmar aure? Na yadda da amsoshinku,amma ba ita bace Kalmar aure ina zuwa."
Nan ya fita ya shigo ajin su Mubeenat yace "A cikinku wacece zata gaya min me kalmar aure yake nufi?"
Kowa yanata bada irin amsar da ajin matan aure suka bayar. Farhan yace sam ba haka bane, dama Amal da Mubeenat basuyi magana ba,dan haka Amal ta mik'e tsaye tace "Malam na sani"
"Kin tabbata Amal?"
"Eh"
"To shikenan kibiyoni muje,idan kika dawo seki gayawa 'yan ajin naku ma'anarsa"
"To Malam" sannan ya fice tana biye dashi a baya har suka shiga ajin matan auren.
Farhan ya kalli aji yace "To Amal,inaso ki gaya mana me ake nufi da aure?"
Kunya sosai taji,amma tasan babu kunya a wurin neman ilimi kuma na addini dan haka tayi magana ta yadda kowa zaiji.
"Aure yana nufin saduwar Mace dana Miji."
Farhan ya tambayeta "Kin tabbata?"
"Eh Malam wannan itace kalmar aure a wana fahimtar."
"Nagode Amal zaki iya komawa aji"
Bayan ta fitane ya kalli Aji "Wannan fa budurwa ce batama yi aurenba,amma ta fiku sanin menene aure,idan kuma kun sani kunyace ta hanaku fad'a inaga wannan ba hujja bace,dan babu kunya a wurin koyar addininka" nan dai yayita musu bayani har suka fahimta.

KOMAI NISAN JIFAAWhere stories live. Discover now