32

275 17 1
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸

     by maman shureim
            🌺sad-nas🌺

*©Pure Momment Of Life Writers*
         We don't just entertain and educate,we also touch the heart of the reader❤


               ❤❤❤
I DEDICATED THIS PAGE TO YOU NANA KHASLIM🌹THANKYOU SO MUCH FOR THE LOVE AND CARE,ALLAH YA BARMU TARE AMEEN.
          🌸🌹🌸🌹🌸🌹



Page 32
Koda ta shiga kuwa gurin Salma Taimoor ta wuce "Ina wuni?"
"Lafiya Mubeenat right?"
"Kai Mubeenat ta d'aga mata alamun "Eh"
Nan take Salma ta rungumeta tana rarrashinta cikin harcen turanci hartayi shuru nad'an wannan lokacin ganin Amal da mamanta sun shigone yasa ta mik'e tayi gunsu.
Nanma dai kukan sukai tayi su biyu.
"Mubeenat" muryan Ya Musty taji
"Na'am"
"Ku dena wannan kukan kunji,addu'a Umma take buk'ata agunki ba kuka ba,duk wani mamaci baya buk'atan kuka se addu'a domin kukanki azaba yake k'ara mata kinji?"
"To" tace dashi sannan suka wuce d'akinta ita a Amal sukayi alwala tare dayin sallah sunata mata addu'a.
Haka dai akaci gaba da zaman makoki harna tsawon kwana uku sannan aka watse amma banda 'yan'uwan Mubeenat.
Dama akwai k'anwar mahaifiyar tasu mai suna Rabi kuma batayi aureba,dan haka Abban Mubeenat ya nemi da abashi aurenta kodan jaririn da aka bari wato Shureim.
  Haka kuwa akayi,bayan kwana arba'in aka d'aura musu aure inda ta tare, tare da rik'e 'ya'yan yarta tamkar nata wanda ita ce dai Umma da kukeji a baya.
Zuciya d'aya ta rik'esu babu wani abu sannan suna zaman lafiya sosai kamar dai yadda suke da mahaifiyar su Mubeenat.
Ita ta rik'e Shureim tayi renonsa tun bai cika wata biyu ba.
Se'a wannan lokacinne Farhan ya damu iyayensa dasu koma can k'asarsu,amma Umminsa tak'i sam wai Nigeria ya mata dad'i dan haka sukaci gaba da zama abinsu inda ya zauna a gidansa na Nigeri.
Farhan dai k'asar ta ishesa badan sun soba haka suka tattara suka koma.

Gidan su Mubeenat da Amal babu nisa ko kad'an,hakan yasa iyayensu suka sake k'ulla k'awance dama kuma can ita Mahaifiyar Amal d'in tasan Rabin tunda k'anwar k'awarta ce marigayiya.
Haka sukaci gaba da zama wani sabon alak'ane sosai ya k'ullu musamman da 'ya'yansuma suka sake zama k'awaye Mubeenat da Amal.
Haka ake tare dukka kaman 'yan'uwa,ko gidan Uncle Muhamma Mubeenat zataje yini toda Amal suke tafiya a hakanne ma suka saba da Aisha k'anwar Atif sosai duk suka zama k'awayen juna kusan kullum a tare zaka gansu.
Makaranta ma dama Mubeenat da Aisha makaranta d'aya suke,dan haka Amal ma tace a sata agunsu Mubeenat,dayake Mahaifiyarta tana da hali shikenan aka had'asu kullum Abba shine mai kaisu ya d'auko su,wata rana kuma idan Atif yaje d'aukan Aisha seya d'aukosu ya sauk'esu a gida sannan su wuce.
Sunada k'awaye sosai acan suka had'u da Aisha Kabir haka zasuyita yawo a school kamar 'yan hud'u.
Ya Musty ya gama karatu inda yake aikin Banki,shi kuwa Ya Abdulhamid tunda ya samu aiki da wani kampani suketa canja mishi gurin aiki yanzu haka US aka turashi hakan nema yasa Mahaifinsu yace lallai sedai yayi aure kafin ya tafi.
Biki akayi gangariya ya tafi tare da matarsa can.
Ya Ra'is kuwa dama shine miskili a gidan,a fanni Arabic yake karatunsa acan Egypt,se lokaci-lokaci yake zuwa ganin gida,baya barinsu Aisha da Mubeenat su sake sam indai yana gari gashi baya shiga harkan mutane amma ya takura musu sukam.
Ana hakane auren Ya Musty ya tashi shagali sosai akayi su Mubeenat anyi ado ansha kyau amma koda Ya Ra'is ya gansu cewa yayi su koma bazasu jeba,nan take Aisha ta fara kuka ta wuce ta gayawa Mummy'n su,Atif yana jin haka yace "Ku k'yaleshi sedai ya ganku acan,ku zauna ku jirani zanje na dawo semu tafi."
Harda Amal haka Ya Atif ya dawo bayan ya kai mutane yazo ya kwashesu segun dinner.
Ab'oye suke shagalinsu wai dan kar Ya Ra'is ya gansu,ai kuwa seda ya gansu amma baice dasu komaiba agun haka aka gama shagali sune na farko da Ya Atif ya fara mayarwa gida sannan yace "Sis Mubeenat ku jirani idan na gama kai mutane zanzo sena maidaku gida kinji?"
"To bakomai seka dawo"
Ai kuwa bayan tafiyar sane sega Ya Ra'is da belt nashi lokacin Amal tana toilet nan ya shiga zubawa Aisha da Mubeenat "Wato kun rainani kenan ko,ince bazakujeba shine kukaje dan baku da kunya,na zama sa'anku ko!
  Kuka suke suna cewa "Wayyo Ya Ra'is kayi hak'uri wlh bazamu sake ba"
"Kun rainani ko,wlh daga yau bari na sake ganin kunje wani program na biki zaku gamu dani kuna k'ananan yara wai har kunsan kuje wani dinner ko baku jiba?" Ya tambayenu cikin d'aga murya
"Munji wlh bazamu sakeba kayi hak'uri"
Sannan ya dakata da dukan nasu ya kalli Mubeenat "Anan zaki kwana?"
Cikin muryan kuka tace "A'a"
"To muje in kaiki gida"
"Amal ta shiga toilet ita nake jira"
Se'a lokacin Amal ta bud'e k'ofa duk tsoro ya cikata ta fara tafiya a hankali kanta a sunkuye.
Nan Ya Ra'is ya nufota "Harda ke ko,zomin nan." 
   Duk cikinsu Amal tafisu tsoro duka dan haka ta kalli Mubeenat tana komawa da baya "Ya Ra'is dan Allah kayi hak'uri wlh banda lafiya"
"Bakida lafiya kikaje biki,kizo nan nace"
Nan Amal tasa kuka tana bashi hak'uri yayinda take kiran Mubeenat sabida tsoron bulala.
Cikin k'arfin hali Mubeenat ta mik'e zuwa gaban Amal ta tareta tana bawa Ya Ra'is hak'uri.
"Dan Allah kayi hak'uri wlh bata da laifi ninace tazo muje kuma da gaskene bata da lafiya wlh"
"Zaki karb'a mata dukan kenan?"
Kanta take girgizawa "A'a Ya Ra'is dan Allah kayi hak'uri mun tuba wlh bazamu sakeba Allah"
"Tausayin Mubeenat yaji dan haka ya juya ya fice tare da cewa "Ku fito in kaiku gida"
Hawaye suka share tare da d'aukan jakansu suka wuce Aisha tana cewa "Mubeenat Amal dan Allah kuyi hak'uri kunji?"
"Bakomai Aisha semunzo gobe" cewar Mubeenat sannan suka wuce gun motar.
Shida abokinsa ne a cikin motan,har zasu shiga seka Ya Atif daga nesa ya hango su.
"Sister Mubeenat,zaku tafi ne?"
"Eh seda safe"
"Wazai kaiku gida?"
"Ya Ra'is ne"
"Ok to shikenan gobe zanzo in d'aukeku a gida kigaida Umma"
"Zataji" sannan suka wuce baya ita da Amal.
Atif yana shiga Aisha ta fashe da kuka tare da rungume shi.
"Aisha meya sameki?"
"Ya Ra'is ne ya zanemu nida Mubeenat wai dan munje gurin dinner,tana ta kuka yanzu suka tafi"
"Ya zane ku?"
"Eh da belt nashi"
Ran Atif in yayi dubu seda ya b'aci nan ya saki Aisha yaje gun Daddy'n su "Daddy kayiwa Ra'is magana wlh karya sake dukan Aisha da Sister Mubeenat,wai kawai dan yace bazasuje gurin dinner ba ni kuma na d'aukesu muka tafi shine wai ya zanesu yanzu harda Mubeenat marainiya cefa ita Daddy kuma ai naga bikin Yayansu ne."
"Zanesu yayi?" Daddy ya tambaya
"Eh da belt,wlh Daddy kayi mishi magana Allah bazan sake bari ya dakesu ba tunda ba wani laifin azo a gani sukayi mishi ba."
"Shikenan zan sameshi ina Mubeenat d'in?"
"Ta koma gida"
"Badamuwa kayi hak'uri"
Sannan Atif ya fita rai a b'ace Daddy yana binsa da kallo.
Tun Mubeenat tana k'arama Atif yake ji da ita dan itace kad'ai k'anwarsu mace har goyonta yanayi Ummanta marigayiya tayita dariya shikuwa ko'a jikinsa renonta yake sosai tun bata san kanta ba shiyasa baya son duk wani abu dazai tab'ata.

"Sister Mubeenat bazaku gaida abokina bane?" Cewar Ya Ra'is.
A tare suka had'a baki "Ina wuni?"
"Lafiya ya kuke?"
"Lafiya" sannan duk sukayi shuru inda su kuwa suketa hira har suka isa k'ofar gidan su.
  Dukkansu suka fito daga motar inda Ra'is ya kalli Mubeenat "Kema anan zaki sauka?"
"Eh zan rakata cikin gidansu sannan in wuce"
Fitowa yayi daga cikin motar yace "Muje"
Ba musu sukayi gaba yana binsu a baya har suka kai Amal bakin gate nasu sannan suka juyo.
"Sister Mubeenat?" ya kira sunanta
"Na'am"
"Kiyi hak'uri kinji,kuma karki gayawa Abba ko Umma cewar na dakeki pls"
"To" tace dashi suna takowa har bakin gate sannan ya sake cewa "Kin ji?"
"Eh bazan fad'a musu ba"
"Ok zakizo yini gobe ne?"
"Eh zanzo"
"Da yaushe zaki zo sena zo na d'aukeki?"
"Ya Atif yace zaizo ya d'aukemu tare da Umma zamu zo"
"Alright please kiyi hak'uri and idan nayi miki magana ki dinga ji kinji?"
Kai ta d'aga mishi alamun taji batare datayi magana ba.
"Sister Mubeenat are you angry at me?"
"No" ta bashi amsa a hankali
"Are you sure?"
Kallon shi tayi tana murmushi "Yes"
Shima murmushin yayi tare da knocking gate d'in sega maigadi yazo ya bud'e inda Mubeenat ta shige ta barsu suna gaisawa.
D'akin Umma ta wuce kai tsaye,kuma bata gaya mata cewa an dakesu ba.
Bayan ta gamayiwa Shureim wasane sannan ta wuce d'akinta ta watsa ruwa seta kwanta tana tuna yadda sukayi da Ya Ra'is.
"Yau wai Ya Ra'is ne yamin wad'annan maganganun,shida ko gaishesa kayi kamar bazai amsaba dan miskilanci shine har yana bani hak'uri tare da tambayar koyazo gobe ya d'aukeni?"
"Koda yake shima yasan bai kyauta bane ai sabida ba wani laifi mukayi mishi ba dazai dakemu"
"Allah ya kaimu gobe inbawa Aisha labari nasan zatayi mamaki k'ilama ta k'aryata ni..."

 
                             
                          Team #KNJ

KOMAI NISAN JIFAAWhere stories live. Discover now