34

272 20 2
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

     by maman Shureim
            🌺sad-nas🌺

*©Pure Momment Of Life Writers*
         We don't just entertain and educate,we also touch the hearts of the readers❤



here is a page for you Ayusher Moh'd Allah yabar zumunci ya yara mana yaranmu ameen.
             WITH LOVE
            ❤❤❤




Page 34
   A haka dai rayuwar su Mubeenat taci gaba da tafiya cikin jin dad'i da kwanciyan hankali babu wani mai takura musu se Ya Ra'is.
Shima kuma se idan sunyi hutu ne ya dawo Nigeria,amma idan ya koma cin karensu suke ba babbaka inda Atif ya d'aure musu gindi tunda basa wani abu daya kauce hanya.
Shak'uwar su da Atif se gaba-gaba yakeyi domin shi Atif Mutum ne mai son jama'a musamman su k'annen nasa yana kulawa dasu sam baya son abinda zai tab'asu,koda a school ne aka tab'asu tofa seyabi diddigi ya had'a abota da malamin nasu ta yadda baza'a sake tab'asu ba.
Kuma dama shima mai jama'a ne domin shi tun tashinsa k'wallon kafa ne kawai abinda yake bashi sha'awa,hakan yasa ya matsawa Daddyn'shi lallai seya mishi hanya domin ya zama mai bugawa k'asarmu Nigeria k'wallo,haka kuwa akayi dayake ya iya k'wallon sosai akayi nasarar d'aukansa kud'i sosai yake samu musamman idan shi yaci k'wallo kuma duk k'asar da za'aje tofa idan k'wallo ta shiga hannun Atif Muhammad Bakari to tabbas seyaci wannan wasan.
Hakan yasa k'ungiyar 'yan k'wallon takeji da Atif sosai,ko d'an gurd'ewa yayi zakaga shuwagabannin sunyi cah akansa ana mishi treatment yadda ya kamata ganin hakan yasa Atif k'ara shagwab'ewa dama Mummynsu ta shagwab'a shi kamar shine auta.

Su Mubeenat kuwa sunata karatunsu sosai,shi kuwa Shureim se girma yakeyi ya biyo Mubeenat dan tana da gab'an girma.
Mubeenat kyakkyawace sedai bata layin farare amma kuma baza'a kirata bak'a ba,tana da tsawo kad'an sannan jikinta dai-dai yake bamai muniba dan tafi Aisha jiki gata da gashi masha Allah dangin Mahaifinta ta d'auko,tana da kunya sosai musamman ga wad'anda bata sansuba hakama maganarta se ga wanda ta sani takeyi.

Aisha kuwa fara ce tas,dan tana d'an kama da Atif dukda dai ya fita kyau sosai,sannan Aisha tana da tsawo sosai gata da son saka takalma masu tsinin gaske bugu da k'ari akwai son kwalliya wanda kuwa ita ba gwana bace tagun sedai taje gun Mubeenat tayi mata,dake ita Mubeenta ta k'ware sosai gurin tsala kwalliya dan har Amare tana yiwa kwalliya amma wanda suke zumunci kuma sam bana kud'i take yiba haka dai take dason ado.
Aisha tana son yayyunta sosai musamman Ya Abdulhamid bayan tafiyarsa US ne soyayyar ya dawo kan Ya Atif inda ayanzu zance tafi kowa son Atif tana ji dashi sosai musammanma da taga mata had'ad'd'u suna mata hidima sosai akan Atif,waisu a dole son shi sukeyi.
Goma na arziki sukeyiwa Aisha dukdan su samu shiga agun Atif,amma ina sam baya kulasu bayima da lokacin su.
Ganin hakanne yasa wasu daga cikinsu suka fara mishi tallan kansu duk dan su samu shiga,tun Atif yanak'i har shaid'anun mata sukai nasara akan shi,dama kuma cikin friends nashi akwai 'yan iska sosai acikinsu nan suka shiga zugashi "Haba dude,kai daka samu ana zuwa maka a kyauta mufa semun biya kafin a bamu,kawai ka d'an gwada koda da guda d'aya ce.
Yau da gobe se Allah,ranan dai Atif ya amince wa wata yarinya mai suna Rashida ta had'u ba k'arya sannan budurwa ce sonda take yiwa Atif ya wuce misali hakan yasa taji zata iya bashi kanta indai zai sota ya aureta tofa burinta ya cika.
Subhanalillah Allah ka rabamu da son zuciya,ka rabamu da mugayen abokai wanda zasu kaimu ga aikata haramun,ka tsarkake mana zuciyoyimmu ka dauwamar dashi akan imani da tsoronka ameen.
Tunda Atif yayi tarayya da Rashida seyaji bazai iya rabuwa da ita ba haka ya ajiyeta a matsayin matarsa duk lokacin da yake da buk'ata waya kawai zai mata su had'u.
Alhali dah shi Atif mutumin kirkine ba ruwansa da irin wannan abubuwan amma yin abokai da mutanen banza yasa shima ya zama irinsu.

Ya Ra'is ya gama karatunsa inda ya samu aiki acan Egypt d'in ta fannin Arabic,shima 'yar can ya samu ya aura inda suke zamansu acan.
Akwana a tashi babu wuya su Mubeenat suna da shekaru goma sha tara ita da Amal,Aisha kuma sha takwas.
Ra'is da farhan kuwa suna da 32 years kenan shi kuwa Atif yana da 29
Su Mubeenat suna ajin k'arshe kenan a secondary. A wannan lokacinne aka gama aikin Company nasu Farhan da akeyi harma da babban Shopping mole wanda yaci suna *TAIMOOR STORE*.
Tun kafin suzo Nigeria Abban Mubeenat yayiwa mutane sama da d'ari hanyan aiki a company da kuma Store d'in.
Shi kanshi Abban Mubeenat ba k'aramin kud'ad'e ya samuba waje gina wannan gurare biyun,dan komai ta hannunshi Abbi d'in Farhan ya turo inda yake cewa "Gaskiya nidai ashe aure jari nayi abokina,irin wannan dukiya na Family d'in matana ai dolene kaima kaci rabonka indai aminantakarmu ta gaskiya ce"
Dad'i sosai Abban Mubeenat yaji dukda dai suma Alhamdulillah suna dashi dai-dai gwargwado kuma suna taimakawa marasa k'arfi shiyasa ma Allah yake dad'a bunk'asa musu.
A cikin wannan watan ake sa ran zuwan su Abbin Farhan tare da wasu daga cikin Family nasu domin bud'e wannan Company d'in.
Dama Abban Mubeenat ya gama komai tare da taimakon Yayansa da kuma babban d'ansa wato Ya Musty,anyi gayyatar manyan bak'i harda Governor na Gombe wato Talba,da duk wani babba an gayyata an kuma sanar ta gidan TV da Radio.
"Mamana"
"N'am Abba gani"
"To Mamana albishirin ki?"
"Goro fara tass Abba"
"Yau Yayanki zai dawo gidan nan da zama"
Farin ciki ne fal akan fuskarta tace "Waye kenan Abba?"
"Yace karna gaya miki,idan yazo zaki ganshi"
"To Allah ya kawo shi lfy,inama da Ya Atif ne dana had'a babban liyafa a gidan nan yau"
"To ai gara kije ki fara had'a liyafar" cewar Umma.
"Da gaske Umma,kina nufin Ya Atif ne?"
"To koma bashi bane tunda ance zai dawo nan da zama ai abin farin cikine agunki tunda kin dad'e kina son Yaya"
"Sosaima Umma,bari naje na had'a mishi abinci to"
Sannan ta fice tana ta murna inda su Abba suke binta da dariya.

"Ni wlh ban yarda ba Ya Atif" ta fad'a fuska had'e tana zunb'ura baki"
"Oh sweet Sis,hakan ba yana nufin na barki bane ai,kuma kinji kema gidan Ya Musty zakije zama da matarshi kafin ta haihu,kinga nima kafinnan aina dawo ko?"
"Ka tabbata?"
"Yes" ya fad'a tare da bata hannunshi suka tafa ya rungumeta kamar wata k'aramar yarinya.
Nan ta sake tana dariya tare suka wuce har d'akin shi tana tayashi shirya kayansa.

Mubeenat kuwa  had'ad'd'iyar jolof tayi wanda yaji abubuwa kala-kala se k'amshine kawai yake tashi,ga peppe soup na kaza da fruit salat. Tana gamawa tace da Shureim "Jeka kayi wanka k'anina"
"To Sis Mubee" sannan ya wuce.
Shureim tun bai gama iya maganaba yake k'ok'arin kiran sunan Mubeenat kamar yadda yaji ana cewa Sis Mubeenat,shi kuwa bazai iya had'awa duka ba se yace Sis Mubee.
Tun daga wannan lokacin su Amal da Aisha suka shiga kiranta da Sis Mubee,harma da Ya Atif d'in.
To shinefa har girman Shureim wanda a yanzu yana da 6years kenan kuma a hakan yaci da kiranta Sis Mubee...

Vote & comment

                           Team #KNJ

KOMAI NISAN JIFAAWaar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu