25

325 21 0
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

      by maman shureim
             🌺sad-nas🌺

*©Pure Momment Of Life Writers*
         We don't just entertain and educate,we also touch the hearts of the reders💐






Page 25
Bayan an gama had'uwane aka bud'e taro da addu'a sannan Farhan yayita jawabi sosai.
Abba ne ya karb'eshi shima yayi nashi jawabin a matsayinshi na Aminin Mahaifin Farhan.
Kusan mutane da dama akayita gabatar da taro yadda ya kamata tare da raba kyaututtuka masu yawan gaske,koda aka kira Mubee ita da Atif sukaje suka k'arba.
Hakama Amal Ahmad ne ya rakata ta karb'i nata kyautan,haka dai akayita bayarwa har aka gama sannan kowa ya nufi gurin cin abinci.
Seda su Abba tare da manyan bak'i suka gama sannan su Farhan hakadai akeyi bi da bi.
Wayan Farhanne yaketa ringing mutanen madina sun dameshi da kira hakan yasa ya d'auka dan yanzu a nitse yake yana cin abinci.
Abdullahi yayansane ya kira vedio call dan yaga gurin taro inda suke ta jin haushi babu su a wannan taro.
Hira sosai suke tayi inda Umminsa ta nemi ganin Mubee,Farhan bazai iya musu da itaba dan haka ya mik'awa Atif yace "Ummi ce take so su gaisa da Sis Mubee."
Atif ya karb'a suka gaisa,sannan yaje har inda su Mubee suke zaune ya mik'a mata. Fuskar Ummin Farhan ta gani inda farinciki ya baiyana akan fuskarta k'arara,shi kuwa Atif yana bata yabar gun.
Farhan yana zaune daga nesa amma hankalinsa gaba d'aya agunsu yake,se kalon fuskar Mubee yakeyi.
Hira sosai sukayi da Ummi cikin harshen turanshi sannan suka sake gaisawa da Abdullahi tace "Bari na kaiwa Ya Farhan d'in" sannan ta wuce gurinda suke zaune.
Yayin da Abdullahi yaketa sata dariya har ta isa gurinsu dariya takeyi. Cikin sauri Abdullahi ya sake cewa "Please answer my questoin Mubeenat"
Cikin dariya tace "No i don't"
"Ok thanks byee"
"Byee" sannan ta mik'awa Ya Farhan. Ahmad yace "Nidai yau Sis Mubee bata gaisheniba"
Murmushi tayi "Sorry hidimace tasa na mance dakai,ina kwana?"
"Gaskya naga alama yau kina cikin farin ciki"
"Gaskya kam" sannan ta wuce ta koma gurin zamanta"
Wani daga cikinsune yake tambayar Atif "Wai kai har yanzu bamu samu k'aruwa bane,naga kamar babu alaman ciki a tattare da matarka kana sanya ko?"
Dariya sukasa dukkansu sannan yace "Tukunna dai,Kasan komai se lokaci yayi"
"Hakane,to Allah ya kawo masu albarka"
"Ameen" dukkansu suka amsa harda Farhan...

Kowa yaci ya sha ya k'oshi sannan aka shiga d'aukan hoto. Hmm abun ba'a magana hotuna sosai akeyi a wannan taro 'yan'uwane,abokaine,dangine,masoyane,k'awayene,mata da mijine dukdai anata fama.
Sunyi ta hotuna inda Atif ma yayi sosai da Mubee da shureim. Mubee da Farhanne kawai basuyi hoto su biyu ba,amma yayi sosai dasu Amal da Aisha da sauran 'yan company'nsu.
  Tana zaune daga gefe ita da wannan arniyan mai suna Ruth suna hira,amma hankalinta duk yana gunsu Amal da suketa hotuna dasu Farhan.
Shureim ta kira ta bashi wayanta "Kaje ka d'aukamin Ya Farhan batare daya saniba"
"To" Shureim yace sannan ya wuce da gudu.
Ai kuwa suna kallon Shureim ya b'uya daga bayan wani,lokacin Farhan yana kallon inda su Mubee suke yana dariya kyat Shureim ya d'aukesa sannan ya dawo da gudu.
"Na d'auka Sis Mubee kuma yayi kyau kalli"
Murmushi tayi tare da cewa "Nagode Shureim,hoton yayi kyau sosai kuwa"
"To nidai na tafi"
"Ok" tace dashi sannan ya ruga a guje ya koma inda Farhan yake.
Atif ne yazo inda suke shida wani abokinsa suka gaisa sannan yace wa Sis Mubee "Zamuje can gefe mu zauna idan kina nemana"
"Ok" tace dashi tana kallonshi. Peck ya bata a goshinta sannan suka wuce duk akan idon Farhan.
Mubee tace da Ruth "Kona second d'aya bana son Ya Atif a matsayin mijina,kawai ina yin biyayyar aurene amma wlh har abada zuciyata Ya Farhan kad'ai take so."
Tausayin Mubee ya kama Ruth sosai,ta shafi kafad'arta tace "Sorry Mubinat"
K'walla Mubee ta share tace "Thankyou" yayinda wani k'wallan yake shirin fitowa tayi saurin sa hannayenta ta goge.
Hankalin Farhan ya tashi sosai da ganin hakan dukda dai baya iya jin abinda suke cewa amma yana ganin komai. Ahmad ne ya katseshi da cewa "Muna zuwa" sannan yace da Amal muje.
Wucewa sukayi har inda Mubee suke tace "Mubee ina dawowa yanzu"
"Ok sekun dawo" ta kalli Ahmad tana dariya.
"Dariyan me kikeyi Sis Mubee?" Cewar Ahmad
"Bakomai kuje abinku nida Ruth nake dariya bada kuba"
Dariya sukayi suma sannan suka wuce.
Ruth ta kalli Mubee tace "Shine zai aureta ko?"
"Ehh" ta bata amsa.
Aisha ce tazo da sauri ta kamo hannun Mubee "Zomuje ku gaisa da wasu"
Mubee bata ce komaiba tabi bayanta yayinda Aisha take jan hannunta hargun wasu maza.
"To gatanan,itace matar Ya Atif"
Nandai suka gaisa sosai sannan ta juya zata koma se taji Shureim ya rik'o hannunta tare da cewa "Sis Mubee kizo muje gun Ya Farhan muyi hira tunda idan kuka barnan gidanku zaku wuce."
Mubee bazata iya k'in zuwaba,dan haka ta bishi suka tafi.
Koda suka isa gurinshin shi kuma ya mik'e dan wani dayazo suyi hoto. Bayan sunyi hotonne watama ta sake zuwa sukayi sannan yazo har inda take tsaye yana murmushi "Sis Mubee?"
Murmushi itama tayi tace "Ya Farhan ya hidima?"
"Alhamdulillah" ya bata amsa
Shureim yace "Ya Farhan ku tsaya na muku hoto naga bakuyiba ku biyun"
Farhan ya kalli Shureim tare da shafan kansa "Waya gaya maka cewa bamuyiba?"
"Nidai banga lokacin da kukayiba"
"To ai ba lallai seka ganiba lokacin kana cin abinci ne"
"Ohh todai nima ina so in d'aukeku ne kawai"
Farhan ya kalli Mubee itama shi take kallo,Shureim yayi gudu zaije ya d'auko ipad su kuwa suna tsaye sun rasa abin fad'a sega Amal tazo a hargitse ta rik'o kafad'ar Mubee tare da juyo da ita tana magana tare da sauke numfashi.
"Mubee?"
Ita kuwa Mubee ta tsorata da ganin yanayin da Amala tazo mata dashi "Na'am lafiya?" Ta tambayi Amal
"Mubee did you sleeped with Ya Atif?"
Kunyar tambayar sosai Mubee taji musamman ma da tasan Farhan yana tsaye agun,juyowa tayi ta kalli Farhan dake tsaye a bayanta sannan ta kalli Amal tace
"What a stupid question Amal,are you out of your mind?"
"Please answer my question Mubee" ta fad'a kamar zatayi kuka,ganin hakan yasa Mubinat cewa
"Yes I did"
"You what?" Ta sake tambaya tana zare ido
"I say I did Amal,why are you asking me this stupid question here?"
"Sorry Mubee,when,please tell me when?"
"You're not serious Amal,will you stop this nonsense!" Ta fad'a a tsawace.
"I'm sorry Mubee,but you need to answer me please when?"
"Yesterday night!"
"Oh my gosh" ta fad'a sannan ta rungume Mubee tana kuka.
Daga Mubee bar Farhan sun tsure sosai,nan Farhan ya shiga tuna wayan da sukayi d'azu shida Atif inda yake sanar dashi Mubee ce bataji dad'iba shiyasa suka makara.
Kukan da Amal takeyi ya dami Mubee sosai,dan haka ta sake tambayar Amal
"Amal please tell me what is going on,why are you craying?"
Kanta ta d'ago tana kallon Mubee cikin tausayawa tayi k'asa da muryan tace "Mubee,Ya Atif is H I V positive" sannan ta sake fashewa da kuka.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" Farhan da Mubee suka furta a tare.
"Amal ki dena wannan shirmen,kinsan me kike fad'a kuwa?" Cewar Farhan
"Wlh Ya Farhan abinda na gaya muku gaskiyane,zaka iya tambayan Ahmad shima shaidane,Ya Atif da bakinshi mukaji yana fad'a yanzu haka sun tafi gurin doctor ne domin ya sanar dashi halin da Mubee take ciki."
Mubee ta gama rud'ewa,dan haka ta yanki jiki zata fad'i Farhan da Amal sukayi saurin tareta ta fad'a hannayen Farhan dayake dama ata bayanta yake tsaye...😔


                           Team #KNJ

KOMAI NISAN JIFAAWhere stories live. Discover now