23

313 22 0
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

     by maman shureim
            🌺sad-nas🌺

*©Pure Momment Of Life Writers*
         We don't just entertain and educate,we also touch the hearts of of the readers💐







Page 23
Zaune suke agaban Abba suna sauraran nasihar da yake musu mai shiga jiki,musamman ma Mubinat dayake duk rabin nasihar ita yayiwa.
"Ki sani Miji ya wuce wasa Mamana,abu kad'an zaki mishi ya kaiki wuta dan haka ki gyara duk wasu kuskuren da kikeyi a baya sannan ki bawa Mijinki dukkanin kula da biyayya na aure,karki yadda ki bari Mijinki ya kwana cikin b'acin rai dan hakan ba k'aramin musifabace akan duk wata matar aure."
"Kai kuma Atif kaji tsoron Allah,idan Mamana tayi ba daidaiba kazo ka sanar dani ko kuma ka sanar da Yayyunta duk d'ayane,ku tashi kuje Allah yayi muku albarka."
"Ameeen"suka amsa tare dayin godiya sannan suka tafi.

Acan Company kuwa kowa se murna yakeyi akan nasarar da sukayi,daga company'n Farhan dasu Ahmad suka dawo zuwa *Taimoor Store*.Namma murna sosai aketayi yayinda nan d'inma Farhan yayi jawabi sosai tare da godiya ga dukkan ma'aikatan gurin da irin k'ok'arinsu.
Mutane se tambayan Amal sukeyi "Where is Sis Mubee?"
Ita kanta Amal tayi farin cikin zuwa nan d'in,dan tun lokacin da aka fara maganan bikin Mubeenat da Ya Atif tabar zuwa domin ta zauna rarrashinta. Hakan yasa Amal ta rasa me zata gaya musu,tasan cewa dole Mubeenat zata zo taron gobe,dan haka tace dasu "You will all see her tomorow insha Allah" nan sukaita murna yayinda hankalin Farhan duk yake gurin su.
Wata daga cikinsu ba musulma bace suna shiri sosai da Mubeenat. Tace da Amal "When are they getting married with Sir Farhan?"
Nanne jikin Amal yayi sanyi ta kuma rasa me zata ce dasu,murmushi tayi sannan tace "She's already married to Atif."
Gabad'aya jikinsu yayi sanyi dajin abinda Amal ta gaya musu. "What of Sir Farhan?" Suka tambayeta
Sunkuyar da kai Amal tayi dan bata so suci gaba da tambayarta. Farhan ne yayi saurin cewa "All of you should come here" hakan yasa Amal taji dad'i duk suka tafi,inda ya k'irk'iro bayanai kuma masu amfani sukaita tattaunawa akai babu wanda ya samu daman sake tambayar Amal wani abu.
Shi kuwa Farhan office ya koma ya zauna yana tuna wani rana da yayi bak'uwa a office nashi suna magana sun jima sosai,inda Mubeenat ta fara zargin wannan bak'uwar dayayi,hakan yasa ta bar office nata ta shigo office d'in Farhan d'in kai tsaye tace "Escuse me" tana kallon Farhan tare da d'an had'a rai.
"Yes come in" ya fad'a yana murmushi.
Kusa da kujerarsa tazo tare dad'an sunkuyowa ta kunnensa tace "Sir can I get you a coffee?" Tana k'arewa bak'uwar kallo kyakkyawace sosai gashi tasha ado.
"Yes of cause,and you?" ya tambayi bak'uwar
Wani irin takaicine ya tokari Mubee a k'irjinta,lallai ma Habibi zaka had'u dani yau ta fad'a a zuciyarta, yayinda ita Yarinyar tace "No thankyou"
Bata jira jin abinda Farhan zai sake cewa ba ta wuce tana murgud'a baki,bayan ta isa dai-dai k'ofar fitane ta juyo suka had'a ido,gwalo yayi mata ita kuwa rai b'ace ta fice babu jimawa ta dawo rik'e da cup na coffee a hannun ta.
A hankali ta ajiye a gabansa tare da cewa "Here it is Sir" tana murmushi.
"Shukran laki" ya furta yana dubanta sannan ta fice. Gun Amal ta wuce kai tsaye tanata zirga-zirga,Amal kuwa se dariya take mata.
Bayan bak'uwar tasa ta tafine seya kira wayan Mubee amma sam tak'i d'auka wai ita a dole tayi fushi,wayan Amal ya kira yace "Amal pls ki sanar da Habibty cewa tazo office"
"Ok,sannan ta kalli Mubee wai kije inji Habibinki"
"Bazani ba" ta fad'a tana zaune akan kujera
Farhan yana jin me take cewa dan bai katse wayar ba. "Bakomai Amal naji abinda tace ina zuwa"
Bayan Amal ta ajiye wayanne ta kalli Mubee tace "Kishi kumallon mata" duka Mubee takai mata a baya tace "Ai k'ilama gara ni akanki"
"SLM" Farhan ya fad'a,wslm suka masa amma ita Mubee tak'i kallon inda yake.
Ganin hakan yasa Amal barin gurin ta fice. Inda Amal ta tashi anan Farhan ya zauna kusa da ita "Habibty what's going on?"
"I don't know" ta bashi amsa tare da mik'ewa.
Shima mik'ewan yayi "where are you going?"
"Home"
"But why now?"
Kallonsa tayi har cikin ido "Are you asking me Habibi?"
Hancinci ya shafa tare da kallon sauran ma'aikatansu sannan ya kalleta yace "OK let me take you" sannan ya fice zuwa office nashi ya d'auka key'n mota ya dawo gunta "Let's go"
Yana gaba tana biye dashi a baya har suka k'arasa gun motan. Shi da kansa ya bud'e mata tana tsaye ko kallon inda yake batayi.
A hankali yake driving yana kallonta amma sam tak'i kallonsa,seda ya samu wani gefe da babu mutane sosai sannan ya tsaya.
Juyowa yayi yana fuskantarta yayinda ita kuwa take kallon gefen glass nata.
"Habibty" ya kirata cikin daddad'ar muryarsa,ahankali ta juyo suna kallon juna.
Lips nashi ya lasa sannan yace "What's going on?"
"Are you still asking me Habibi?" Ta fad'a cikin fushi
Lips nashi ya sake lasa "Habibty how many times do you wan me to tell you this? There is nothing between me and all the women's that you will see,is all about business Habibty please put that in you're mine i have nothing to do with all of them you are the one that my heart tell me to love,only you Habibty."
"I'm sorry idan na miki laifi,but please stop acting like that because you are hurting me Habibty,koda wasa bana son ganinki cikin fushi bare har ranki ya b'aci please stop it Habibty?"
Dad'i taji har cikin ranta da wad'annan kalaman nashi,hakan yasa tayi fuska tace "I don't believe you Habibi,me yasa zaka tambayeta ko'a kawo mata coffee?"
Iska ya huro daga bakinsa "Huuh,Habibty she's our visitor right?"
Shuru tayi kamar meyin wani nazari sannan tace "OK tell me,what are you discosing with her more than an our?"
"Hmm,Habibty har yanzu baki yarda daniba kenan?" Ya fad'a yana kallon fuskarta.
A hankali ta kalleshi cikin shagwab'a tace "Ba haka babe Habibi,na yarda dakai wlh amma su 'yan matanne ban yarda dasu ba."
"Murmushi yayi mata tare da rik'o yatsan hannunta guda d'aya yace "Har yanzu dai wannan yardan taki akwai gyara a cikinta,amma bakomai nasan sone yake kawo hakan,yanzu dai inaso kisan cewa... Kanta ta d'ago suna kallon juna sannan yace INNOBY HABIBTY."
Ma'ana (I Need No One But You Habibty) Dariya sosai tayi dan taji dad'in kalamansa sosai tace "Ana hubbuka Habibi"
Shima ya mayar mata da cewa "Ana hubbuki Habibty...

Farhan yayi saurin mayar da k'wallan dake shirin fito masa bayan ya dawo daga kogin tunani daya tsunduma a ciki.

Su Atif kuwa sun koma gida inda Mubinat take kwance a jikinsa tace bari naje na hada maka abinci nasan bakaci komaiba.
Bai dakatar da itaba dan yanajin yunwa sosai amma bayajin zai iya cin komai dan haka ya janyota ta fad'o jikinsa yace "Sis Mubee inaso muyi magana ne dake akan abinda ya faru ki saurareni please?"
"No Ya Atif bana son inji komai ya riga daya wuce tunda gamu a tare ina cikin farin ciki"
"Please ki saurareni maganace mai muhimmanci Sis Mubee ina so ki bani shawara ne yaya zanyi?"
"OK ina sauraron ka..."

Nasan kuna son jin bayanin Atif,toku biyoni anjima😜

     Vote and comment

                            
Team #KNJ

KOMAI NISAN JIFAANơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ