22

333 26 0
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

      by maman shureim
             🌺sad-nas🌺

*©Pure Momment Of Life Writers*
   We don't just entertain and educate,we also touch the hearts of the readers💐







Page 22
Farhan yana kwance a d'aki wayarsa tayi ringing,tashi yayi zaune dan ganin bak'uwar number ce ya d'auka tare da cewa
"Assalamu Alaikum"
Ta d'ayan b'angaren aka amsa da
"Wa'alaikumus salam,kana magana da Aliko ne"
"Aliko?" Ya tambaya cikin rashin fahimta
"Eh Aliko D'an gote,ina tayaka murnan sanar da kai cewa company'nku tazo na uku a wannan k'asar tamu ta Nigeria,congratulation Farhan Abdullahi Taimoor."
Tsaye Farhan ya mik'e tsabar murna yanata godiya cikin harcen turanci suke magana dama.
"Yana gama wayan ya kira wayan Abee nashi amma ba'a d'aga ba,wayan Ummin shi ya kira bugu d'aya ta d'auka
"Alu Habibi"
"Ummi,Alhamdulillah we have won Ummi,aina Abee?"
"Masha Allah tabarakallah Habibi"
Haka dai sukaci gaba da magana cikin harcen larabci wanda nidai bana jin komai game da abinda suke cewa,amma dai akan nasarar da company'nsu tayine.
Bayan sun gama waya da Mahaifiyarsa ne sannan ya kira mutane da dama daga cikin ma'aikatan company'n nasu ya sanar dasu cewa lallai a had'a taro na musamman gobe sabida nasarar da sukayi,sannan akai sanarwa gidajen TV da radio.

Farhan ya fito cikin murna dan yaje ya sanar da Abba,se yaga motar Ya Musty a pake a harabar gidan,hakan yasa ya isa parlour'n Abba da sallama aka gaisa.
Abba ne se Umma da Ya Musty suna magana,ganin hakan yasa Farhan cewa
"Abba dama nazo in sanar da kai company'nmu tazo na uku a Nigeria yanzu ake sanar dani hakan"
Ba Abba kad'ai ne yayi farin cikin jin hakan ba hardasu Ya Musty,Murna sosai suka taya Farhan da duk 'yan company'n.
Farhan yayi godiya sosai tare da cewa "Abba zanje can compan'yn tunda na dad'e banje ba,zanje muyi shirye-shiryen taro na nusamman gobe"
"To Farhan Allah ya taimaka,nima zan fito bayan na gama"
"Ba damuwa Abba sena dawo" sannan ya fita sunata faman murna inda Abba yake cewa gashi Mahaifinsa baya k'asar.
Shiga mai kyau Farhan yayi cikin suite brawn yayi kyau sosai sannan ya fito ya nufi gun motarsa.
Cak ya tsaya dan ganin Mubinat da Shureim sun fito zasu nufi parlour'n Abba,yasan Ya Musty ne ya aika a kirata.
"Ya Farhan ina zaka je?" Shureim ya tambaye shi
"Zanje company ne"
Da sauri Mubinat ta d'ago jajayen idanunta ta sauke akan Farhan. "Company Ya Farhan?" Ta tambayeshi
"Yeah Sis Mubee,ina tayaki murna company'nmu tayi nasarar zuwa na Uku"
Bata san sanda murmushi ya bak'unci fuskar taba,shima murmushin ya mayar mata sannan yace
"Mafarkinki ya zama gaskiya ko?"
Dariya tayi wanda ya bayyana hak'waranta a waje "Na tayaka murna Ya Farhan" ta fad'a cikin muryan kuka
"Thankyou,and you too" ya bata amsa suna masu kallon cikin idanun junansu.
Take hawaye yayita gangarowa daga idanunta. "Ya Farhan ina kwana" suka jiyo muryan Amal
Juyowa sukayi a tare sannan Farhan ya amsa "Lafiya Amal ya kuke?"
"Lafiya lau,congratulation yanzu Ahmad yake sanar dani abin farin ciki"
"Wlh kuwa Amal,thanks kema na tayaki murna"
"Thankyou Sir" ta fad'a tana mai kallon Mubinat
"Mubee,yaushe kika zo?"
Bata lura da yanayin fuskar taba se'a yanzu,Mubee lafiya naga kina kuka?
Shuru sukayi dukkansu babu wanda yayi magana,Farhan ne yace "Amal kije ki shirya,Ahmad zaizo seya d'aukeki ku sameni acan company daga can zamu wuce Store."
"To Ya Farhan" sannan ta juya cikin sanyin jiki ta koma gida.
Mubinat ta rik'o hannun shureim suka wuce zuwa parlour,shi kuwa Farhan yana tsaye yana binsu da kallo sannan ya shige cikin motar sa.
Ko daya shiga cikin motar amma seya zauna shuru fuskar Mubinat kawai yake kallo lokacin da suke kallon junansu. Tunani ne ya fad'o mishi lokacin suna hira da Mubee a parlour'n Umma inda take cewa
"Habibi Allah yasa muna cikin wanda zasuyi nasara a wannan harkan namu,kasan har mafarki nayi wai muna d'aya daga cikin masu nasara har a TV anyita nunamu?"
"Heey Habibty,harda mafarki?"
"Wlh da gaske nake gaya maka ba wasa ba"
"To Allah ya tabbatar mana da wanna mafarkin naki,sedai banaso a nunaki a TV"
"Why"
"Because za'ayita kallonki,which i don't like"
"Hhhhhhh se inyita b'oye fuskana a bayan Amal ai"
"Habibi burina guda uku ne kawai a yanzu"
"Tell me,menene su?"
"1 Inga na zama matarka"
"2 Inga Ya Atif ya samu mace ta gari,shiyasa na mishi sha'awan ya auri Amal amma seya cemin bata cikin irin 'yan matan da yake so"
"3 Inji yau ance Taimoor Company sunyi nasara,wannan abubuwa guda uku zasu sani cikin farin ciki ko a ina nake"
Muryan Atif sukaji yace "Nima dai ina miki fatan na farko dana k'arshen,but banda na tsakiyan dan sam bana sa ran yin aure anan kusa,in kuma zanyi to banda 'yan nigeria sedai Farhan ya bani k'anwarsa."
"Hhhh" sukayi sukayi dariya sannan ya zauna sukaci gaba da hiransu cikin raha...
  Bayan Farhan ya dawo daga tunanine sannan ya goge 'yar k'wallansa yaja motarsa ya fita.

"Ya Musty ina kwana?"
"Lafiya Mubinat,meya farune tsakaninku da Atif?"
"Wlh Ya Musty ban san komaiba nima,yadda kuke min wannan tambayan nima shi nakeyiwa kaina da kuma Ya Atif d'in,amma sam ban samu amsan ba har yanzu."
"Kina nufin babu wani abu daya shiga tsakaninku kona b'acin rai kona fad'a?"
Shuru tayi tana tunanin abinda ya faru shekaranjiya da dare,kuma ai sun daidaita komai ya wuce,hakan yasa ta sake cewa
"Eh babu komai"
"Mamana ki gaya mana gaskiya" cewar Abba
"Wlh Abba babu abinda ya faru nidai a iya sanina."
"Shikenan zanje in sami Atif d'in,duk yadda akayi shi yasan komai,dan Allah Abba kuyi hak'uri?"
"Haba Mustapha babu komai wlh,dama zaman tare aiya gaji haka,Allah yasa muji alkhairi"
"Ameen Abba zan koma"
"To agaida iyalan"
"Zasuji insha Allah."
Umma ta kalli Mubinat tace "wlh idan kinsan akwai wani abu tun wuri gara ki gaya mana kar kiyita mana wasa da hankali dan ranki inyayi dubu seya b'aci wlh."
Cikin sanyin murya tace "wlh Umma babu abinda na sani,kuma wlh banyiwa Ya Atif komai ba"
"Nidai na gaya miki,ai  dama seda na raya wani abu a raina tunda naga Farhan ya samu lafiya nayi tunanin zaki fara yiwa Atif shegantaka iri-iri,to wlh imma hakane zaki gamu dani kuwa."
"Mamana tashi ku koma ciki"
Ba tare da b'ata lokaciba suka wuce ita da shureim.
"K'walla Umma ta goge tace "Wlh Alhaji ni kaina nasan Mubinat bazata min k'aryaba,amma d'an yau baka shaidarsa zai iya yuwa akwai wani abu daya had'asune wanda bata son fad'a,dan na tab'a jin hiransu kamar  har yanzu babu wata tarayya na auratayya daya shiga tsakaninsu har yanzu."
"A ina kika ji?" Cewar Abba
"A bakin Mubinat d'in,bata san cewa naji ba,to shine nake tunanin ko shine dalilin,tunda kaji abinda Mustapha yace Atif ya gaya masa cewa bazai iya sanar dashiba,watak'ila kunyan fad'an hakan yakeji."
Shuru Abba yayi baice komaiba in banda tunanin zuci da yake yi.

Mubinat ce kwance ta kira wayan Amal
"Hello Amal kin tafi ne?"
"Eh Mubee muna company kinji muryan Ya Farhan yana bayani ko?"
"Eh tose kin dawo"
"Ok byee"
Wayan Atif ta kira yanata ringing sannan ya d'auka "Hello Sis mubee"
Cikin kuka tace "Ni baruwa da kai Ya Atif,ni kayiwa haka ko? Ashe dama ba sona kakeyiba Ya Atif,dan Allah ka gayamin laifin dana maka dahar zaka sakamin shi da saki,tunda nake ko fad'a mai zafi Umma bata tab'a minba amma se gashi yau ka janyo min duka agunta ko? Nagode Ya Atif..."
Kyat ta kashe wayar,hankalin Atif ya tashi sosai fiye da tunanin mai karatu.
Motarsa ya shiga se gidansu,yana isa yayi parlour'n Abba da sauri.
"Dan Allah Abba kuyi hak'uri na maida Sis Mubee,Abba bazan iya rayuwa koda na rabin yini bane idan babu Sis Mubee a tare dani,dan Allah Abba ku yafemin ku bani Matata mu koma gida wlh na mayar da ita na janye sakin Abba."
"Atif,ka nitsu dan Allah,babu wanda zai rabaka da ita amma ina so kamin bayani menene Mamana tayi maka?"
"Abba kayi hak'uri karka tambayeni dan Allah tunda na mayar da ita,inaso a bani matata mu koma gida."
"Shikenan Atif,kaje tana ciki sekuzo da ita nan kafin ku tafi"
Mik'ewa yayi da sauri yana cewa "To Abba nagode" sannan ya nufi gefen Umma direct d'akin Mubinat ya shiga da sallamarsa tana kwance Shureim kuwa yana zaune yana game.
Mik'ewa tayi tsaye tana hawaye "Me kuma kazoyi Ya Atif,kazone domin kaga kukana kodai wani sakin ka sake kawo min?"
Rungumeta yayi tsam a k'irjinsa yana hawaye "Nazone domin in d'aukeki mu koma gida Sis Mubee"
Da sauri ta d'ago suna kallon junansu kowannensu ya galabaita "Are you serious?"
"Yes Sis Mubee,Abba yana kiranmu"
Murmushi tayi tare da sake shigewa jikinsa tana jin dad'i har cikin ranta.
Fuskarta ya kamo yana share mata hawaye,ita kuwa lips nashi take kallo wanda shima ya lura da hakan,dan haka yabar share mata k'wallan yace "Muje" yana mata murmushi.
Bai ankaraba seyaji ta fara kissing nashi,tama mance da Shureim yana zaune,shi kuwa Atif sam ya kasa sakewa kamar yadda suka saba wanda ita kanta ta lura da hakan amma se bata damuba tace dashi "I love you"
Ya bata amsa da "I love you too" sannan ya rik'e hannunta suka fita akabar Shureim da lumshe ido yana murmushi...

Vote and comment

                                  Team #KNJ

KOMAI NISAN JIFAAWhere stories live. Discover now