64

469 31 4
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

      by maman shureim
             🌺sad-nas🌺

® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
    ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛ'Ş

#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
*#IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com



Dedicated to You Meela Adeel,nagode sosai da kulawarki a gareni Allah yabar zumunci ameen❤



Page 64
Bikin Farhan da Mubeenat sai k'ara towa yake yi,duk wani shirye-shirye an gama shi dan shi Farhan yace babu abin da za'ayi a bikin,amma sam su Atif sunk'i dan sune ma suka had'a musu dinner.
Mubeenat kuwa Ummin Farhan ne take ta had'a ta irin nasu had'in na larabawa dama kuma can Umma tana bata ruwan lalle da ganyen magarya tana shiga ciki. Ita kanta Mubee tana jin irin aikin da abubuwan keyi a jikin ta,na Ummin Farhan d'in duk dai ba wasu b'oyayyun abubuwa bane *INIBI NE BUSHASHSHE* irin wanda ake samu a makka,hmmm yana saurin sauk'ar da ni'ima babu wasa sam acikin sa dan cikin minti biyar zakiyi mamaki.
Sai kuma *man hulba dana habbatus sauda da zuma* wannan kullum chokali uku-uku take bata safe rana da kuma dare,amma shi man habba d'in chokali d'aya take bata sau uku a rana.
Bayan wannan abubuwan dana lissafa muku babu komai sai fruits,koda yaushe tana shansu sosai musamman ma kankana.

Yau aka shiga satin biki, Ango dai had'uwa ya gagara tsakaninsa da Amaryan sa,duk da cewa kusan kullum saiya zo amma baya ganin ta.
Ranan laraba tana shirin tafiya saloon saiga wayar shi "Slm Habibty"
Ita kanta tayi kewarsa sosai dan haka tayi magana cikin shagwab'a "Wslm Habibi had'uwa tayi wuya"
"Ban yadda ba kece dai bakya son mu had'u ko?"
"Wlh Habibi hidima ne,amma ai komai ya kusa zuwa k'arshe ka d'an k'ara hak'uri kaji?"
"Nak'i,kina ina?"
"Gani yanzu zamu je wanke kai dasu Amal"
"Wa zai kaiku?"
"Wlh ban sani ba tukun,may be Anwar ne zasu zo da Aisha"
"Ban yarda ba,ki sanar dasu kowa yayi tafiyar sa ni zanzo in kai Wifey na"
"Hhhh to shikenan zan gaya musu,idan kana kusa to ina jiran ka"
"On my way Habibty"
"Ok saika iso" sannan ta sanar dasu Aisha suna ta mata tsiya.
"Sis Mubee zan rakaki,kinga Ya Farhan ya shareni yanzu kamma"
"Hhhh haba Shureim kaima kasan Ya Farhan ba zai tab'a mancewa da kai ba,kama san kuwa kaine babban aboki?"
"Ni kuma,hmm Sis Mubee aini na b'ata da Ya Farhan ni dai muje in raka ki"
"To shikenan muje" suna isa waje yaga motar Ya Farhan ne nan ya juya zai koma Mubee tayi saurin janyo rigar sa tare da buga motar Farhan da d'ayan hannun ta tana cewa "Haba K'anina na kaina,kafi kowa sanin waye Ya Farhan ai dai ka mishi uzuri ko?"
Dai-dai nan Farhan ya iso gurin su sanye yake da suite blcak yayi kyau sosai ya kalli Mubee tare da cewa "Barni dashi Habibty,ba'a shiga tsakaninmu ai koba haka bane?"
Shureim ya zunb'uro baki yace "Ni dai mun b'ata tunda aka fara maganar auren ka da Sis Mubee shikenan ka sani a kwandon shara na d'auka ma nine babban aboki?"
Kamo hannusa yayi dukka biyu yana murmushi "Haba Shureim kar kasa Habibty ta mana dariya mana,na gaya mata fa cewa kai ne babban aboki harta kayan da zamu sa iri d'aya ne,ita kanta Habibty munfi sati bamu ga juna ba kayi hak'uri na karb'i laifina shikenan?"
Nan yayi murmushi "Toh na hak'ura amma fa zan biku"
"Of cause kaine ma a gaba ita sai ta zauna a baya ita kad'ai ko?"
Nan suka tafa itama sai dariya take musu tare da satan kallon Farhan dan yayi mata kyau sosai.
Suna gaba tana baya shi kuwa sai kallonta yake ta mirrow,data gano kallonta yake sai ta saka wayarta a kunne kamar mai yin waya tace "Hello Amal,ki cewa Ahmad idan yana driving ba'a kallon baya musamman ma daya san ke tashi ce har abada dan haka kice ya kalli gaban sa."
Farhan yasan dashi takeyi dan baiga lokacin data danna wayan taba kawai sawa a kunne tayi bayan ta kalleshi tayi murmushi.
"I love you Habibty" shine abin da ya furta a yayin daya juyo suna kallon junan su.
Kunya sosai taji ganin Shureim yana zaune kuma yasan me hakan yake nufi,sunkuyar da kanta tayi dan kunya daya kama ta shima ya d'auki kiran wayan da Ahmad yake mishi.
Har suka iso shagon saloon d'in waya yake yi,ita kuwa Mubee fitowa tayi daga motar shima yace wa Shureim ya jira shi a ciki sannan ya fito yabi bayan ta,tana shirin shiga shagon yayi saurin kiran sunan ta "Habibty"
Cak ta tsaya tana jiran isowar shi,ganin bai gama wayan bane yasa tace dashi "Karka damu kaje kawai idan na gama zan kira ka"
"Are you sure?"
"Yes thankyou"
"Habibty wait,ina so inji wani abu daga gareki"
Murmushi tayi tare da cewa "I love you too Habibi" sannan tayi saurin shigewa yana murmushi tare da cewa Ahmad "Wlh gaba d'aya ka dameni"
"Hhhh to shikenan bari in jira ku gama soyayyar taku saina sake kira"
"Ai ka koreta dan haka nima gani nan zuwa,kuma kayi sauri ka kawo Amal dan bana so ta zauna cikin kad'aici."
"An gama ango mai jiran gado"
"Allah ya shirya"
"Hhh ameen,nima dai na kusa in zama ango mai jiran gadon inji yaya kake ji a yanzu"
"Ka isheni Ahmad sai ka iso nama fasa tafiyan ina jiran ka"
"A'a kaje kawai tunda koka jirani ma ba'a mota d'aya zamu tafi ba"
"To shikenan" sannan ya katse wayar ya kalli Shureim "Me kake so in saya maka?"
"Ice cream"
"An gama babban Aboki"
"Hhhh Ya Farhan ka dena zolaya na fa"
"Da gaske nakeyi,kuma zaka gani,ka manta farkon zuwa na garin nan da kai na fara sabawa? Dan haka kaine babban Aboki"
"Ya Abdullahi fa da Ya Ahmad?"
"Duk a bayan ka suke ai kai daban ne aguna Shureim,infact tare ma zamu tafi Madina tunda kunyi JSCE"
Nan dai Shureim yayi ta murna suka ci gaba da hiransu cijin raha.
Bayan Amal da Aisha sun iso ne namma sukai ta tsokanar Mubee har suka gama Ya Atif ne yazo d'aukan su kamar yadda Farhan ya sanar dashi,Mubee ce a gaba nan suka had'e kai da Atif yana tayata rama abin da su Amal sukai mata.

  Yau take ranar sa lallai da dare yayi  sai feshe Mubee ake da turare masu k'amshin gaske har da Ya Atif yana ta zolayarta,nan taji kukan gaske yazo mata tana tayi Aisha da Amal suna mata wak'an *Ke kika ce kina so da bakice kina soba da ba'a baki shiba,ariii ke amaeya.* Atif yace "Ku dinga tafi mana" sannan ya ciro wayarsa yana veiwing nata wai zaije ya nuna wa Farhan yadda ake sa lalle. Umma ta lek'o ta gansu sai dariyan Atif rake yi.
Washe gari friday bayan an dawo daga Masallaci aka garzayo k'ofar gidan Alhaji Abdullahi Bakari aka d'aura auren *Farhan Abdullahi Taimoor tare da Mubeenat Abdullahi Bakari akan sadaki 500k.*
Farin ciki agun wad'an nan masoya bazai misaltu ba,kowannen su da irin farin cikin da yake ji. Ba sai na zai yana muku irin taron mutane da wannan aure ya samu ba,sai dai ince ku anyana a ranku. Daga Angon har Amaryan kun san su,kun san kyawawane musamman ma shi Ango Farhan😘.
Wurin tand'e-tand'e da lashe-lashe aka wuce shima basai nace komai akai ba,amma anyi albazaranci wanda shi dai Farhan bai so hakan ba,duk aikin Atif ne ya kashe naira bana wasa ba.
Haka akai ta pictures ta b'angaren Ango da Amaryan duk kowa farin ciki kawai yake nunawa su Ya Abdul-Hamid da Ra'is ma duk sun halarci wannan aure kowa yana farin ciki fiye ma da aurenta na baya.
Bayan sallan isha aka fara shirin dinner nan ma Ango yayi fita na kece raini dan harya fi Mubeenat kyau,inda yayi shiga irin nasu,itama tayi kyau sosai dan bamma gane taba.
Abdullahi shine yazo d'aukan Amarya shi da Shureim ne a gaban mota Ango Farhan yana zaune a baya har suka iso gidan su Mubeenat.
Su Amal ne ke mara mata baya har gun motar,inda Ya Atif yayi saurin zuwa ya bud'e mata k'ofa tare da feshe ta da spray harta zauna kusa da Habibin ta sannan ya rufe k'ofar tayi saurin sunkuyar da kanta dan wani kunyan sa take ji,gashi taga ya mata k'warjini sosai a ido.
Abdullahi ya juyo yace "Zamu iya tafiya Amarsu,kodai mu jira su?"
Shuru tayi dan kunya Farhan ne yace "Muje" tare da kamo hannunta yasa a cikin nashi ji tayi kamar ta nitse ya dena ganin ta.
Bayan an isa gurin dinner ne Abdullahi da Shureim suka fita a cikin motar suka barsu,Farhan ya tallafo ta zuwa kafad'arsa har zaiyi magana sai Mubee tayi saurin nuna masa yatsan hannunta inda Farhan ya hango *sadnas* ina ta faman rubutu a cikin littafina. Kallona yayi sosai tare da cemin "Sad-nas ko zaki d'an bamu minti goma?"
"Cikin sanyin jiki nace "To" sannan nabar cikin motar nima na tsaya daga waje ina gadin su...

Vote and comment

                       TEAM FARBEEN

KOMAI NISAN JIFAAWhere stories live. Discover now