13

391 28 0
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

      by maman shureim
            🌺sad-nas🌺

*©Pure Momment Of Life Writers*





Page 13
Assalamu alaikum 'yan'uwana mata,nice wadda kukafi sani da Hajiyan juyi. Nazo gidan radio ne badan komaiba sedan innemi gafarar ku daku da mazajen ku akan zalincin ku danayi.
Kamar yadda kowa yasan wacece ni ya kuma san sana'ata,tun bayan da wani d'an iska yayi tarayya dani na kamu da ciwo mai zafin gaske,ko danaje gun doctor se aka tabbatar min da cewa ina d'auke da cuta mai karya garkuwar jiki.
Hakan yasa na dakata da wannan sana'ar tawa,amma masu cuta irin tawa sukanzo muyi abinda muka saba.
Bayan nan nayi tafiya domin inje sayo kayayyakin da nake had'a maganin mata dashi,na kashe kud'i sama da dubu d'ari biyu da hamsin akan magun gunan. Bayan na dawone daga tafiyan sena zauna domin had'a tsimina mai suna "yankan wuk'a".
Na gama had'a komai da komai a cikinta,sena manta ban yanka d'aya daga cikin had'in ba. Na d'auko wuk'a ina yankawa,sakamakon kaifin wuk'anne sena yanke tafin hannuna yanka sosai. Kan in mik'e daga inda nake jini yayi ta zuba acikin wannan had'in tsimin dake gabana,ni kuma gaskiya bana jin zan iya zubar da wannan stimin dan kud'i mai yawa na zuba a kanshi gashi kuma gaba d'aya na had'ashi babu ragowa. Sam banyi tunanin wannan d'an jinin nawa daya zuba a cikin tsimin zai haifar da matsala ba,se dana je na tsaftace hannuna dana yanken kafin nazo na k'arasa had'a tsumin. Shikanshi tsimin dama bak'i-bak'i yake kuma jaja-jaja,dan haka na zuba acikin robobi na ajiye akazo aka sayesu tas harma ana neman wasu saboda tsabar k'warewa ta a wannan harkan.
Bayan na koma ganin doctor ne nake masa tambaya cikin dabara akan abinda ya faru da tsimina,doctor ya tabbatar min da cewa lallai mutane zasu iya kamuwa da cutar danake d'auke da ita.
Tun daga wannan lokacin se hankalina ya tashi sosai nashiga damuwa fiye da tunanin mai sauraro,saboda mutane sama da dubu d'aya suke sayan kayan mata a gurina,idan akace duk sun kamu da wannan cuta aina shiga uku,musamman ma masu kishiyoyi. Kullum cikin kuka da damuwa nake, na zauna zaman jiran abinda zaije ya dawo,wata uku na farajin k'ishin-k'ishin,kan in ankara naji anata zance mace ta kamu da cuta kuma bata bin namiji, lokacin danaji aminaina suna wannan hiran, shikenan nasan lallai maganar doctor ya tabbata hakan yasa nazo gidan radio domin neman gafarar ku dan Allah kuyafe min ni Hajiyan juyi yau duniya ta juyoni gareku...
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" mutanen dake tsaye suna sauraran bayanin wannan yarin yar suketa maimai tawa.
Taci gaba da cewa "wannan shine abinda nama mijina,na halaka shi na halaka kaina harma da sauran abokan zama na. Tir da mai hali irin nawa...
"Tabd'i" cewar Mubinat, amma gaskya baiwar Allah na tausaya miki, domin kin d'auki alhakin 'yan uwanki da mijin ki. Ta dubi tarin matan dake tsaye agun duk jikinsu yayi sanyi dajin labarin.
Su kuwa mazajen cewa suke "Allah dai yasa matata bata d'aya daga cikinsu" suka yiwa mutumin jaje sannan suka wuce gida cikin sauri dan suje su d'ibi matan su zuwa asibiti. Atif ya dubi Mubinat wanda taketa bayani mamaki ne ya kamashi sosai, ganin ita dai yarinya ce 'yar kimani shekara ashirin aduniya amma gata gaban manyan mata wasuma iyayen tane tana musu bayani kamar wata malamar su tana cewa...

"Haba 'yan uwana dan Allah mu dena yaudarar kanmu."
"Ina da wata k'awata mai suna Aisha Kabir, k'ila wasu daga cikinku sun santa,dan mahaifinta babban mutum ne agarin nan."
"Tare muke koda yaushe dani da ita da kuma Amal, Aisha ta aminta da maganin mata sosai tun muna 'yan mata komai aka bata sha takeyi. Munyi-munyi da Aisha tadena sha amma tak'i, ana aurenta saura wata uku Aisha tazo mana da wasu magun guna wai ance yana had'a mace ta matse sosai, mudai munk'i amin cewa dashi kuma mun hana ta amma tak'iji seda tayi amfani dashi. Dana matsi dana sha da kuma na tsarki duk tayi amfani dasu.
Kuma saya takeyi sosai sedai idan bataji ance ga sabon fitowa ba.
Bayan bikin Aisha da wata biyu ta fara rashin lafiya, kowa tunaninsa ciki Aisha take d'auke dashi, amma da akaje gun doctor se yace ba ciki bane kawai dai zazzab'i ne, akayita jinya zazzab'i yak'i tafiya se aka koma gun doctor. Bayan an gama dukkan bincike ne se aka gano cewa kansa ne da ita, kuma kansan a gabanta yake. Ita kanta tayi mamakin abinda doctor yace,wlh tun daga lokacin Aisha tasa damuwa a ranta ciwo yak'i warkewa, kuma ta sanar da doctor cewa maganin mata ne take amfani dashi tun tana budurwa wanda muma shaidane akan hakan.
Intak'ai ce muku watan Aisha hud'u a d'akin mijin ta Allah yayi mata rasuwa."
Mubinat ta tsaya da labarinta anan tana share k'walla tare da fad'in "Allah ya jik'anki Aisha" mutanen dake gurin suka amsa da "Ameen"
Mubinat taci gaba da cewa "Me yasa muke yaudaran kanmu ne mata? Inba yaudaran kaiba kina budurwa meya kaiki amfani da maganin mata wai kina matsi dashi? Kuna tunanin akwai wani maganin mata da budurwa zata sha harya sake had'e ta fiye da yadda Allah yayi mata halittan ta? Haba 'yan uwana! Wlh duk wanda ya gaya miki wannan to babban mak'aryaci ne kuma mayaudari, dan duk mai ilimi da tunani wlh baza a yaudare sa da ire-iren wad'an nan abubuwa ba. Gaba d'ayan mata yanzu akan maganin mata suke cinye duk arzikin su, basa iya yiwa kansu komai bare suma 'ya'yan su ko iyayen su da suka haife su. Kuma wlh maganin mata yanzu zanba ne, wata ma kuka zata daka tasa citta da kanumfari indai yana kamshi shike nan a baki k'ullin sa naira d'ari ace kisha da madara zakiga aiki. Wata ma bata san me dame aka had'a ba, amma duk se a yita saya daga baya ya zama miki illa a rasa gane me yake damun ki.
Dan Allah 'yan'uwa na mata mufarka, mudena yadda ana cutar damu bayan muma muna da damar gyara kammu da kammu base munje gun wata ko wani ya mana k'arya ya cucemu ba. Duk duniya babu abinda yake kawo wa mace ni'ima irin kwanciyan hankali, kai ba mace kad'ai ba hatta na miji, duk wacce bata yadda ba to dan Allah ki zaunar da mijin ki ki tambaye shi na tabbata zaki yarda da magana ta. Duk macen kona mijin da bashi da kwanciyan hankali to dole ki samesu da k'aran cin ni'ima wlh.
Bawai nace ku dena amfani da maganin mata bane, ina nufin ki had'a shi da hannun ki wanda ke kin san abin da kika harhad'a acikin sa bawai kije ki sayi fitina da kud'in kiba kizo kina ciza yatsa daga baya. Inda zakuci gaba da biyo ni, to  zakuji irin abu buwan dake k'arawa mace ni'ima da kuma d'an d'ano...
Atif ne yayi saurin shigowa gefen matan, dan gaba d'aya an zaga ye Mubinat ana jin bayanin ta mai d'auke da darusa iri-iri ya kamo hannun ta tare da cewa "Kuyi hak'uri, lokacin tafiyar mu yayi"
Muryan mata kake jiyowa ana cewa "Dan Allah kad'an k'ara mana minti goma bawan Allah"
Amma ina, bai ma tsaya sauraran suba, ya janyeta  daga k'arshe ma d'aukan ta yayi cak har cikin mota. Mutane se binsu da ido akeyi yayin da wasu suke cewa "Ai dole ya d'aga ta, irin wan nan bayani nata aima yaci ace ya goya ta wlh, k'aramar yarin ya da basira haka."
Suna tayi dai wasu samarai kuwa cewa suke ai itace matar Atif Muhammad Bakari d'an wasan k'wallon nan ai d'an uwanta ne, da bashi zata aura ba wani balarabe ne mai suna Farhan, sakama kon accident dayayi ne yayi losing memory d'in shi shine aka had'a ta da Atif d'in.
Wani daga gefe yace "short up duk bakusan komaiba, accident d'in Farhan d'in ai abune shiryay ye, kuma se Allah ya kaddara hakan zai faru dashi, mubar wannan zancen tunda bai shafemu ba danni wlh Atif d'in burgeni yake yi Allah, akwai iya short d'in ball."
Eh wlh gaskiya nima gayen yana kai min, infa ball ya shiga hannun sa tose ya cinyesu kamar maye wlh. Haka dai sukai ta hiran su sannan suka wuce...

"Me yasa ka janyoni ban gama magana ba Ya Atif?"
"Sabo da maza sunyi yawa kuma duk sun tsaya saura ran baya nanki ne kuma suna kalle min ke wanda hakan yasa naji kishi sosai a cikin raina."
"Hhhh kai Ya Atif har wani kishi kake yi a kaina?"
"Hmm bazaki tab'a ganewa bane Sis Mubi,i love you more than you'r thinking" ya fad'a tare da mai da kansa kan driving kamar mai yin tunanin wani abu.
Kallon shi take tayi tare da shafar sajen fiskar sa da hannun ta tace "Are you thinking of something?"
"Yes" yace da ita
"Tell me, mene ne?"
"Matso da kunnen ki kiji"
Ba musu ta matso dashi tana sauraron sa.
"Ina tunanin irin kukan da zakiyi yaune" ya rad'a mata tare da cizan kunnen nata a hankali yana mata dariya mai had'e da zolaya...

                                   Team #KNJ

KOMAI NISAN JIFAAWhere stories live. Discover now