47

305 17 0
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

     by maman shureim
            🌺sad-nas🌺

*©Pure Momment Of Life Writers*
        We don't only entertain and educate,but we also touch the heart of the readers❤

#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com







Page 47
"Slm"
"Wslm please Sis Mubee ina buk'atan kasancewa ni kad'ai."
Zama tayi akan kujerar dake d'akinsa tana kallon fuskarsa "Kasan dai bazan bar d'akinnan ba tunda na ganka haka."
"Sis Mubee pls...
"Haba Ya Atif nice fa,me yake damunka ko kuma waya b'ata maka rai ka gayamin zanje in rama maka nefa?"
Bai san lokacin da dariya ya kubce mishi ba.
"Hhhh wlh kinban dariya amma kije da gaske nake Sis Mubee i'm not in the mode pls?"
"Shikenan tunda kace haka,amma dai ina fata bani bace dan naga kamar laifin ya shafeni nima?"
"Kije mana pls leave me along Sis Mubee"
Cikin rashin jin dad'i ta fito ta koma d'akinta tana daga kwance tana tunani akan abinda Atif yayi mata.

Tun daga wannan ranan Atif baya sakewa duk 'yan gida garama Abba da Umma wanda su kansu sun lura kan cewa akwai wani abu da yake damun sa.
Koda Abba ya tambayeshi sai yace babu komai haka aka k'yale shi.
Tabbas Atif sai a yanzu yake tunanin maganganun mutane da aketa mishi akan Mubeenat wanda a yanzu gaba d'aya zuciyarsa ta karkata a gareta amma shi kanshi yasan bazaima yuwuba dan sunyi nisa ita da Farhan ta yadda babu mai iya rabasu cikin sauk'i.
Hakan yasa ya fara neman hanya amma duk ta inda yayi yunk'urin farawa se kuma ya bari.
Ganin hakanne yasa abokai suka dinga bashi mugayen shawara wanda shi baizai iya aminta dashi ba,dan yana ganin idan aka raba Mubeenat da Farhan to lallai zata shiga cikin wani hali wanda bazai so ya ganta a cikin damuwa ba.

Kusan sati biyu kenan Mubeenat ta kasa gane kanshi dan haka ranan taje yini a gidansu inda take gayawa Aisha abinda yake faruwa nan Aisha tayi ajiyar zuciya ta fara magana kamar haka.
"Agaskiya Mubee inaga mubar wannan maganar kawai,kema kuma kid'an ja baya dashi kamar yadda ya miki."
Cikin rashin fahimta ta kalli Aisha sosai tace "Me yasa kika ce min haka Aisha? Shin akwai wani abune da kema zaki b'oye min a yadda muke dake?"
"Ba haka bane Mubee wlh rashin sanar dake shiyafi komai dacewa dan bansan ya zakiji ba wlh"
"Dan Allah ki sanar dani Aisha babu wata b'oye-b'oye fa a tsakanina dake please?"
Muryar Hajiya Kaka sukaji tana cewa "Ba komai bane yake damun Atif sai k'aunarki da yakeyi a cikin zuciyar shi tunda jimawa wanda kafin ya bayyana miki har Farhan ya riga shi."
Cikin rud'ewa Mubeenat ta kalli Aisha wanda ta sunkuyar da kanta sannan ta sake duban Hajiya Kaka tace "K'aunata fa kika ce Hajiya Kaka? Meyasa bai sanar daniba to? Ke Aisha kinsan da haka me yasa lokacin dana nemi shawarar ki akan amincewa da Ya Farhan kika bani goyon bayanki akai batare dakin gayamin k'udirin Ya Atif a gareni ba? Haba Aisha agaskiya banji dad'in abinda kika min ba wlh,yanzu ya kike so inyi kenan? Dama wannan shine dalilin dayasa Ya Atif ya sauya min gaba d'aya kenan? Allah sarki Ya Atif me yasa kayi zurfin cikin sanar dani akan lokaci,yanzu yaya zanyi kenan ni Mubeenat? Dan Allah ku bani sharawa Hajiya Kaka?" Ta k'arashe maganar tana k'awlla.
Hajiya Kaka ta matso kusa da ita "Mubeenat shawara a gareki take,ke kika san yadda zakiyi ai"
"Wlh bansan meya kamata inyiba Hajiya Kaka,saboda zuciyata tayi nisa da soyayyar Ya Farhan wlh bansan ya zanyiba"
"Dan Allah Mubee ki dena kuka" cewar Aisha.
"Dole ne inyi kuka Aisha,gaba d'aya yanzu k'wak'walwata ta toshe ta dena aiki akan kowa Ya Farhan kad'ai take ganewa,to taya bazan yi kukaba bayan Ya Atif yana cikin irin wannan yanayin a yanzu?"
"Mubee Ya Atif fa ya riga daya hak'ura tunda Ya Farhan ya riga shi,kawai dai inaga har yanzu abun bai gama fita a ranshi bane."
"Taya zai fita a ranshi bayan gida d'aya suke dukkansu kuma yana ganinsu a tare ai dole zai dinga jin wani abu" cewar Hajiya kaka.

"Innalillahi wa inna'ilaihir raji'un yanzu miye abinyi Hajiya Kaka?"
"Babu wani abinyi ai yanzu sai dai kawai yabar gidan ya dawo nan da zama,dan hausawa sunce k'azantar da baka ganiba tsafta ce."
"Haba Hajiya Kaka,wlh Ya Atif ba zai bar gidammu ba"
"Ai kuwa dole yabar gidan dan bazan yadda ciwo ya kashemin jika ba."
"Dan Allah Hajiya Kaka kibar wannan maganan... "Idan ma nabar maganar ai aure zakiyi ki tafi ke ki barshi ina? Dan haka gara yabar gidan tunda wuri" tana kaiwa nan ta fice daga d'akin rai b'ace.
"Subhanalillah Aisha please ki bani shawara pls?"
Shuru Aisha tayi dan bata san me zata ceba,hasalima ita bata san da zancenba seda Kaka take gaya mata dan sam hiran bai had'asu da Atif ba,kuma koda ta tambayeshi randa yazo gidan ce mata yayi acikin 'yan watanni uku ne yaji  sonta yana shigarsa,kafin ya ankara kuma yaji har Farhan ya riga shi.
"Aisha kinyi shuru kina jina kice dani wani abu mana?"
"Mubeenat please karma maganar ta dameki dan shi fa yama janye a ranshi,ki auri Ya Farhan ai duk d'ayane kuma gaskiya Ya Farhan mutum ne na gari sosai kowa fa murna yake miki wlh harta Daddy ma."
"Nagode Aisha ni gaskiya bazan iya wannan wunin dana zoba,dan haka zan koma gida kawai."
"To yanzu wa zai mai dake?"
"Zan hau nape karki damu dama Ya Farhanne ya kawoni akan idan yazo d'aukana seya gaisa dasu Mum dan sauri yakeyi sosai yanzun kinsan jibi ne Iyayensa zasu zo."
"Mubee ki kirashi kawai yazo ya d'aukeki"
Badan ta soba ta kirashi ringing d'aya ya d'auka "Slm Habibty?"
"Wslm nace idan babu abinda kakeyi dama ina so in komane yanzu"
"Ok kin fasa wunin kenan?"
"Hmmm nidai idan kana wani abunne kawai in hau nape karna tsai da kai?"
"Hhhh Habibty ina kan hanya zuwa nan bada jimawa ba"
"Ok seka k'araso to" sannan ta katse wayar.
Daga ita har Aisha babu wanda ya sake cewa komai har Farhan ya iso,ita Aishan ce ta mishi jagora ya gaida su Mum da Hajiyan su Ya Musty da kuma Hajiya Kaka sannan Mubeenat ta musu sallama cikin sanyin jiki ta shige mota suka tafi.

Shi kanshi Farhan yaga canji a tattare da ita dan haka yayi magana cikin nutsuwa "Habibty yana ganki haka,akwai wani abu ne?"
"Ba komai"
"Ban yarda ba,please tell me kodai nayi laifi ne banzo akan kari ba?"
Murmushi tayi "Ai baka laifi Habibi,kawai dai bana jin dad'in jikina ne shiyasama na fasa wunin"
"Oh no Habibty bari muje muga doc"
Cikin sauri tace "Please Habibi muje gida kawai nasan gajiyane da zaran na d'anyi bacci shikenan wlh"
"Are you sure?"
"Enhen kasan bazan maka k'arya ba ai,i'm okay Habibi" tana kallon shi cike da so.
Shima ita yake kallo yana mata murmushi "Kinsan me Habibty?"
"Seka fad'a"
"Burina a duniya yanzu shine inga an d'aura mana aure,daga wannan rananne zan samu sukuni acikin heart d'ina"
"Ke kuma fa?"
"Ya Farhan bank'i ace yaune d'aurin aurena da kai ba,dan haka yanzuma please ka sanar da Abbi cewa kana son auren nan kusa,dan gani nake kamar mutuwa zanyi wannan buri namu bazata cikaba ni da kai."
Kallonta yayi sosai danya tuna da mafarkin daya yi na cewa anyi auren Mubeenat da wani wanda bashi bane.
"Habibty please ki dena fad'i hakan bana so,yanzu haka kin tayar min da hankali sosai wlh,bana fatan rasaki a rayuwata Habibty Allah ma ya kare."
Ganin yadda hankalinsa ya tashine yasata cewa "Ameen Habibina,kayi hak'uri naga bakaji dad'in kalaman nawa ba."
Murmushi yayi mata tare da cewa "It's okay Habibty, INNOBY"
"Me kenan?"
"I Need No One But You"
"Hhhh OLKUT Habibi"
Kallonta yayi da alaman tambaya akan fuskar shi,dan haka tayi murmushi tare da cewa "One Love Keep Us Together Habibi"
  Dad'i sosai yaji yace "Ki bari haka kar kisa in b'ata hanyar komawa gida.
Haka sukaita sanyayawa junansu rai da kalamai masu dad'i har suka iso gida,yana sauketa ya juya ya koma.

Atif ne a parlour'n Abba yana kallon ball shida Shureim.
"Ya Atif ina so inyi magana da kai ne"
"Ok Sis Mubee ki bari se anjuma kinsan bana so wannan wasan ya wuce ni"
"Shureim kad'an bamu guri kaji?" Cewar Mubeenat.
Bayan fitar Shureim ne taje ta kashe TV tare da tsayawa a gaban shi tana k'walla.
Kallonta Atif ya tsayayi tare da mik'ewa yaje inda take tsaye "Sis Mubee me haka kuma?"
Cikin muryar kuka tayi magana "Kayi hak'uri da kashe TV danayi kana kallo,Ya Atif ina so ka gaya min gaskiya akan abinda Hajiya Kaka ta fad'a min"
"Wai da gaskene kana sona?"
Tambayar a bazata yaji tazo mishi,dan haka yayi murmushi tare da cewa "Haba Sis Mubee ke dama baki san ina sonki ba harse na gaya miki?"
"Ya Atif ba wannan son nake nufi ba,ina nufin wai kana sona da AURE?"
"Hhh haba Sis Mubee wani irin aure kuma? Kin manta da abinda na gaya muku ne ke da Aisha,bana ra'ayin aure a k'asarnan kema shaida ce taya za'ayi ki yadda da maganar Hajiya Kaka?"
"Ya Atif kabar wasa wlh da gaske nake maka,Hajiya Kaka ta gaya min komai yanzu dana je gida."
Murmushi Atif yayi tare da kamo hannayenta biyu "Sis Mubee burin Hajiya Kaka shine taga munyi aure ni da ke,a tunaninta soyayyace a tsakanina da ke kuma kema shaida ce kusan kowa wannan tunanin yakeyi akammu,lokacin da maganar nemanki da Farhan ya baza ko ina shine take tambayata na sanar da ita cewa babu soyayya tsakanina dake shak'uwa ce kawai."
"Sis Mubee Hajiya Kaka tak'i amincewa da maganata dan har cewa tayi to lallai in dasa soyayyarki acikin zuciyata dan ita burinta kenan a duniya taga munyi aure."
Atif ya saki hannun Mubeenat tare da juya mata baya yaci gaba da bayani.
"Sis Mubee duk lokacin danaje gida sai Hajiya Kaka ta tareni da zancen ki,saina sanar da ita cewa to yanzu ai kin zab'i mijin aurenki kuma mutum ne nagari gashi ansan juna,amma sai Hajiya Kaka ta nuna babu ruwanta ita dai tana nan akan bakanta,tun abun baya damuna har yazo yana damuna Sis Mubee shiyasa kikaga kwanaki na canja miki bakya ganemin duk dan Hajiya kaka ta samu labari nayi,ashe ita kuma yadda ta fassara abun daban ne."
"Sis Mubee koda bakya tare da Farhan maganar gaskiya shine bawai so nake miki na kizama matata ba,sone na k'anwa da Yaya da fatan kin fahimta Hajiya Kaka so take ta b'ata komai."
Shuru Mubeenat tayi tana nazarin kalamansa "Ka tabbata Ya Atif?"
"Come on Habibty,kinsan fa Habibi ya kusa dawowa gara ki goge hawayenki kar kisa yazo yayi pornishing d'ina."
Dariya Mubeenat tayi yayinda ya sake matsowa inda take yace "Share hawayenki Sweet Sis,bana so ki sake sa maganar Hajiya Kaka acikin ranki,verry soon ma zan kawo muku matar da zan aura ta fiki had'uwa sosai fa" ya k'arasa maganar cikin zolaya.
Nan take Mubeenat ta sake se dariya takeyi ita dai taji dad'i tunda sun shirya da Yaya Atif nata.
Shi kuwa se sata dariya yake yana zolayarta amma acikin zuciyarsa shiya san me yake ji akan soyayyarta daya dabaibaye shi...

               

                          Team KNJ

KOMAI NISAN JIFAAWhere stories live. Discover now