33

264 22 0
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

      by maman shureim
             🌺sad-nas🌺

*©Pure Momment Of Life Writers*
        We don't just entertain and educate,we also touch the hearts❤of the readers

INA MAI BAKU HAK'URI DA JINA SHURU DA KUKAYI 2DAYS,HAKAN YA FARUNE SAKAMAKON D'AN RASHIN LAFIYA DANAYI NA ZAZZAB'I.
  AMMA ALHAMDULILLAH NA SAMU LAFIYA ZAKUCI GABA DA GANIN #KNJ# FIYEMA DA YADDA KUKE SAMU A BAYA NAGODE DA KULAWARKU ALLAH YABARMU TARE AMEEN...
             ❤❤❤



Page 33
  Washe gari da safe Umma ta shirya kanta sannan ta shirya Shureim inda Mubeenat ma ta shirya tare da wucewa gidan su Amal dan taga kosun shirya.
Tsaf suka shirya ita da Mahaifiyarta "Umman Amal ina kwana"
"Mubeenat,lafiya k'alau ya Ummanki da Shureim?"
"Lafiyansu k'alau muma mun shirya"
"Amal kinyi kyau"
"Hmm ina kyau d'in,kinaga Umma tace wai kada nayi kwalliya wai nafi kyau a haka"
"Sosai ma kuwa ai shiyasa nace miki kinyi kyau"
"Ba wanin nan"
"Wlh kuwa da gaske ai natural face naki yafi miki kyau."
Haka sukaita hira sannan suka fito dukkansu suka nufo gidansu Mubeenat.
Bayan d'an gaishe-gaishe da akayine Umma tace kawai mubi su Amal mu tafi in yaso Atif ya dawo damu tunda nasan Umman Amal baza sukai dare ba.
Haka kuwa akayi su Umma ne a gaba su Amal kuwa suna daga baya rik'e da Shureim a hannunsu.

Isar su ne aka taresu da kunun gyad'a da kuma taliya wanda yaji kayan had'in sosai.
Nan su Mubeenat sukayi d'akin Aisha da Shureim a hannunsu tana basu labarin yadda sukayi da Ya Ra'is a daren jiya.
  Mamaki sosai sukayi dajin yadda ta kasance tsakanin Ya Ra'is da Mubeenat.
Jin muryan Yayyun sunne yasa Aisha fita da gudu ta kamo hannun Ya Atif.
"Aisha har kin shirya ne?"
"Eh ina zaka haka?"
"Gidan Uncle Abdullahi zanje in d'anko su Umma ne"
"Ai sun iso,tare da Umman Amal suka zo yanzun suna ciki"
"Haba ina Sis Mubeenat?"
"Tana d'aki na"
Nan ya kamo hannun Aisha suka wuce d'akinta.
"Ya Atif wannan gayu haka,ina kwana?"
Murmushi yayi "Lafiya Sis Mubeenat yanzu kuwa dama zanje d'aukoku se Aisha tace min kun iso"
"Eh wlh kaga shikenan ka huta sedai ka kaimu yawo zuwa anjuma"
"I promise kuwa zan kaiku"
"Ina kwana Ya Atif?"
"Amal kina lafiya ya Umma da Baba"
"Lafiyansu lau"
Shureim ya karb'a a hannun Mubeenat tare da cewa "Ooh fine boy,Sis Mubeenat sorry naji abinda Ra'is ya muku jiya kiyi hak'uri kinji?"
"Haba Ya Atif aiba komai,mai sonka ne zaiyi maka fad'a idan kayi ba dai-dai ba wlh ba komai ya wuce."
"Hakane,bari naje da Shureim idan ya fara kuka zan dawo dashi"
"To shikenan" sannan ya fita.
"Hmmm Aisha kinji dad'i wlh" cewar Mubeenat inda Atif bai gama barin k'ofar d'akinba seya tsaya domin yaji abinda Mubeenat zata ce.
"Dad'in me Mubeenat?"
"Kina da Yayyu dewa gashi duk suna sonki da kulawa dake yadda ya dace,inama da ace nima ina da Yaya danaji da'i."
"Haba Mubeenat ai kema Yayyun kine kuma duk suna sonki"
"Aisha baki gane me nake nufiba,ina so ya zamana cewa nima akwai wani Yayana da muke zaune dashi a gidan mu,kullum ya d'aukeni mu fita yawo ya kaini gun friends nawa ya kaini school ya kuma d'aukoni hakan ba k'aramin farin ciki zai sani ba."
"Indai wannan ne to karki damu zan gayawa Daddy abinda kikace seya bawa Uncle Abdullahi Ya Ra'is ya koma gidanku da zama"
"Ya Ra'is kuma,gaskiya ni tsoron shi nake ji,bayida son dariya da wasa  kamar Ya Muhammad Ya Abdulhamid da kuma Ya Atif,gaskiya imma za'a tambayeni toni Ya Atif nake so ya dawo gidanmu da zama don duk cikinsu yafi sona sannan nima duk cikin Yayyuna nafi son shi."
Atif yana tsaye yana sauraron hiransu daga nan ya wuce yana murmushi tare da tunanin maganan Mubeenat.
Haka akai yinin biki lafiya zuwa bayan la'asar Amal da Ummanta suka koma.
Su Mubeenat kuwa harse bayan isha Abba da kansa yazo d'aukansu.
Suna cikin tafiyane a mota Mubeenat tace "Abba nima ina son Yayana d'aya ya dawo gidanmu da zama nima in zama mai Yaya"
"To Mamana yanzuma ai kina da Yayyu gasu nan dewa se wanda kika zab'a"
"To Abba ka dawo da d'aya cikin gidanmu mana wlh ina son in zauna da Yayana nima kamar Aisha"
Wayan Abba ne ya fara ringing ya d'auka tare da sallama "Mutanen Madina"
"Ya kuke ya hidima da iyalai ina 'yata da d'ana?"
"Alhamdulullah gamunan muna hanyan komawa gida mun fito yinin bikin kenan,ina nawa d'an Farhan?"
"To Allah ya sanya alkhairi ya basu zaman lafiya ga d'anka nan zaku gaisa"
"Assalam Abba"
"Wa'alaikumus salam Farhan my son,ya kake ina Ummi?"
"Alhamdulillah Abba ya Mubeenat?"
"Mamana tana lafiya dama yanzu kuwa take cewa tana son d'aya daga cikin Yayyunta ya dawo gidanmu da zama wai ita bata da Yaya a gida"
"Really Abba,tell her that I'm coming for her"
"Hhh okay I will,how is Ummi?"
"She's fine,can I talk to Mubeenat?"
"Sure my Son" sannan ya mik'awa Mubeenat tare da cewa "Toga Yayanki na Madina zaku gaisa"
Murmushi fal akan fuskarta ta karb'i wayan tare da cewa "To Abba" sannan tasa a kunnenta "Hello"
"Assalamu Alaikum Mubeenat"
"Wa'alaikumus salam,how are you Brother?"
"Well I'm good and you?"
"I'm good also how is Ummi?"
"Ummi is fine,she's always talking about you,I think she Love's you so much"
"Really?"
"Yeah,when are you coming to Madina?"
"Ooo I don't know Ya Farhan,but I will ask Abba okay?"
"Okay my regard to Ummi and... Sorry I forget the name"
"Shureim"
"Yeah Shureim,give my love to him okay?"
"I will,thankyou Ya Farhan"
"You're welcome, ma'assalam"
"I don't know what to say Ya Farhan,will you teach me how to speak arabic?"
"Sure,you say bissalam"
"Alright,bissalam Ya Farhan"
"Hhhh okay,Mubeenat how old are you?"
"I'm 13years old"
"13,are you sure?"
"Yeah i'm 13"
"Masha Allah"
"And you Ya Farhan?"
"I'm 23 Mubeenat"
"Okay,ma'assalam"
"Bissalam" sannan ta mik'awa Abba waya sukaci gaba dayin hira sannan ya mik'awa Abbi nashi wayan.
"Abokina ina so zamu zo Nigeria mu bud'e wa Farhan wani campani ne saboda munyi magana sosai da kakanan sa sun nemi shawarata a matsayina na Mahaifinsa,shine na basu wannan shawaran inaga za'a samu nasara sosai idan hakan ya kasance amma meka gani kai?"
"Tabbas wannan shawarace mai kyau sosai sedai muyita addu'a Allah ya tabbatar mana da alkhairi akan hakan"
"Ameen ameen nagode sosai zanzo nima insha Allah idan komai ya kammala domin fara shirye-shirye"
"Toba damuwa Allah ya wuce mana gaba,Allah kuma yasa albarka aciki"
"Ameen nagode seka jini"
"To shikenan agaida kowa da kowa" sannan Abba ya katse wayan yana gayawa Umma duk yadda sukayi da amininsa.
Farin ciki sosai Umma ta nuna tare da musu fatan alkhairi.
"To yanzu wa zasu nad'a anan d'in?" Cewar Umma.
"Eh to tukunna dai,seya zo maji yadda abin zai kasance,kinga ai zan samawa mutane da dama aiki a wannan campanin"
"Wlh kuwa,Allah dai ya tabbatar mana"
"Ameen" suka amsa dukkansu sannan sukai ta hiransu har suka iso gida.

Washe gari da safe Atif da Aisha suna breakfast se yake cewa "Aisha naji hiran da kukeyi da Sis Mubeenat jiya"
"Da gaske Ya Atif,tome ka gani akai?"
"Eh Sis Mubeenat taban tausayi gaskiya,dan haka yadda ta fad'a haka za'ayi"
"Ban ganeba Ya Atif,waye zai koma gidan Uncle Abdullahi da zama kenan?" Ta k'arashe maganar tare da ajiye spoon d'in abincin dake hannunta tana jiran amsar shi.
Shi kuwa Atif ya gano k'anwar tasa,dan haka yace "Ra'is mana"
Dariya tayi tare da d'aukan spoon nata taci gaba dacin abinci "Aina d'auka zaka ce kaine da bazan yarda ba,dan bazan yarda kabarni ba"
Atif yasan halin Aisha sosai,dan haka ya b'ullo mata ta nan.
"Ina! Ai muna nan tare babu inda zanje in barki Sweet Sis"
"Hhh amma fa Ya Atif Mubeenat tsoron Ya Ra'is take ji,kasan wai ita tafi son kaika koma gidansu da zama?"
"Haba dai?"
"Wlh haka ta gaya min wai duk cikin Yayyu kafi damuwa da ita sosai sannan itama tafi sonka"
Murmushi yayi Allah sarki Sis Mubeenat,tana bani tausayine tun da Umma ta rasu wlh shiyasa k'aunarta ya sake shiga zuciyata ina sonta matuk'a"
"Kana sonta matuk'a,kana nufin zaka aureta kenan?"
"Hhhhh ba haka nake nufiba small girl,ina sonta kamar yadda nake sonki ai duk ku k'annena ne babu maganar aure a tsakanina daku kinji?"
"Towa zaka aura Ya Atif?"
"Hhhh Aisha tambayar taki tayi yawa,ni gaskiya bani da ra'ayin auran 'yar Nigeria acan waje zan nemo matar aure"
"Hhhh lallai Ya Atif dama nima nafi so ka auro balarabiya ko 'yar india dan zakufi dacewa kai kyakkyawa itama haka"
"Hhhhh karki damu haka za'ayi oya kici abinci anjuma semu je yawo ko?"
"To Ya Atif amma zamubi mu d'auki Mubeenat ko?"
"Eh zamubi" ya fad'a yana murmushi tare da barin parlour...

                                Team #KNJ

KOMAI NISAN JIFAAHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin