37

242 16 0
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

     by maman shureim
            🌺sad-nas🌺

*©Pure Momment Of Life Writers*
         We don't just entertain and educate,we also touch the hearts of the readers❤







Page 37
Hon d'in motoci dasu Mubeenat sukajine yasasu fitowa zuwa harabar gidan.
Tun daga nesa Farhan yake kallonsu dukkansu ukku yana tambayar kansa wacece Mubeenat acikinsu,dan rabonsa daya ganta tun tana 13 years.
Gun motar suka nufa cike da murna suna musu sannu da zuwa.
Bayan duk sun fitone Ummin Farhan tace "Where is Mubeenat?"
Matsowa Mubeenat tayi zuwa gareta tare da rik'e hand bag d'in hannunta tace "I'm here"
Kallonta su Farhan da Abdullahi sukayi suna mamakin girman ta.
"Mubeenat kece kika girma haka?" Cewar Abbin Farhan.
Cikin jin kunya tace "Sannu da zuwa Uncle"
"Sannu Mubeenat lallai semun sha bikinki kafin mu koma"
Nan dai aka sa dariya sannan Abba yace "Bismillah mu isa"
Mubeenat se bin Farhan da Abdullahi take da kallo tana sak'ar zuci "To waye Ya Farhan d'in a cikinsu?"
Haka dai suka wuce parlor'n Abba,su Ummin Farhan kuwa suka wuce parlour'n Umma.
Seda sukayi sallah sannan Atif yayi serving nasu,canma dai Mubeenat ce ta zubawa Ummin Farhan tare da kallon screen d'in wayanta dake ajiye a gefe,fuskar d'aya daga cikin maza biyun nanne ta gani akai dan haka Mubeenat tasan cewa lallai shine Farhan.

Farhan ya kalli Abban Mubeenat yace "Uncle can i get a coffee?"
"Sure my Son" sannan ya kalli Shurim "Kaje kace Mamana ta kawo musu coffee"
"To Abba" sannan ya fice da gudu alokacin Mubeenat ta shiga toilet,dan haka Aisha taje ta had'a takai musu.
"Thankyou" cewar Farhan
"Wlcum" tace sannan ta fice.
Haka sukaita hira ana cin abinci daga nan kuma Atif yayiwa su Farhan jagora zuwa d'aya b'angaren da yake zaune dama akwai d'akuwana da toilet nasu masu kyau ba laifi dan gidan a tsare yake sosai.
Su Abba suna cikin hira a parlour'nsa shida Abbin Farhan da kuma Kakansu se Ya Musty. Sallamar Abban Amal suka jiyo,nan ya shiga suka gaggaisa sannan ya zauna anata hita.
Idanun Kakan Farhan gabad'aya akan Abban Amal yake,dan shi kanshi Abban Amal d'in se daya tsargu da irin kallon da yaga wannan tsohon yana binsa dashi.
Bayan an fito sallan magariba ne Kaka ya keb'e da Abbin Farhan yace "Wannan Mutum daya shigo waye shi?"
"Mak'ocin sune ana zaman mutunci sosai dasu ga gidansa nan babu nisa dasu" cewar Abbin Farhan.
"To akwai asiri a jikinsa"
"Subhanalillahi,asiri fa kace?" Abbin Farhan yasan lallai gaskiyane tunda daga bakin Kaka yaji,danba yau ya fara gane hakanba shiyasama ya yadda da maganan Kaka,amma kuma mamaki yaketayi a zuciyarsa to waye ya masa asirin?"
Kaka ya katseshi da cewa k'warai kuwa asiri mai muni ma kuwa,dama kuma ana haka sosai ne ta nan?"
"Wlh Kaka nidai ban saniba,tunda ban tab'a ganiba sedai naji wai-wai"
"To Allah ya wuce mana gaba"
"Ameen" sannan suka dawo gida.
Ya Musty yace "Abba mu zamu koma zan wuce da Aisha"
"To Mustapha mungode Allah ya kare a gaida Iyalai"
"Ameen Abba zasuji insha Allah" sannan yama sauran sallama suka tafi tare da Aisha.
Amal ma ta mik'e inda suka fito tare da Mubeenat zata rakata gida.
"Sis Mubee ina zakije?" Atif ya tambaye ta
"Zan raka Amal gida ne"
"Ok" sannan suka wuce suna hira.
"Mubee yau gamu ga larabawa"
"Hhhh wlh kina da abun dariya"
"Ke kuwa nidai a TV nake ganinsu se kuma yau gani gasu,gaskiya Allah yayiwa Mahaifiyar Ya Farhan kyau,kina ganinta kamar wata aljana,gaskiya Ya Farhan ma bai d'auko kyawunta ba wlh"
"Gaskiya dai kam nima se kallonta nakeyi bana d'auke idanuna fa"
Nan suka tafa suna dariya se sukaji muryan Sagir yana cewa "Amal ya kikayi dare haka yau?"
Cikin mamaki suka tsaya suna kallon shi.
"Kai kuma asu wa da zaka titseni da tambaya kamar na zama k'anwarka?"
"Haba Amal aidai naga a matsayin yayanki nake nima indai da kara"
"Tofa su angulu anyi takalmi,muje in rakaki kinji kima dena b'ata lokacinki kina sauraron shi."
Cewar Mubeenat sannan suka wuce yana binsu da kallo.
"Kinga iya shegen nashi ko,ni wlh bansan meya ajiyesuba har yanzu sunk'i tafiya se shegen sa ido daga ita Yar tashi har shi"
"Hmmm dadai ina ganin laifinki Amal,ashe dai gaskiyarki ce wannan ai damuwa ne zuwansu"
"Nagode Mubee zan shigo gobe"
"Ai nice da godiya kinsha aiki ki huta gajiya"
"Kun jiki wani aiki,seda safe" sannan Mubee ta fito zuwa waje.
"Haba Mubeenat,ban tab'a tunanin haka daga gareki ba"
"Oh saboda ni k'anwarka ce?"
"Yanzu dan nayiwa Amal gyara laifi ne?"
"Laifi ne sosai ma kuwa,yanzu fa aka idar da sallan magrib,kuma ni wataran bana kaiwa isha'i ne agidansun da zakace wani tayi dare bayan ga gida ga gida kuma iyayentama sunsan tana nan d'in ai"
"To Allah ya baku hak'uri"
"Ameen!" Ta bashi amsa a tsawace sannan ta wuce gida.
Haka ta shigo gida rai b'ace su Abba suna harabar gida zaikai su Abbin Farhan gidan su dan sunce bazasu kwana anan ba su takura musu.
Ko tsayawa batayi a gunsuba ta wuce.
"Sis Mubee"
Cak ta tsaya donjin muryan Ya Atif ya kirata.
Juyowa tayi tare da takowa inda yake tsaye gasu Farhan daga gefe "Na'am Ya Atif"
"Lafiya kuwa?"
"Lafiya k'alau"
"A'a Sis Mubee kamar ranki a b'ace na ganki"
"Sagir ne"
"Wani Sagir d'in?"
"Wannan na gidansu Amal yasa mana ido dewa wai yanzu har cewa yake meyasa Amal tayi dare haka"
Cikin sauri Atif yayi waje ya nufi inda Sagir yake tsaye "Kai Sagir,ka mugun kama kanka kana jina ko,ina ruwanka dasu dazaka titsesu kana tambayarsu? Kaika isa ka hana Amal zuwa gidannan ne,ko kwana Amal tace zatayi a gidannan babu wanda zai hatana dan haka ina baka last warning karka sake shiga hidimarsu wlh inba hakaba zanyi maganinka a unguwan Allah."
"To d'an gidan masu kud'i dama ida mutum yana da kud'i ai babu abinda bazai yiba"
Tasss kakeji saukar mari akan fuskar Sagir "Ni kake gayawa maganan banza,ko ance maka sa'an kane ni?"
Haba nan fad'a ya kaure tsakaninsu dama hankalin Mubeenat kaf yana waje da gudu ta fita taga dai fad'a sukeyi aise ta dawo da sauri "Abba Ya Atif da Sagir suna Fad'a"
"Fad'a kuma da Atif yau?"
Cikin sauri su Farhan suka biyo bayan Abba alokacin Atif yaji mishi ciwo a goshinsa su Farhan da Abdullahi ne suka rabasu inda Umman Amal da Samira da Amal d'inma suka fito zuwa waje.
"Atif meya had'aku da Sagir kuma?"
"Abba ya takurawa Amal ne da Sis Mubee dama tun ba yauwa ina samun labari akan dukkanin abubuwan da yakeyi ban tab'a mishi maganaba se yau,amma shine yake min maganan banza"
"Wani irin maganan banza na maka,yanzu dan nayiwa Amal magana akan tayi ba dai-dai ba laifine?"
"Me tayi maka na ba dai-dai d'inba?"
"Me kika mishi Amal?"
"Babu abinda na mishi,kawai munzo zamu wucene da Mubee shine yace wai meyasa nayi dare haka"
"Kaji ko Abba,a gidan bare take dazaka ce wani tayi dare,waye kaima tukunna da zaka titsesu kamar wani wanda yake da iko akansu? Wlh daga rana mai kamar ta yau karka sake shiga hidimarsu tunda ba wani abu daya kauce hanya sukeyiba."
Yana kaiwa nan ya wuce gida.
Abban Mubee yace da Abban Amal "Dan Allah kayi hak'uri wlh ni bansan Atif da Fad'aba sam"
"Bakomai wlh shaid'an ne kawai"
Nan Samira tayi magana cikin b'acin rai "Amma kuwa aiba wani abu yayiba dazai kaiga duka,kawai zamu koma garinmu tunda naga kamar har mun fara damun 'yan unguwa Sagir wuce mu tafi"
"Haba Samira meyayi zafi kuma haka da zakice haka,ayi hak'uri dai" cewar Abban Amal.
Umman Amal kuwa hannun Amal ta kamo suka shige gida inda Abban amal yakeba Abban Mubeenat hak'uri sannan ya wuce gida.
Abba ya kalli Mubeenat yace "Muje gida to"
Wucewa sukayi dama su Ummin Farhan da Kaka suna cikin mota basu fito waje ba.
"Habibi" shine sunan da take kiran d'anta Farhan dashi.
"Na'aam ya Ummi" sannan ya k'arasa ta gefenta ya rungumeta tare da bata peck a kumatunta kamar dai yadda sukeyi acan k'asashensu sannan sukai magana cikin harcen larabci Abdullahi ma yayi mata magana sannan Abbin Farhan ya zauna a gaba yayinda Abban Mubeenat yaja motar suka tafi.
Mubeenat taga daga ita se Farhan da Abdullahi a tsakar gida,hakan yasa tayi gaba batare da tace dasu komai ba.
"Mubeenat" ya kira sunanta da murya mai dad'i irin na larabawa.
"Na'aam Ya Farhan"
"Won't you say anything to me?"
Se'a yanzu ta tuna da cewa basu gaisa ba. Ya sake cewa "Ko kin menta dani ne?"
Dariyar hausar nashi takeyi tare da cewa "Wellcome to Nigeria"
"Thanks,but why are you laughing?"
"Hausar kace taban dariya"
"To ai gyaramin zakiyi not laughing"
"I'm sorry"
"It's okay"
"You say kokin manta dani ne,not menta dani"
"Hhhh sukayi dariya dukkansu sannan yace "OK manta right?"
"Yeah" tace dashi sannan ta sake cewa "Alright then good night"
A tare sukace mata "Good night" sannan ta wuce ciki suna dariya...


                           Team #KNJ

KOMAI NISAN JIFAAHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin