26

317 17 0
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

     by maman shureim
           🌺sad-nas🌺

*©Pure Momment Of Life Writers*
          We don't just entertain and educate,we also touch the hearts of the readers💐





Page 26
Atif ne zaune shida Abokinsa a gaban Doctor yana bayani cikin tashin hankali.
"Doctor i slept with her"
"Haba Atif,yaya zakayi haka bayan na gaya maka abinda kake d'auke dashi?"
"Doctor i'm sorry,wlh ba laifina bane,nayi iya bakin k'ok'arina dan inga na nisanceta amma hakan bai yuba,please Doctor gayamin cewa Sis Mubee bazata kamu da irin abinda nake d'auke dashiba" ya fad'a yana hawaye.
Doctor ya fara yimusu bayani kamar haka.
"Atif gaskiya seka kawota anyi mata gwaji kafin mu sani,sannan idan akayi mata gwajin baza muyi amfani da abunda gwajin ya nuna mana ba har sai an k'ara yin wani after 3 month daga nan sai a kara wani after 3 month,idan result din farko ya bada negative ba zamu d'auka negative d'in bane har sai an ga result na biyu idan ya bada negative still ba zamu d'auka negative bane,idan result na ukku ya bada negative shine zamu yarda cewa negative din ne."
"Idan final result ya bada positive to tabbas hakan yake positive d'in ne,abinda yasa ake yin awon har kashi ukku ga wanda ake tunanin yana d'auke da cutar shine  wasu tashi daya cutar bata bayyana kanta kuma bata karya garkuwar jiki sai ta dad'e tsananin dad'ewarta shine wata shidda zuwa tara,kafin ta karya garkuwar jiki wanda idan aka kai wannan lokacin dukkan sakamakon da aka samu to haka abun yake."
"Innalillahi wa'inna ilaihurraji'un,ba damuwa Doctor zan kawota insha Allah,fatan da nakeyi shine Allah yasa Sis Mubee bata d'auki wannan cuta ba,idan harta d'auka to lallai na cuceta Doctor."
"Muma fatan da mukeyi kenan Atif,but ka sani koda wasa karka sake kusantarta saboda yanzu haka bamusan me take ciki ba."
"Insha Allah doctor,base ka gayamin wannanba nasan abinda zanyi akai."
"To shikenan Atif,Allah ya sauwak'a,ka kuma tabbata kana shan maganinka."
"Hmm,Doctor me amfanin shan maganina indai akayi nasara Sis Mubee bata dashi to ai kaga dole zamana da ita yazo k'arshe kenan,amma nasan bazan iya rayuwa babu Sis Mubee a tare dani ba,dan haka babu wani magani dazan sha kawai zan jira mutuwata dan ta fiyemin zamana babu sis Mubee a rayuwata,bazaku tab'a gane irin son da nake yiwa Sis Mubee bane."
Yana kaiwa nan ya mik'e cikin damuwa,Doctor yanata mishi magana amm sam bai tsaya sauraron saba. "Allah sarki Atif,Allah ya baka lafiya" cewar Doctor.

Mubee kuwa tana kwance a jikin Farhan ta suma. Goran Faro Amal ta d'auko akan wani table ta bud'e tare da mik'awa Farhan yana durk'ushe ya karb'a ya yayyafa mata a fuskarta tare dajan d'ankwalinta ya shafa mata akai.
Acikin zuciyarsa kuwa addu'oi yaketa karanto mata.
Mutane ne a cike akanta,Abba da Ya Musty ne suke tambayar meya faru? Amal ta kalli Ya Farhan se kuma tayi shuru,Farhan yace "Kawai fad'uwa mukaga tayi."
Ya kalli mutanen gun sannan yace "Amal ku rik'eta" da sauri matan dake gun suka kakkamata shi kuwa Farhan yayi hanyan waje.
"Farhan ina zakaje?" Cewar Abba.
"Zanga wanine awaje Abba" sannan ya fita Abba yana binshi da kallo sam ya kasa gane yanayin da Farhan yake ciki a yanzu kawai.
Yana fita waje yaga  babu motar Atif,seya hango Ahmad zaune a cikin mota ya had'a kai da siterin mota.
Cikin sauri ya k'arasa gunshi tare da buga motar da hannunsa,Ahmad ya bud'e "Farhan lafiya?"
"Kai zanma wannan tambayan,me yake faruwa ne,me naji Amal tana gayawa Sis Mubee?"
"Farhan wlh nayi iya k'ok'arin dakatar da Amal amma hankalinta ya tashi sosai kasan yadda take da Mubee,wlh duk abinda kaji ta fad'a gaskiyane Atif ne yake gayawa sayyid batare dasunsan muna gurinba."
Juyawa Farhan yayi tare da shafar gashin kansa yace "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un"
Shureim ne yazo a guje "Ya Farhan,Sis Mubee ta farfad'o."
Kamoshi yayi "Shureim kaje ka cewa Sis Mubee karta yadda tace komai agun,kace nina aikoka sannan akunne zaka gaya mata ta yadda babu wanda zaiji kayi sauri."
Da gudu shureim ya koma ciki ta inda Amal take zaune ya sunkuya "Sis Mubee,Ya Farhan yace in gaya miki karki ce komai agun" sannan ya tashi ya koma waje.
Abinda Shureim ya fad'a kuwa a kunne Aisha taji komai.
Farhan suna tsaye a waje sega su Atif sun dawo,Ahmad ne yaja hannu Farhan "Muje ciki dan Allah karka ce mishi komai tukunna."
Aisha tana tunanin zata iya yiwa Farhan cin fuskane,amma data ganshi seta kasa,hango Atif datayi daga bayansune yasa ta mik'e da sauri taje ta gaya mishi abinda ya samu Mubee da kuma abinda Farhan ya aiko a gaya mata.
Cikin sauri Atif ya k'araso gurin,yayinda Amal tabar gun dan tasan zata iya gaya mishi maganganu marasa dad'i.
Karb'eta yayi daga hannun mutane yana shafar gashin kanta da yake kame a tsakiyar kanta yana cewa "Sis Mubee what's rong?"
Kallonsa kawai takeyi sega hawaye zir-zir a fuskarta. D'agota yayi cak ya nufi waje da ita Aisha tana biye dasu ya ajiyeta a cikin motarsa.
"Sis Mubee tell me what's happen?"
"You tell me Ya Atif,are you hiding something for me?" Ta fad'a tana hawaye
Jikin Atif yayi sanyi "Nothing Sis Mubee,I'm not hiding anything... "You're such a liar Ya Atif,ka gayamin me kake b'oyemin tun kafin in gano gaskiyar da kaina."
Yadda yaga ta fita daga cikin motarne tana masifa yasa shima fitowa yana k'ok'arin rik'ota yana bata hak'uri.
A can ciki kuwa wani irin ciwon kaine ya kama Farhan kamar dai yadda ya tab'a mishi acan Madina,an kuma tabbatar mishi da cewa yawan damuwane da yake sawa a ranshi ya jawo mishi hakan. Hakannema yasa ya tara jama'a tare dayi musu godiya sannan aka rufe taro da addu'a kowa ya kama hanya.
Fitowa sukayi yabar komai a hannu wani daga cikin ma'aikatan akan ya jira a watse seya rufe gurin sannan suka fito yana rik'e da Kansa.
"Farhan lfy?" Cewar Abba
"Lfy Abba kainane yake d'an min ciwo"
"Subhanalillah,Ahmad kuje ka kaishi gun Doctor"
"Abba base najeba zanje in kwanta a gida ind'an huta"
"A'a Farhan Mahaifinka ya gayamin komai game da ciwon kanka,dan haka kuje hospital kaga Doctor."
"To Abba,muje Ahmad" harda Amal suka tafi sannan su Abba ma suka wuce akabar Atif da Mubee da kuma Aisha suna bin motar su Farhan da kallo.
"Ya Atif bafa zan bika gidankaba,harse ka shirya gayamin gaskiya dan haka ni gida zan tafi kuma karkayi k'ok'arin dakatar dani."
"No Sis mubee,you can't do this to me we are going home"
"No! No Ya Atif bazan bikaba wlh senaji gaskiyan lamari,idan ka shirya gayamin to ina sauraronka."
"Aisha kid'an bamu guri dan Allah" cewar Mubinat,ba musu tabar gurin tana mamakin meya had'asu haka?
Ta maida kallonta gun Atif ta sake cewa "Da gaskene abinda naji game dakai?"
"Me kikaji Sis Mubee tell me,nayi alk'awarin zan gayamiki gaskiya wlh bazan b'oye miki komaiba just tell me please?"
Cikin kuka tace "Da gaskene wai you're H I V positive?"
Mamaki sosai Atif yayi dajin wannan maganan a bakin Mubee,dan shi yasan bai gayawa kowaba bayan sayyid.
Hannunta ya rik'o "Sis Mubee tell me who tell you please?"
"Karka damu da sanin wanda ya gayamin just answer me!
Cikin rud'ewa da ganin yadda take magana cikin tsawa yace "Yes it's true Sis Mubee,it's true but pease...tasss ta wankeshi da mari wanda seda Aisha taji,da gudu tazo gurin zata mari Mubee Atif yayi saurin rik'eta. Kud'i ya ciro daga aljihunsa ya mik'a mata "Kije kihau machine ki tafi gida Aisha kinji,and please karki sanar da Mum komai."
"Ka barni Ya Atif,koma me Ya Atif ya miki ai bai kamata ki mareshiba a matsayinshi na mijinki."
"Aisha kiyi shuru da bakinki karki shigo cikin maganan da bakisan komai akaiba."
Janyeta Atif yayi dan sam bata da niyan barin gurin ya samu abin hawa ya d'aurata sannan ya dawo amma seya hango Mubee can tana tafiya zuwa bakin titi.
Da gudu yabita tare da rungumeta a jikinshi yana hawaye "I'm sorry Sis Mubee,please ki saurareni."
"Let me go Ya Atif,you know that you're HIV positive and you slept with me! You're a monster Ya Atif!
"Sis Mubee please forgive me I'm so sorry,nayita k'ok'arin dakatar dake amma kikak'i wannan dalilinne yasa na sakeki dan kar incigaba da zama dake in cutar da rayuwar,amma danaji kin kirani kina gayamin Umma ta dakeki shine naji haushin kaina dan a tunani dukni na janyo miki,hakanne yasa nazo nace musu na mayar dake."
"Sis Mubee koda wasa bansan a raina zanyi having sex dake ba,kawai na dawo dakene dan bazan iya rayuwa babu keba shiyasa a wannan daren nayita dakatar dake inak'i amma kece kika tunzurani ta yadda bazan iya barin kiba,idan baki mantaba kinga canji sosai aguna wlh wannan shine gaskiyan Sis Mubee please karki barni please?" Yana kuka da hawaye sharb'e-sharb'e.
"Dukda haka Ya Atif laifinka kawai nake gani,dama can kasan kana da wannan cutar sannan ka aureni?"
"No,wlh bani dashi,asalima kece silar dayasa hakan ya sameni Sis Mubee."
"Ni kuma,kamar yaya zakace ni?"
"Sis Mubee tunda mukayi aure kike k'in in tab'aki kika kafa min dokokinki na kuma amince  miki,lokacin da muka tafi Abuja ne kiketa wasu irin  shiga sannan ina ganin yadda matan abokaina suke rayuwarsu cikin soyayya,rananne da muka fita da abokina shaid'an ya had'ani da wata yarinya har muka aikata zina da ita ananne na samo wannan cutar." Ya k'arashe maganar yana mai zuba gwuiwowinsa a k'asa "Please Sis Mubee believe me wannan shine gaskiyar lamarin."
"Sannan wlh bansan na kamu da wannan cutarba harse lokacin da kuka kaini hospital dasu Abba a wannan treatment d'in da Doctor yaminne bayan an sallamoni yake sanar dani cewa yana son ganina,bayan na fita mun had'une yake gayamin abinda nake d'auke dashi wanda shine ranan kikaga ban dawo gida da wuriba ko dana dawoma kika kasa gane kaina..."


                             Team #KNJ

KOMAI NISAN JIFAAWhere stories live. Discover now