9

373 34 0
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

     by maman shureim
           🌺sad-nas🌺

*©Pure Momment Of Life Writers*


wannan page d'in nakune readers d'ina na whattpad, thanks for the love and support.OLKUT😘😘😘


Page 9
Duk wani wuta dayake jikin Atif sedaya d'auke cak. Ita kuwa se wani murmushi take mishi tana kashe mishi ido d'aya. Hannunsa yasa ya bud'e mata k'ofar baya ta wuce ciki sannan tajanyo k'ofar.
Mazauninsa ya canja daga gaba zuwa baya batare da b'ata lokaciba Atif ya rabata da kayan dake jikinta tare da taimakon ita yarinyar nan take suka fara aika-aika acikin mota.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,Allah kayi mana katanga da irin wad'annan shaid'anun matan ameen."
Duk wani nau'i na farin ciki wannan yarinyar seda ta nunawa Atif,saboda taji dad'i sosai har cikin ranta wanda hakan yasa ta rik'eshi tsam ajikinta tak'i sakeshi.
Shikuwa gudun kar Hamza yazo ya tatdasu ahakanne yasa ya k'waci kansa tare da maida suturarsa dama ba dukka ya cireba ita yarinyarce dai ta cire komai na jikinta.
Bayan ta kimtsane lokacin ya koma mazauninsa can gaba seyace da ita "kiyi sauri kifita ga wannan bana so abokina yazo ya tarar dake acikin motarnan."
Dubu biyar ya bata,tasa hannu ta karb'a tare dayin godiya sannan ta fice tana murmushi.
Harta fara tafiya se kuma ta dawo tace"kozan samu number'n wayanka,dan gaskiya zanso mu sake mu'amala irin ta yau"
Atif da hankalinsa yake tashe yace" badamuwa kibani naki number'n zan nemeki inhar buk'atan hakan ta taso"
Cikin rawan jiki ta cire paper a jakarta ta rubuta ta mik'amishi sannan ta tafi.

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un" shine abinda bakin Atif yake furtawa tare da cewa "wannan wace irin masiface haka take shirin faruwa dani? meka aikata hakane Atif meyasa kayi hakan bayan ga Sis Mubinat naka agida?"
  Wad'annan tambayoyi yaketa jerowa kansa yayinda yaketa dana sanin abinda ya aikata.
Tsawon ninti goma kenan sega Hamza ya dawo yana murmushi yace "sorry for keepping you so long muje ko?"
Shuru Atif yayi sannan yace "muje" cikin sanyin murya.
"Yadai ango koharka fara yin baccine?"
Murmushi Atif yayi tare da cewa "please muje, and kuma kayi sauri."
Bamusu Hamza ya d'auki hanyar gidansu nanya ajiyeshi sukai sallama sannan ya wuce.

Tunda sukazo abuja Atif bai tab'ayin dare a waje shi kad'aiba sedai idan tare suka fita da Mubinat koda sauran abokansa da matansu.
Hakan yasa Mubinat tad'an damu dan har 11:24pm seta kwanta a parlour tana jiran isowarsa.
Ai kuwa setaji yana nocking tare da cewa "Sis Mubi"
Da sauri ta mik'e ta nufi k'ofan tare da b'udewa,ai kuwa seta tsaya turus tare da had'a rai tace "meyasa kajima haka Ya Atif?"
Cikin fargaba ya rufe k'ofan sannan ya juyo ya rungumeta yace "nasan nayi laifi i'm sorry Sis Mubi hakan bazai sake faruwa insha Allah" yana rungume da ita.
"To amma meyasa ka dad'e haka yau,waima ina kajene haka?"
"Na raka Hamza abokina hirane,yakaini danmu gaisa da matar da zai aura acan muka b'ata lokaci wlh please kidena fushi dani kinji?"
"Aiba fushi nake dakaiba,kawai dai naga baka tab'a dad'ewa irin yau bane shiyasa na damu,but bakomai muje dan bacci nakeji tun d'azu amma na gagarayi."
"I'm sorry my Sister bazan sakeba,kinyafemin?"
"Yafewa kuma?"
"Yes,kina jin bacci nahanakiyi ai dole in nemi gafararki"
"Hhh dama aini banrik'eka azuciyaba Ya Atif"
"I know,nidai kice kinyafemin" ya had'a hannayensa biyu agu d'aya.
Murmushi Mubinat tayi sannan tace "nayafe maka to shikenan?"
"Yes,thankyou so much" ya fad'a yana murmushi tare da d'agata cak se d'aki ya direta akan gado.
Peak ta manna mishi akunnensa tace " i love you" tana dariya.
Kamar daga sama yaji kalman akunnensa sannan ya juyo gareta yace "what?" Cikin mamaki
"Kallonsa take cike dajin dad'i tace "yes i love you Ya Atif"
Dad'i yaji har cikin ransa seya rungumeta yace "i love you more Sis Mubinat,inama da ace wannan kalmar da kika furta yana nufin kina sonane amatsayin mijinki ba Yayankiba,danafi kowa farin ciki yau aduniya."
Shuru tayi dajin kalamansa tare da sunkuyar dakanta kasa.
Furkarta ya d'ago yace "karki damu hakanma naji dad'insa sosai har cikin raina,bari naje na watsa ruwa."
Tana ganinshi ya cire kayan jikinsa dagashi se shorts nashi ya wuce toilet.
Mik'ewa tayi ta kwashi kayan zuwa mazauninsu sannan tadawo ta kwanta. Zancen zuci tashigayi "Ya Atif nayi k'ok'arin dasa soyayyarka acikin zuciyata amma dai still amatsayin Ya Atif nake ganinka akoda yaushe."
Atif seda yayi wankan janaba sannan yayi wanka ya fito ya sameta ta tsunduma ciki tunani.
Ruwan fiskarsa ya watso mata wanda hakan shiyadawo da ita daga tunanin data tsunduma cikinsa.
Murmushi tayi tare da k'are masa kallo,Atif ya had'u kota ina,wanda ta tuna da irin 'yanmatan dake bibiyansa har gida gashi da farin jini dake shi d'in d'an k'wallo ne... "Sis Mubinat is everything okay?" Ya tambayeta
"Yeah, I'm fine" tafad'a tana murmushi
"No i don't believe you" ya fad'a tare da zama kusa da ita ya mannata da jikinshi inda ta jingina dashi tare da lumshe idanunta tace " I'm fine"
Peack ya mata a wuyanta yace "are you sure?"
"Uhum" tace dashi cikin sanyin murya,shikuwa ya kasa fahimtarta dan haka yayi shuru tare da sake mannata dajikinshi sosai yana shak'ar kamshin dake jikinta...

Tun daga wannan ranan bai sake fita batare da Sis Mubinat ba.
Ita kuwa wannan 'yar iskan tayita zuba ido domin ganin kiran Atif ko zuwansa amma sam babu kod'aya. Hakan yasa ta damu sosai ita adole takamu da sonshi.

Yanzu watansu d'aya da sati biyu harma da kwana uku agarin abuja. Yau suka shirya suka dawo gidansu.
Mubinat se murna takeyi yau gata ga Ummanta ga kuma Shureim dan gidansu direct suka sauka kamar yadda ta nemi hakan agun Atif kuma ya amince mata.
Umma taji dad'in ganin 'yarta danta k'ara haske sosai sedai sam batayi jikiba.
Shureim yace "Sis Mubi Ya Farhan ma zai dawo nanda sati d'aya"
"Da gaske kake?"
"Eh bakwa wayane?"
"Gaskya mun kwana biyu"
"Tomeyasa Sis Mubinat?"
kanshi ta shafa tace "saboda Ya Atif baya so muna yawan magana dashi shiyasa,inaga yana zargine shiyasa kawai nima nadena kiransa."
"To Sis Mubi dama shi Ya Farhan d'in baya kirankine seke?"
"Uhm gaskya bai tab'a kiranaba nine nake kiransa,ranar dai nayi mishi gorin baya kirana shinefa ya kirani sau d'aya kuma tun daga rananma bamu sakeyin maganaba har yau sedai kawai Ya Atif yacemin Ya Farhan na gaisheni."
   Shuru shureim yayi yace "to Sis Amal bata da lafiya kwananta biyu a kwance zazzab'i da mura yake damunta"
"Subhanalillah, kwana biyu ina kiran wayanta akashe wlh" mik'ewa tayi taredasa takalmi Shureim yayi saurin cewa "ina zakije Sis Mubi?"
"Zanje duba Amal"
"Sis Mubi baki tambayi Ya Atif bafa,a islamiyya an gayamana cewa duk matar auren data fita batare da izinin mijintaba to tsinuwar Allah da Mala'ikunsane kebinta har taje ta dawo."
Jikin Mubinat yayi sanyi sosai dajin kalaman shureim k'aninta d'an shekara goma sha uku... tsayuwar mutum taji abayanta,tana juyowa sukayi ido hud'u da Atif.
Sunkuyar da kanta tayi,dan tasan yafahimci cewa fita zatayi.
"Ina zakije?" Ya tambayeta
"Gidansu Amal" ta bashi amsa cike dajin kunya
"Toki gaisheta,kuma 4pm zamu tafi gida."
Da sauri ta d'ago kai suna kallon juna tayi magana cikin sanyin murya "haba Ya Atif bamunyi dakai se bayan isha ba?"
Gwalo yayi mata tare da cewa "nafasa"
K'afafunta ta buga ak'asa tare da zunb'uro baki "ni wlh ban yaddaba"
dariya yayi tare da wuceta ya kamo hannun Shureim yace "dan Allah bakaga tayi muni ba Shureim?"
Shureim yayi dariya hhhh sannan yace "tayi kam."
  Itama dariyan suka bata sannan tabi shureim wai zata dakeshi,aikuwa se Atif ya d'agashi sama suka fara zagaye gidan da gudu suna mata dariya😄... nima dai maman shureim natayasu dariyan,kufa readers?

Vote and comment pls

                             TEAM #KNJ

KOMAI NISAN JIFAAWo Geschichten leben. Entdecke jetzt