18

334 23 0
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

       by maman shureim
             🌺sad-nas🌺

*©Pure Momment Of Life Writers*
   We don't just entertain,we touch the hearts of readers💐


     
      💐🌹💐🌹💐🌹
_*Wannan shafin nakune 'yan group d'ina sad-nas novel💋ku sani da bazarku nake rawa harma da juyi💃🏻 nagode sosai da k'aunar da kuke nuna min Allah ya barmu tare ameen*_
❤💐❤💐❤💐❤💐
                *IWALY*




Page 18
"Me kike nufi danine Sis Mubee,i'm your husband taya zaki dinga guduna haka? For God sake auren mu 3month+ Sis Mubee ahakan kike so muci gaba da zama kenan ina kallonki kina kallona? Wlh bazai yuba na gaji,indai ba wani abu daban kike nufi ba!
Kuka sosai takeyi ganin yadda ranshi ya b'aci sosai. Yaci gaba da cewa
"Kodai kina adana kanki wa Farhan ne?" Cikin sauri ta d'ago da idanun ta wanda yasha kuka tace
"Wannan wani irin magana ne Ya Atif,taya zaka min wannan zargin?"
"Taya bazan yiba Sis Mubee,indai ba haka bane to lallai zaki bani hakkina a yau d'innan! Yana kaiwa nan yayi hanyan fita daga d'akin cikin b'acin rai.
"Wlh bazai yuba Ya Atif,bazan tab'a mallaka maka kainaba sedai in zaka min dole." Sannan ta rushe da kuka wanda yasa shi tsayawa cak yana mamakin anya Sis Mubee ne tayi wannan maganan?
A fusace ya dawo tare da d'agota daga kwancen da take ya janye hijabin jikinta ya wurgashi gefe sannan ya rik'eta "Me kika ce Sis Mubee?"
Tsoron sane sosai ya kamata dan tun da take bata tab'a mishi gatse kamar na yauba. Cikin jin tsoro ta sake cewa
"Nace sedai kamin dole"
Kallonta yakeyi har cikin ido yace "Kin amince inyi miki dole?" Kai ta d'ago suna kallon juna,da sauri ta shige jikinsa tana magana cikin muryan kuka.
"Dan Allah kayi hak'uri Ya Atif karka min dole wlh...shhhh shikenan,zaki bani had'in kai?"
Kai ta girgiza mishi alaman a'a
Magana yayi cikin sanyin murya "Toya kike so ayi,kina so inje in fara neman matan banza a wajene Sis Mubee?"
Kai ta sake girgizawa da sauri alaman a'a
"Toya kike so inyi ki gaya min,me yasa kike son ki cutar dani Sis Mubee bayan ni kuma bazan tab'a iya cutar dake ba? Please give me this chance Sis Mubee,wlh ina cikin wani hali ina da buk'atarki sosai,please indai ba kina so in shiga cikin wani hali bane toki canja ra'ayinki please?"
Yana gama fad'in haka ya fita ya barta.
Tausayin shi ne ya kamata sosai,toilet ta shiga ta wanke fiskanta sannan tayi zamanta a d'akin nashi.
Kusan awa biyu tana kwance bata sake jin motsin Atif ba, hakan yasa taje d'akin nata,kwance ta ganshi yana juyi akan gado hannayensa suna kan cikin sa
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" ta furta,gaba d'aya ta rikice.
"Ya Atif, subhanalillah Ya Atif me yake damunka? Dan Allah Ya Atif kayi hak'uri ka gafarceni wlh bazan sake hanaka kaina ba, na amince dan Allah ka tashi." Kuka sosai takeyi.
"Bakomai karki damu,kije ki kwanta kinji?" Yayi maganan cikin wata irin murya mai ban tausayi.
Hankalin Mubinat ya sake tashi sosai "Dan Allah Ya Atif kayi hak'uri wlh bazan sakeba daga yau, na amince maka na mallaka maka kaina amma dan Allah ka tashi."
"Sis Mubee karki damu kije ki kwanta zan samu sauk'i...lips d'inta yaji cikin nashi tana mishi yadda suka saba,sam yak'i kulata "Sis Mubee stop it please" tare da janye jikinshi daga nata.
"Ya Atif hakan yana nufin kayi fushi dani kenan?"
"Banyi fushi dake ba,kawai dai bana jin dad'i ne zanso ki k'yaleni dan Allah"
Cikin sanyi jiki ta sake matsowa inda yake ta rungume shi tana hawaye.
Babu yadda ya iya da ita a hakan sukayi bacci...

Da asuba shine ya fara tashi ya wuce toilet,bayan ya fito ne seya tasheta tayi alwala sukayi sallah.
"Ya Atif ina kwana"
"Lafiya kin tashi lafiya?"
"Lafiya ya jikinka?"
"Da sauk'i"
"Allah ya sauwak'a,please kayi hak'uri da abinda ya faru jiya"
"Kidena damuwa Sis Mubee,ya riga daya wuce" yana gama fad'in hakan ya wuce zuwa wall drop ya fara shiri.
"Ya Atif ina zakaje da dassafen nan?"
Ba tare daya juyaba yayi magana "Zanje gidan Ya Musty ne,daga can zan wuce hospital"
Cikin sauri ta tashi ta k'araso inda yake ta rungumo shi ta baya "Dan Allah Ya Atif karka kai k'arana gunshi wlh na dena,bazan sakeba domin idan Abba yaji wlh zaimin duka please?"
A hankali ya juyo jin yadda ta rikice,kallon juna sukeyi cikin ido "Sis Mubee,bazai gayawa Abba ba, nasiha kawai zai miki."
"No Ya Atif wlh na dena Allah,please karkaje please my love."
Murmushi yayi yace "Ok shikenan,ki dena damuwa bazan jeba ba kuma zan gayawa kowa ba i promise." Yana shafar furkarta tare da matso da kansa yayi kissing nata.
Ya gama shiri tsaf, se tace dashi "Amma ka tsaya kasha tea mana kafin ka  fitan?"
"Ok had'a min"
Bayan ta kawo mishi ne ta zauna gefensa tace
"Ya Atif ina so in tambayeka ne,kuma inaso ka gayamin gaskiya,meka sani game da mutanen da suka d'aukeni,kuma suwaye suke kiranka a waya baka son d'auka a gabana?"
Ajiyar zuciya yayi sannan ya ajiye kofin tea d'in ya janyota zuwa jikin shi tare da rungumeta ta baya yace "Sis Mubee kina zargina ne?"
"Ba zarginka nake yiba,ina so gaskiya yaci gaba da kasancewa a tsakanin mune tunda kaga yanzu  mu ma'aurata ne na har abada."
Lips nata ya fara kissing saboda yaji dad'in kalamanta. "Sis Mubee,meyasa bakyamin kamar yadda nake miki?"
"Ai kaga yanzu safiyane shiyasa banci na k'oshi bane." Ta fad'a tana murmushi.
Zama tayi sosai akan cinyarsa tace "Tell me Ya Atif" hannayenta yana mak'ale a wuyan sa.
"Shikenan zan gaya miki gaskiya,but bazaki gujeniba ba zakiyi komaiba right?"
kai ta d'aga mishi alamun "Eh"
Atif yace "Wlh Sis Mubee bansan komaiba akan wanda suka miki haka,but insha Allah za'a samo su"
"To Allah yasa" cewar Mubinat.
Ya amsa da "Ameen" sannan yaci gaba da cewa. "Wanda suke kirana a waya ba kowa bane illa Mujahid."
"Waye shi Mujahid d'in?" Ta tambaye shi.

"Wani lokaci munje Kaduna meeting wanda zamuyi 2days acan kafin mu dawo. A Inda mukayi meeting d'inne na yarda ID card d'ina,k'anwar Mujahid ita ta tsinto ta bini har masau kinmu ta bani sannan ta bayyana min irin sona da takeyi tun da tasa idonta akaina. K'in amince mata danayi ne yasa ta nuna min zata iya bani kanta dan irin son da take min."
"Sis Mubee a wannan ranan shaid'an ya gifta a tsakanin mu har muka aikata zina,kuma tabbas ita yarinyar cikakkiyar budurwa ce na sameta.
"Bayan tawa biyu se Yayanta Mujahid ya kirani yake sanar dani cewa k'anwarsa tana d'auke da cikina na tsawon wata biyu dan haka inzo ko kuma su subiyoni Inda nake."
"Hankalina ya tashi sosai kuma na tabbatar da ciki nane tunda nine mutum na farko daya fara tarayya da ita."
"Haka na shirya na tafi kaduna,dama mahaifinsu ya rasu daga ita se Mamanta se Mujahid."
"Sun nemi da in aureta amma sam nak'i nace azubar da cikin. Su kuwa basu amince da hakanba,naci gaba da tura musu kud'i har cikin ya girma,lokacin aurenmu cikinta yana wata shida."
"Tunda cikin ya haura wata shida take ta wahala da matsala kala-kala,ni kuma na gaji da kashe kud'i dan haka na fita hanyar su."
"Kawai se ranan ya kirani wai an kaita asibiti haihuwa kuma suna buk'atan kud'i mai yawa aguna, bayan na tura musu kud'i mai yawane bayan awa biyu ya kirani yake sanar dani cewa ta haihu amma baby'n bata zo da raiba kuma ita  k'anwar nashi tana buk'atan k'arin jini."
"Haka na sake tura musu da kud'i amma sena gargad'esa da karsu sake kirana akan wani abu tunda baby'n ta koma."
"Bayan sati biyu ya sake kirana wai suna da buk'atar k'arin kud'i na jinyar k'anwarsa, tun wannan lokacin naci mishi mutunci tare da gargad'insa karya sake kiran wayana, dan asalima ita k'anwar tasa ce ta nemeni bawai nina neme taba."
"Wannan shine dalilin dayasa kikaga ake kirana bana d'auka saboda bana so ki fahimci halin da ake ciki."
Hannunta yayi saurin rik'owa yayin da take k'ok'arin tashi daga jikinsa yace "Please forgive me Sis Mubee, ki rufa min asiri kar su Abba suji wannan labarin please I'm sorry Sis Mubee?"
"Yanzu duk kai ka aikata wannan laifin Ya Atif,dama haka kake kenan? Ya Atif d'in dana sani da ba haka halayyar sa sukeba me yasa ka canja daga Atif d'in dah?"
Kuka sosai takeyi yayinda yake binta yana bata hak'uri.
Fad'uwar sa kawai taji a k'asa, da sauri ta juya cikin firgicewa tana girgizashi tana magana "Ya Atif,dan Allah ka tashi me hakan kenan,wlh banyi fushiba ka tashi please..."
Amma sam Atif baya ko motsi, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un please Ya Atif ka tashi dan Allah..."


                                    Team #KNJ

KOMAI NISAN JIFAAWhere stories live. Discover now