P19

496 30 2
                                    

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*

 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *19*

Zama yayi bakin gadon gami da dafe kansa da har sara yake jin yana yi masa.

Daga nan bai 'kara ha'duwa da ita ba, bai je ba haka itama bata sake dawowa inda yake ba.

Mu'een kuwa Ja'afar sun tafi dashi da yake anyi hutun makaranta.....so kowa sai yake jin babu da'di.

Washe gari da safe Ja'afar ya 'kira shi dan yaji ko ya shirya tafiyar anan Tahir yake sanar da shi cewa ai ya fasa tafiyar gaba 'daya maganar ma ta wuce.

Baiyi masa dogon bayani ba ya yanke 'kiran shima Ja'afar 'din bai damu ba cuz dama can baso yake yi ba, ya ha'kura ne dai kawai dan babu yadda zaiyi, amma ai abun a zahiri yake, duk wanda kaga ya aikata irin wannan abun to kuwa shi ka'dai yasan me ya taka, shi ka'dai yasan shirin sa akan hakan, Tahir 'din ne dai kawai yake da taurin kai shiyasa ya kasa fahimtar su... Amma yanzun da yaji cewa ya fasa sai yaji hankalin sa ya kwanta sosai.


〰〰〰
...... Basu sani bama ashe ko wancan case 'din da ya faru da Tahir.... Lawyern ne ya assaso shi tunda ya samu labarin binciken da Tahir yayi akan sa sai ya rasa yadda zai yi ya 'kas'kantar da shi da rayuwar sa, ya so yasa akashe shi amma sai ya fasa ganin cewa managern Oando babban aminin sa ne, dalilin haka ya sanya suka shirya deal akan hakan da zummar idan an tuhume shi kan satan fuel dole zai biya ku'din komin yawan su, wanda dalilin hakan zaisa ragowar dukiyar dake hannun sa zata sami gi6i na gaske shikenan daga ranan koda zasu nemi karawa dashi they ll not win against him dan basu da komai, rayuwar yanzu kuwa sai kana da shi ake yi da kai.

Ku'din da zasu biya 'din kuma shi manager zai ri'ke sai lawyer ya cika masa ya zama 100million shi kenan deal 'din su ya 'kare daga nan.... amma 'karfin addu'ah da kuma rashin sabo da cin amana ya sanya manager rashin natsuwa bayan sun gama shirya komai, sai gashi kafin deal 'din nasu ya kammala da kansa ya bayyana cewa an samu ku'da'den...sai dai bai sanar da kowa cewa su suka shirya hakan ba.

'Bangaren Lawyer kuwa ganin ha'kar sa bata cimma ruwa ba a karon farko ganin hakan ne ya sanya shi canza tunani zuwa plan B.



*****
Bayan wasu kwanaki sai Oando suka rin'ka damun Tahir akan ya dawo bakin aikin sa, shi kuwa gaba 'daya aiki dasu ya fice masa arai harma ya fara 'ko'karin neman wani aikin a wani wajen daban.

Itama Aishatu bata goyi bayan ya koma can 'din ba haka ma Ja'afar, sai ma tace suje Kaduna su 'dan kwana biyu daga nan su duba gidajen mahaifin ta dake can 'din daga baya sai su dawo kafin nan ko zasu rage damun sa.

bai 'ki shawarar ta ba dan ko shima 'din yana so ya 'dan kauce ko ma dan ya huta, cuz tun bayan faruwar lamarin Kano ta bar ransa kwata-kwata.

              Dalilin haka ne yasa washe gari suka wuce Kaduna su biyun su batare da kowa ya sani ba da yake ma har yanzu Mu'een na Azare gun Ja'afar shiyasa ya kasance su biyu ne sukayi tafiyar.

Sunje sunyi duk abubuwan da ya dace sun kuma huta 'din kamar yadda suka yi buri duk cikin sati 'daya,  harma sun fara 'ko'karin dawowa da tunanin barin Kano su koma Kaduna da zama gaba 'day musamman ma da suka ga yanayin garin yayi musu ba laifi sai suke ganin zasu dasa sabuwar rayuwa a can 'din.

NOORUL✔️Where stories live. Discover now