P73

372 35 7
                                    

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*
 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *73*

Shekarar baby uku Yah Deen ya kaita makaranta amma a kullum hankalin sa na wurinta, da yake ma kuka take yawan yi idan an barta, watarana har 'kiran sa ake ya baro office ya tafi makarantar ta su saboda tsananin rikicin da ta ke yi musu...ni kam sau tari sai dai idan sun dawo gida ya bani labari.

Yah Deen dole ya tilastawa kansa 'daukan hutu, da yake ma yana da burin ya koya min mota saboda tafiya makaranta ta ga kuma baby ma, hutun da ya 'daukan ne ya sa shi samun isashshen lokacin yin hakan, cuz duk bayan ya ajiye Jasmine sai ya dawo nima ya fara aikin koya min motor, da zaran lokacin break in su Baby yayi sai ya sake komawa makarantar ya duba ta sannan ya dawo gida, mu kan fita ne duk safiya da kuma yammaci idan an kaita Islamiya.

Cikin lokaci 'kan'kani kuwa na koya dan ban wani sha wahala wajen fahimtar komai ba, hutun 3weeks yayi sannan ya koma bakin aikin sa, kafin hakan kuwa sai da ya tabbatar ya nemawa Jasmine Special Nanny wacce ke kula da ita a makarantar ita ka'dai yana biyan ta.

Da sun yi break kuwa zata 'kira shi suyi hira da baby yaji muryan ta yayi ta jan ta da hira har sai yaji tana dariya kafin yake hanging 'kiran, aikin ta kenan kulawa da Jamsine har a tashi a school sannan ta wuce bayan ta sada ta da wanda yazo 'daukan ta.

A lokacin kuwa asbiti har biyu Yah Deen ke aiki da su abin sai ya zame masa ba hutu sam, wani sa'in har tausaya masa nake yi, dan duk yadda ya so ya ringa samun isashshen lokaci yana zama da iyalin sa hakan ya kasa samuwa, Baby kanta sosai take damuwa da rashin sa kusa dan ta sha'ku da shi ba laifi...motsin ta ka'dan zakiji ta ambaci sunan sa, ko wasa ta ke yi" Daddy ta fiye ambato.

Da farko shi ya cigaba da sau'ke Baby a school amma daga baya da abubuwa suka yi masa yawa sai na nemi ya bar Baby Jas in rin ka kaita makarantar amma ya'ki amincewa sam.

Da 'kyar na samu ya amince ya bani ragamar kaita makarantar da 'dayan motar sa wanda sanadin hakan yasa ya 'dan samu natsuwa ya rage fita sassafe, yakan yi shirin sa cikin tsanaki ya gama komin sa a nutse sannan ya fita office.

Banfi 2months da fara jigilar makarantar Baby ba nima na fara tawa makarantar.
Lokacin fitar mu da Baby ba 'daya ba haka ma lokacin tashin mu amma duk da haka sosai nake 'ko'kartawa wajen ganin kowa ya isa tasa makarantar akan lokaci.


***** 
    Bazan manta ba ranar wata talata Yah Deen yazo min da batun wai ya ha'du da wani matashi dake son yin aiki kuma wai ya iya tu'ki ba laifi, yace sunyi magana da shi kuma ya fahimci yaron na da natsuwa dan haka zai ringa sau'ke ni da Baby a school yana 'dauko ta in yaso nima idan na futa a lectures sai ya koma ya 'dauko ni cuz shi har yanzu ransa bai kwanta da nawa tu'kin ba.

Wallahi tun lokacin ban ji da'din 6ulluwar yaron nan ba, haka sam banji batun  Yah Deen in ya kwanta min arai ba haka kawai sai na tsinci kaina cikin rashin natsuwa.

Sai ma na tsaya da mamaki ina duban sa, domin da bakin sa ya furta wannan maganar kamar yanda ya ta6a furta min garga'di abaya akan shiga mota da wani, baki na ta6e cikin raina nake ayyana ina kuma kishin ya tafi oho? Ko da yake yace ya yaba da natsuwar yaron 'kila shiyasa ma bai damu 'din ba.
" Baki ce komai ba" Ya sake fa'di yana duba na.
Kaina na kawar gefe sannan nace" Toh ni Yayah me zance?"
" Akwai mana ai naga kamar ranki bai so hakan ba".
" A a ba haka bane kawai nayi mamaki ne...dan Allah Yah Deen yanzu miye abin sai ka 'dauki driver bacin ba shiga hakkin karatun kowa cikin mu akayi ba..".
" Shi ai namiji ne Nuree kuma sosai na yaba da hankalin sa, nima 'din zanfi samun natsuwa idan ya kasance na 'dora wani a bayan ku in ba haka ina office amma kullum hankali na a rarrabe, tunanin halin da kuke ciki nake koda yaushe tunda nasan ba wai sosai kike 'kware a tu'kin ba".
" Ni dai please a barshi Yaya, ka nema masa wani aikin".
" Haba Nuree..zaki fara ko?"
Yayi maganar yana janyo ni jikin sa.
'Dan 6ata rai nayi nace" ni bana san damuwa ne kawai Yayah..."
Bai bari na idasa maganar ba ya rufe min baki da nashi wanda hakan ya tilasta min yin shirun dole.

NOORUL✔️Donde viven las historias. Descúbrelo ahora