P36

400 31 1
                                    

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*

 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Wannan shafin naki ne Antyn mu ( Anty MAIMOUNATH O.G MAHNOOR)*
*Allah ya 'kare mana ke a duk inda kike.* 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *36*

   ........Dan haka dan me zata hana ni?...dan me zata raba ni da jin da'di na?..ina ma laifin mai son naka?..ai wanda yaso naka ma tamkar kai yaso, in ba mai 'kaunar ka ba waye zai yi maka hakan....idan maganar mutane kuma zaka biye zaka da'de bakayi abin kirki ba, dan su mutane komai ka aikata to a wajen su kuskure ne dole sai ka samu masu zagin ka, in zaka yi abu to kawai saki ranka kayi abu saboda Allahn ka ba wai dan gudun abinda za'a fa'di ba tunda ba haramun a ciki..."

Muryar Ammi ne ya katse tunanin da Ummah ta ke yi...inda Ammi tace " Dan Allah Umman Saudah karki ce a'a..kinga gidan yanzu bakowa sai ni ka'dai, idan ma bazaki bar min ita ba to ki bani aron ta  mu cigaba da zama zuwa wani lokacin insha Allahu da kaina zan dawo miki da ita...i ll bring her back to u safely kamar yadda kika bani ita insha Allahu.."
Ammi tayi maganar cikin kwantar da muryar ta.

  Murmushi kawai Ummah ta tayi sannan ta biyo bayan sa da fa'din " haba karki damu Ammi, ai 'da na kowa ne...Hudah kam yanzu 'yar ki ce, ga tanan Allah ubangiji ya baki ikon kulawa da ita..Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi".
Iya abinda Ummah ta fa'di kenan daga haka kuwa taja bakin ta tayi shiru.

Take Ammi ta washe baki ta fara godiya wa Ummah ta gami da 'kara janyo ni jikin ta ta rungume ni sosai.

Alhaji Baba yau har cikin gidan mu suka shigo shi da Baban mu, shima Alhajin 'kara mi'ka godiyar sa ga Ummah yayi cike da jin da'di, haka ma Ammi ta ringa zuba godiya.

Kafin su tafi ya ciro ku'di ya ajiye wa Ummah ta duk yadda tayi kan ya bar ku'din amma Alhaji Baba ko kulawa bai ba, Ammi ce tace " Haba Ummahn Saudah...idan kina haka kuma ai sai ya zama tamkar ba'a zama 'daya ba...dan Allah ki bar shi ki siyawa jikokin ki alawa dashi".
Su kam su Alhaji tuni sunyi waje inda suka sake fita tare da Baban mu.

Ko ranar kuwa ban kwana a gida ba muka wuce da su Ammi...sai 'kara jana ajiki ma da takeyi kamar zata maida ni cikin ta.

Tun daga ranar Ammi ta ninka komai da take yi min ada, komai nawa sai da ya fita daban, ta shagwa6ani ta riritani tamkar ni ka'dai ce abu mai sunan 'da data fara gani a fa'din duniya, sosai Ammi ta 'kaunace ni ta nuna min soyayya na zahiri, sai dai duk abin nan bai sa na zama mara kunya ba, sai ma shiru-shiru da na 'kara zama a ko'ina...Ammi ta hanani yawan surutu sosai take kwa6a ta a fa'dar ta wai tafi so in dinga yin komai da 'kwa'kwalwa ta.

Ma'kwabtan mu kuwa da yake ranar da abin ya faru kan idanun wasun su ne sai hakan ya sanya suka canza akalar zancen su da fa'din wai su Ummah ta saida ni sukayi ganin Alhaji Baba ya bawa Ummah ta ku'di...mutanen duniya sam ba'a iya musu wallahi...(na lura abin ma harda hassada a ciki).


     *****
     Zaune suke, Ummah ta, Baban mu, Yaya Usman dan shima wannan karan yazo gida har Addah ta Saudah dake gidan mijin ta...

Baban mu ne yake neman shawarar su game da sabon gidan gona da suka bu'de a can Jos wanda Alhaji Baba yake so ya 'dora shi akai amma shi yana ganin tamkar shekarun sa sunja ya kuma manyan ta yana ganin kamar bazai iya ba.

NOORUL✔️Where stories live. Discover now