P76

467 46 5
                                    

💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *76*

Safwan da barin inda suke 'din sai ya nufi 'dakin da aka kwantar da Deen, shi ka'dai ne 'dakin sai na'ura da aka sanya masa a hancin sa, hannun sa kuwa canular ne da tun jiya aka cire drip 'din da aka jona masa bayan ya 'kare.

Ko motsi baya yi amma kuma idanun sa gefe da gefe hawaye ne ke bi a hankali, hakan ne ya tabbatar masa da cewa Mu'een ya farka daga suman da yayi... _Alhamdulillah_ ya furta a fili yana me 'karasawa bakin gadon.

Hannu yasa ya cire masa abin hancin tare da zama gefen sa yana 'kiran sunan sa cikin natsuwa, bai amsa ba haka kuma bai bu'de idanun sa ya dubi Safwan ba illah hawayen sa da suka cigaba da tsiyaya sai dan wannan karon cikin turereniya wani ke bin wani.

Ko ba'a fa'da masa ba ya san zuwa yanzun kowa ya tsane sa, kowa ya riga ya san mugun halin sa da ke 6oye...kunyar Safwan yake ji mafi tsananin kunya, domin Safwan ba sau 'daya ba ba sau biyu ba yake yawan yi masa tuni akan illar Zina, Safwan sosai ya so yaga rayuwar gidan sa ta daidaita ko dan yadda da yayi da natsuwar Nuree yake kuma bata wata daraja ta daban, amma duk ya watsar da shawarwarin Safwan ya cigaba da rayuwar sa yanda yaga dama.

Ganin bai tanka shi ba sai aikin hawaye da ke bin gefen idanun sa ya sanya Safwan furta" Haba Mu'een manta ko kai waye kayi ne, me yasa zaka dinga zubda hawayen ka har haka? Cuta ai ba mutuwa bace Insha Allahu ba abinda zai sami Jasmine...bu'de idanun ka inyi maka wani albishir.."
Ya 'karashe maganar yana murmushi.

A hankali Mu'een ya bu'de lumsassun idanun sa ya sau'ke su kan Safwan dake zaune gefen sa, yun'kurawa yayi da niyyan tashi Safwan sai yayi saurin taimaka masa ya zauna da 'kyar yana dafe 'kirjin sa da hannun daman sa.

Bai iya ya kalli Safwan cikin idanu ba, fuskar sa gefe cikin muryar da daka ji zaka fahimci cewa yana jin jiki yace
"...Safwan Allah yasa albishir 'din Nuree ta yafe min zaka yi min...kuma kace min Baby na tana lafiya".

Hannun sa 'dayan Safwan ya kamo cikin nasa da alamun rarrashi yace da shi" Ka kwantar da hankalin ka please, kai fa namiji ne, 'karfafa musu gwiwa zakayi Mu'een ba wai kaima ka tashi hankalin ka ba".
" Dole hankali na ya tashi Safwan, da kanka kasan ni ne silar komai, ni na jawa Baby wannan abin, 'kila da ban kasance mahaifinta ba da hakan ba zai faru da ita ba.. gaskiyan Noor ne, gaskiyan ta ne da take neman cire ni daga rayuwar su, ha'ki'ka ban kasance abin alfahari a gare su ba...i wish mutuwa nayi Safwan da ace Baby ta taso da wannan tabon agaba na ina ganin ta da shi zuciya ta bazata iya 'dauka ba Safwan..."
Ya 'karashe da sakin kuka mai tsuma rai irin wanda bai ta6a yin irin sa ba..kansa ya kwantar bisa hannun Safwan ya cigaba da kukan sa.

Safwan kam shiru yayi shi kansa idan ka ganshi duba na farko zaka fahimci a matu'kar tashe hankalin sa yake.

Hannun sa 'daya ya 'daga ya 'dora a kan Yah Deen tamkar wani yaro 'karami da ake shirin lallashi, a hankali yace da shi" Kayi ha'kuri, abin ba da'di kam amma babu yanda zamu yi, u have to bear that pain Mu'een, ko ba komai yanzu nasan zaka fahimci abinda na da'de ina nuna maka a baya game da rayuwa, nd ka kwantar da hankalin ka Baby na nan lafiya haka Noor ma..yanzu haka ma na baro su ne zaune Baby zata ci abinci".

NOORUL✔️Donde viven las historias. Descúbrelo ahora