P71

455 41 7
                                    

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*
 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_This page is specially dedicated to my luvly sis...Zainab Kabir Ingawa_ 😍 _Godiya nake 'kwarai da gaske._

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *71*

A fili ya bayyana murmshin sa cike da jin da'di ya 'dagota ya sumbaci goshin ta" I luv u ".
Ya furta a hankali.

Wayar sa ya ciro ya 'dauke ta pics kala-kala sannan ya maida wayar cikin aljihun sa, ni kam kallon sa kawai nake yi, da gama 'daukan pics 'din sai ya kwantar da ita a hankali kamar 'kwai ya sake lullu6e ta.

Gareni ya dawo ya sumbaci goshi na..fuskar sa daf da tawa ya tsaya kallon cikin idanu na.
Yi nayi kamar zanyi kuka sai yayi saurin tambaya ta" Me kike so?"
" Ni bakomai".
Na bashi cike da shagwa6a in kwa6a fuska ta.
Girgiza min kai yayi yace"  Ban yadda ba".

Shiru nayi ni kam nayi 'kasa da idanu na zuwa kan hannu na.
Shima nan ya maida idanun nasa, batare da 6ata lokaci ba ya kai hannun sa kan nawa.

Yatsu na ya sanya cikin nashi ya sarke su, a hankali ta yadda ni ka'dai zan jishi yace" Ji nake kamar dukkanin farin cikin rayuwa ta yana tare da ke ne Nuree please tell me what u want".

Ban bashi amsa ba sai na girgiza mai kaina.
Hannun nawa ya sake ya dube ni da kyau sannan yace" To bazaki kwanta ki huta ba zaman yafi miki?"

Da yake dama na gaji da zaman, da jin abinda ya fa'di sai na sake mi'ka masa hannu na 'daya, shine ya gyara min kwanciya ta yanda zan dinga hango babyn, kusa da kaina ta yadda ni.ka'dai yanzun ma ya kawo kansa a hankali ya furta" Nuree bacci ki huta kinji?"
Da kai na amsa shi.
Sai ya sake fa'din" Zan fita amma bazan da'de ba...Mummy ma na nan in kina bu'katan wani abu ki gaya mata kinji?".
" To" nace da shi murya ta 'kasa-'kasa.
Sai da ya shafi fuska ta sannan daga haka ya fice daga 'dakin.

Anty Zainab, Ishaq, Saif da kuma Zaidu su yayiwa  forwarding photon Babyn kowa 'da'd'daya...yana gama turawa kuwa ya danna flight mode a wayar sa.

Saif na kan WhatsApp a lokacin so shi a take ya ga sa'ko daga Yah Deen, ko da ya bu'de kuwa photon Baby ya gani 'kasan an rubuta _My Diamond_ ai da sauri ya mi'ke ya nufi 'dakin 'dan uwan sa, Zaid na baccin sa kawai yaji an 'daka masa duka gami da fa'din" Zaid tashi kaga ikon Allah....".
Saif ya fa'di cike da 'kaguwa.

Tsaki Zaidu yaja ya juya 'daya 6angaren yana 'kun'kunin Saif zai dame shi da wannan lokacin.

Ganin hakan yasa Saif bar masa 'dakin ya ja 'kofan, direct wurin Ammi ya tafi, yana isa wajen ta kawai ya mi'ka mata wayar sa yana murmushi yace" Ammi guess what?"

Kallan wayar tayi tace" Me ya faru? Kamar Baby nake gani ko?"
Tayi maganar tana mai kar6ana wayar daga hannun sa.

Hannu Saif ya 'daga yana murmushi yace" Ammi Yaya ne ya tura min yanzun nan, ina jin mun samu little pumpkin ne a gidan nan".
Ya 'karashe maganar da tsananin farin ciki kan fuskar sa.

Ammi da mamaki ta kalle shi sannan tace" Kar dai 'yata ce har ta haihu? shine Mu'een ko.sanar da ni bazai yi ba? me ta haifa kuma ikon Allah"

Saif cewa yayi" Nima ban sani ba Ammi kawai 'kira mana Yayan muji daga bakin sa".
Mi'ka min wayata a can ta fa'di tana me 'kara kallon wayar Saif 'din tana murmushin jin da'di.

NOORUL✔️Where stories live. Discover now