P47

488 32 2
                                    

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*
 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

Those who remember Allah standing, sitting, nd lying down on their sides, nd think about d creation of d heavens nd d earth, (saying): “Our Lord! You have not created all this without purpose, glory to You! Give us salvation from the torment of the Fire.(Ali ‘Imran,3:191)🌷

🅿 *47*

'Dakin Yah Deen suka shiga tare inda yayi masa jagora gami da nuna masa bayin yace" Bismillah".

Shiga yayi ya 'dauro alwalar ya fito, yana fitowa sai idanun sa ya sau'ka kan gadon Yah Deen yanda ya sha gyara sosai sai da ya bashi mamaki, yana murmushi bayan ya kawar da idanun sa yace" Ashe fa yaron nawa nada tsafta sosai, irin wannan gyaran gado da ka iya ai har kafi wasu matan ma...kenan ma ko auren Alhaji yayi maka matar bazata sha wahala ba tunda har ka iya 6ata lokaci kayi irin wannan gyaran to sauran ayyukan ma duk zaka iya su...yaushe ka koyi aikin mata har haka ban sani ba...?"

Dum zuciyar sa ta tsinke da 'karfi dan yasan ba shine yayi komai ba.

Yayin da Uncle ya cigaba da fa'din" Kaida na san ko sharar 'dakin ka ma wahala yake baka ada...amma ji gidan nan fa ko'ina tsaf..."

  Murmushin 'karfin hali kawai ya 'ka'kalo ya sanya wa fuskar sa, sai dai inda zaka tona zuciyar sa Allah ne ka'dai ya san yawan beating 'din da take yi wanda ya kasance ba bisa ka'ida ba, a zahirin ma bai iya ya furta komai ba...cikin ransa yake ayyana" Allah ka rufa min asiri...harda rero addu'ar _Allahu Allahu Rabbii..la'ushriku bihi shai'an_..Har baisan sau nawa ya ambace ta bama tsabar rikicewa.

Da haka ya nifi hanyar bayi yana mai sunkuyar da kansa 'kasa...cikin zuciyar cike da tunanin..in shine zai yiwa mace irin wa'dan nan aiyukan ashe kuwa ba zata ta6a zama da shi ba har abada...baki ya ta6e sannan ya shige bathroom 'din.

Alwalar shima ya 'dauro ya samo Uncle a palour wanda da ganin sa sai ya mi'ke yana sake bin palourn da kallo yace.." Wai har da wannan abin matan ma ka'iya amfani da shi?"

Wannan karan kam sai da ya lumshe idanu ya furta" Rabbi help me" Kafin ya juyo ga Uncle 'din bayan ya bu'de idanu cikin dakiya ya amsa da fa'din" Wani abu ne Uncle?"

Da baki Uncle J ya nuno masa Burner..sai ya saki salati cikin ransa shaf ya manta da shi kwata-kwata in ba dan haka ba ai da ba zai bari ba ma balle har yazo ya gani, da i ina ya fara fa'din" Na..iya mana..Uncle ai babu wani wahala...Ishaq ne.. ya kawo min tsarabar turaren wuta daga garin su... kasan 'yan Borno ne su, shine fa na siyo wannan 'din".

Ya fa'di hakan ne kawai dan kare kansa amma ba wai dan ya san ko yanda ake kunna burner 'din ba..bai ta6a bi ta kansa ba, tsakanin sa da abin kawai yaji gidan sa na tashin da'd'dan 'kamshi idan Husnah ta kunna.

Hanyar waje suka nufa Uncle na fa'din" Ko de waccen yar Azare 'din ke zuwa tayaka ayyukan gidan?"
Ya fa'da da sigar zolaya.
Da sauri Deen ya ja ya tsaya kamar zai yi kukan an fara gano sirrin shi yace " Haba-haba.. Uncle kaifa mahaifi ne...me yasa zaka min irin wannan zargin dan Allah..yarinyar da ma tun dawowa ta bansa ta idanu na ba taya zata taya ni yin wani abu?"

Murmushi Uncle J yayi sannan yace" Abin naka ne ai da ban mamaki ga duk wanda ya sanka Mu'een..."

Shiru yayi bai sake fa'din komai ba, cuz ya lura idan ya cigaba da tanka masa zai iya tona asirin kansa da kansa.

NOORUL✔️Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz