P93

288 28 3
                                    

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*
 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *93*

       Satikai da dama suka shu'de har ya kasance yanzu wata guda kacal ya rage wa Noor ta kammala makaranta, yayin da Yah Deen har yanzu ke hutu be koma bakin aikin sa ba.

Sosai ya 'kagu ya gansa gaban matar shi amma abu ya gagara gashi ko waya basa yi da ita.

Anty ma ke yawan 'kiran sa shima yana 'kiran ta amma ko ta ha'da shi da Noor bata cewa komai..Anty duk bata san hakan ba dan da ta ha'da su take barin wurin ta tafi sabgar ta, shima 'din yanzu ba magana sosai yake yi ba dan haka duk shiru suke yi babu me ce da wani uffan.

Sau tari ita ke gajiya ta kashe wayar ko kuma ku'din dake wayar ya 'kare abanza sannan 'kiran ya yanke.

Idan yaga haka sai yayi murmushi kawai, wani sa'in yace" Zan kama ki ai yarinya bari kizo hannu na".

Barin Shuwarin yayi ranar wata litinin da sunan zashi Abuja duba wurin aikin sa daga nan kuwa daya kammala abinda yake yi sai ya nemi ticket ya wuce malesia ko Anty bata san zai zo ba sai 'kiran ta yayi ya sanar da ita cewa ya shigo.

Anty kam mamakin sa ne ya kamata dan bata ta6a zaton zai zo a wannan lokacin ba...bata san cewa ya samu 'karfin jiki har da zai iya doguwar tafiya irin haka ba.

Sai bayan ya iso kafin ya 'kira ya sanar da su Ammi yana dariya.
Ammi ma dariyar tayi tace" Kaji kunya ai...sai kace wacce bazata dawo ba Mu'een?"
'Yar dariya yayi yana sosa kansa.
Ammi sai tace" Antyn ka dawo to itama ta huta wa ranta da yi ma gadin mata tunda ka wanki 'kafa kaje..".

Dariya kawai yayi yana cire wayar a kunnan sa yace" Anty kinji Ammi wai ai sai ki koma gida tunda nazo".
Murmushi Anty Zee tace.
" Dama fa Umrah zamu wuce wai da ita da ta 'kare karatun .."
Take ya yatsina fuska gami da fa'din" A a Anty ni dai ban yadda ba kawai kiyi tafiyar ki, bacin ni nawa Jasmine al'kawari da kaina kuma sai ariga ni ki bari kawai zamu biki daga baya...Yau she ma akayi shawaran tafiyar ni ban sani ba, wato da banzo ba sai dai kawai inji kun tafi..ai kuwa ba da ita za'a yi wannan tafiyar ba".
" To ai shikenan zan yi magana da Baffan ku inji me ze ce shi kuma, kasan tafiyar daga wajen sa ne..".
Zama ya gyara yana duban Anty yace" Kice masa wurin wani likita na nazo kuma sai an yi 2months ana duba ni kafin in koma kar yace taho bada sanin sa ba..kuma kinga idan yaji cewa zan 'dan jima 'kila ya yadda bada Noor za'a Umran ba".
Dariya Anty Zee tace
" Ba wani ni nan..ni dai bazan yi 'karya haka kawai ba".
" Haba my one nd only Aunt dan Allah kiyi ha'kuri..ni ne fa?"

" Kai 'din dai".
" Anty please ki taimake ni kinsan halin sa fa yanzu sai kiji yace ban gama warkewa ba ina yawo bana son surutai wallahi".
" Toh dama me yasa ka tahowa gashi ma ko su Ammi basu san da batun ba".
" Ganin matata nazo Anty kuma ma ai na sanar da da su yanzu..".
" Amma yaushe zaka koma..?"
" Gaskiya ba rana".

Idanu Anty ta zaro tana duban sa sai yace" Erh mana...dan nifa gaskiya Anty 'kafa ta 'kafar mata ta haka kawai zama ya'ki 'karewa da banzo bama da shikenan anyi da ni tunda gashi shirin tafiya wata 'kasar ma kuke yi abin ku da Allah ne ka'dai yasan ranar da zan ganku..ni bawan Allah".
Ya 'karashe da karkata kansa.

" Kai kasa ni ai, dududu wata nawa ne, kayi shekaru biyu ma baka ganta balle watanni biyu kacal?"
" Su 'din Anty sai kiga sun fi yi min tsawo..".
" Hmm" kawai Anty tace tana murmushi.

NOORUL✔️Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt