P81

402 31 5
                                    

💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *81*

Bin bayan sa da idanu Ammi tayi har ya 6acewa ganin ta, sannan ta dawo da hankalin ta ga rubutun da yayi, a hankali ta 'dago takaddan ta sada shi da idanun ta...

Wani tu'kukin bakin ciki taji ya mamaye mata zuciya...sakamakon ganin rubutun da yayi.
Saman la66a ta furta" Mu'een ya raina ni da yawa".

Abinda ya rubuta 'din yawo ya dinga yi mata aka, sake 'dago wa tayi ta karanta karo na biyu tana mai cize le6en ta na 'kasa.

Noor da bata san abinda ya rubuta ba a hankali ta 'karaso gaban Ammi ta dur'kusa tana kuka take ro'kan Ammi akan ta yafe masa kar tayi fushi da shi, tace ita ba nufin ta tsakanin su ya 6aci ba da shi bane, rayuwa da shine ka'dai bata so ayanzu...
Amma bata ce da ita 'kala ba kawai ta saki takkadan ya fa'do 'kasa dai-dai 'kafafun Noor, a hankali Ammi ta 'daga kafar ta tayi waje tana mai jin wani abu na taso mata, tausayin Noor gami da Danasanin bawa Mu'een auren ta da suka yi, ba kowa ce mace ba zata iya irin hakan, ace duk irin abinda yayi mata amma still burinta taga bai samu sa6ani da mahaifan saba, sa6anin matan yanzu da wasun su da kansu ma suke raba tsakanin mijin su da iyayen sa saboda son zuciyar su.

Kuka sosai Noor ta sha har kanta nayi mata ciwo mai tsanani, tana hawaye ta 'dago takkadan da Ammi ta jefar da niyyan ganin yawan sakin da yayi mata amma abinda idanun suka gani sosai ya bata mamaki take kakan ta ya tsaya cak, 'kurawa rubutun idanu tayi tana karamtawa tana 'karawa" _Kiyi ha'kuri.. bazan iya sakin ta ba Ammi_ ".
Abinda kawai ya rubuta kenan...cikin zuciyar ta ta furta _Allahumma ajirni fi musibati_ ...yayin da a fili ta furta" Wallahi ko babu saki tafiya ta zanyi bazan sake zama da kai ba".
Haka ta 'karashi kukan ta tayi shiru...zuciyar ta cike da haushin Yah Deen ji take tamkar ta sha'kesa.

Deen kuwa tunda da barin sa wurun Ammi direct 'dakin sa ya wuce ya 'dauki key kawai yayi waje.

Can wani gida can wani gidan sa da yake ginawa bai 'karasa aikin ba ya tafi da yake babu wani nisa sosai da gidan nasa na asali.

Babu komai a gidan na amfani, amma haka yake tahowa yayi zaman a duk lokacin da yaji abubuwa sun sha mai kai.

Safwan ka'dai ne kuma yasan da cewa yana ke6e kansa a wannan gidan.
Kuka ya dinga rizga kamar yaro 'karami gashi babu mai lallashi, tausayin Noor yake ji sosai, mai yasa Ammi bazata fahimce shi ba? tayaya zai iya rabuwa da Noor cikin wannan halin bacin yasan cewa komai da ya faru sanadin sa ne, meyasa bazasu bashi dama ya cika al'kawarin da ya 'dauka ba?...yasan sakin Noor a wannan ga6ar na iya haddasa mata wani matsananciyar damuwa ne saboda yasan dole tunanin Baby zai dame ta sosai ga kuma ace shima ya sake ta da wanne da zataji?

" Ammi ki yafe min amma bazan iya rabutawa Noor saki ba sam, nasan ni mai laifi ne sosai na sani, kuma ban cancanci afuwar Noor ba, bama ni da idanun.da zan iya duban ta in nemi afuwar ta.
Amma ya zanyi Ammi? Rabuwar mu da Noor bazai gyara komai ba, al'kawari nayi yanzu Ammi zan bar dukakkn abubuwan da nake aikatawa, wallahi ko garin Bauchi Noor tace mu bari zan bari saboda ita ina son sake ganin farin cikin ta..ina son matata ina 'kaunar zama da ita, iyace farin ciki na hasken raina...".
Haka yayi ta sumbatu kamar mahaukaci, duk ya fita hayyacin sa gaba 'daya, gashi yana jin ciwo amma ya basar saboda tsananin damuwar da ke cinsa...a hakan har bacci ya yi gaba da shi.

NOORUL✔️Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang