P85

262 31 3
                                    

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*
 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy, smile, educate nd to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *85*

   Abban Jiddah murmushi yayi yana kar6an wayar yace" Ga dukkan alamu wannan muhimmacin sa na musamman ne, rabo na da ganin ki sassafe haka har na manta Jiddah".

Kunya taji sosai sai tayi 'kasa da kanta tana murmushi.

Kallo sosai ya 'kare wa Yah Deen, domin kuwa ya fahimci shima 'din yana mai ji da kansa ne, sittirar dake jikin sa ka'dai ma ta ishe sa amsa baya ga yanayin sa, domin kuwa ba'kin suit ne ajikin sa mai shegen kyau da tsada, ya rataye farar rigar sa ta aikin likitan ci bisa wuyan sa, yayin da 'dayan hannun kuma ya sanya shi cikin aljihun wandon sa yana murmushi aka 'dauki pic 'din.

Duba 'daya zaka yi masa ka tabbatar bai taso cikin babu ba domin bai gani a yanayin sa ba, motar dake bayan sa ma yasan taji ku'di ba na wasa ba.

Idanun sa kan wayar ya furta" Wannan ba mamaki babban aiki kika samo min Jiddah, takamar dama Naira ne kuma ga dukkan alamu shima 'din cikin ta yake, to da me zamu yi masa barazana kenan?"
Ya 'karasa maganar da kallon fuskar ta.

" Abbah ka ro'ke shi kawai 'kilan zai amince idan yaga kaine dan taurin kai ne da shi sosai,  nuna ku'di bazai sashi ya amince da ni ba Abbah..".

Mi'ka mata wayar yayi yana fa'din" Yanzun dai ki bari zuwa next week muga abinda hali zai yi...".

Cike da shagwa6a tace
" Abbah gobe Allah yafi  ai tambaya ne kawai..."
Idanu ya zaro yana duban ta da tsananin mamakin ta" Kina nufin tambayar auren ki zamu je a wurin mijin?"

Sai yanzu ma maganar tata ya sata kunya jin kunya, 'kasa tayi da idanun ta tana dan kwa6a fuska tace" a a Abbah I thought...maganar fahimta za'ayi...kaga sai asa ranar da za'a fara shirin tar6ar su..."
Cikin ransa yace ikon Allah..zama ni.
A fili kuwa cewa yayi
" Kar ki damu zan yi tunani akai tukunna inga ta inda ya kamata a fara"
Tuni farin ciki ya mamaye ta, fara'a ne sosai ya bayyana kan fuskar ta, tana murmushi ta furta" Thank u Abbah na, Allah ya bar min kai har 'karshen rayuwa ta".


*****
   Washe garin zuwan sa da safe lokacin da zai je gaida Alhaji Baba sai ya tafi da takaddar sakin Noor da ya rubuta yana gaida shi ya amsa a tsanake batare da ya wani bada hankalin sa gare shi ba..Yah Deen sam bai jin da'din yanda iyayen sa suka 'dauki abin da zafi har hakan, a yanzu burin sa bai wuce yaga sun dawo kamar baya ba, rabon da yaga fara'a kan fuskar iyayen nasa har ya manta, 'kara ma idan suna tare da 'yan biyu ko kuma idan suna waya da su a lokacin ne zaka tsinci fara'ar ya'ke akan fuskokin su.

Kan ninkakkiyar takaddar dake hannun sa ya sau'ke idanu, sai yaji ya karaya sosai, yau ga takaddar sakin Hudah ri'ke a hannun sa, abinda ko cikin mafarki bai ta6a tunanin faruwar sa ba..." Allah ka bani ikon jurewa".
Cikin zuciyar sa ya furta hakan yana me sakin numfashi.

Ta shi yayi daga inda yake zaunen ya matsa kusa da Alhaji Baba da hankalin sa ke wani wurin daban, hannu biyu yasa ya ri'ke takaddar da shi sannan ya mi'ka masa yana sunkuyar da kansa yace" Alhaji gashi na rubuta"..batare da wani dogon bayani ba kawai yayi shiru daga hakan.

Alhaji Baba bai yi musu ba ya sa hannu ya kar6a yana sake duban fuskar sa lura da sauyin yananyin dake tattare da shi a lokacin.

" Takaddar mecece wannan kuma?"
Tambayar da yayi masa kenan yana yatsina fuskar sa kamar be san abinda takaddar take nufi ba.
Sai yanzun ya 'dago ya dubi Alhaji Baba, da raunin murya ya bashi amsa da fa'din" Takadda ce Alhaji...takaddar sakin...mata..ta".
Baki Alhaji Baba baki ta6e yanavmurmushin gefen baki, sai a wannan lokacin kuma ya fara warware takaddar yana fa'din" Kayi kyan kai ai...Allah ya ha'da kowa da rabon sa".

NOORUL✔️Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon