P24

392 21 0
                                    

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*

 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *24*

........Ba 'karamin so take yi masa ba...gashi ba ta samun sa a waya ko ta nemeshi, a yanzu babu mai kwantar mata da hankali ko mutun 'daya, gara ma 6angaren Amin 'din ta kanji 'dan dama-dama domin shi ba laifi yana shiga rayuwar ta da nashi salon soyayyar bayaga shi kuwa kowa tsareta yake yi, mahaifin ta kuwa ba magana sosai yakeyi ba shi ko taje wurin sa ma ita ka'dai zata 'karaci kukan ta tafito shi kam sai dai yayi ta kallon ta.

Abin ma da yafi 'daga mata hankali shine dakatar mata da makaranta da akayi, dan Hayat cewa yayi ko an koma ba zata je ba ita, ranan ma tasha kuka ranar da ya gaya mata hakan, " duk menene dalili wai ?
Ta tambayi kanta...wani 6angare daga cikin zuciyar ta ne ya bata amsa da fa'din " kawai yana gudun kar rayuwar ki ta lalace ne Rahma.....wani sabon kukan ta sanya ta 'kudura a ranta cewar da zaran ya dawo zata je ta bashi ha'kuri ta kuma ro'ki alfarmar ya barta ta 'kare ko secondary ma, in yaso sai ta killace zuciyar ta daga soyayya musamman irin ta su Mu'inuddeen da bata da ribar komai daga 'karshe sai asara da tulin abin kunya ma.......tayi al'kawari matu'kar ya barta to bazata sake kula kowa ba hatta Mu'een 'din ma yanzu rabuea zatayi dashi tunda ya barta fiye da sati guda bai 'kara waiwayen inda take ba ko ma yaji halin da take ciki ba f
duk ya shareta...sai daga baya ma da tayi tunani sannan ta fahimci cewa ha'kurin nan da ya tura mata mai reshe ne....manufar sa ba 'daya bane.

Hayat kuwa duk wasu 'kananun iskanci da rashin kunyar sa ya zubar da su tun ranar da idon sa ya gane masa 'kanwar sa da ake shirin lalatawa da a tunanin sa sanadin sa ne, dan babu mamaki yasan Mu'een da gangan ya aikata hakan...... tun ranar da yaga hakan ya nutsar da hankalin sa wuri guda, ya nemo matakan hankali ya cusa cikin rayuwar sa, balle dama gashi mahaifin su babu lafiya yanzu abubuwa sun sha kansa sosai, komai shi ke jagoranta na daga dukiyar mahaifin nasu jinyar sa, ga kuma sha'anin gida ma.

   Yanzu ne ya san cewa shi babba ne a gidan, ko waccan takaddun ma da yaje ansa wurin Rahma....takaddun wani test ne da aka yiwa mahaifin nasu  sai daga baya kuma ya ga inda ta ajiye cikin 'dakin nasa ashe ranar bai nutsu ya duba da kayu bane....wanda baya raba 'dayan biyu hakan ya faru ne saboda Allah ya so nuna masa rayuwar da Rahma take ciki.
  

        Shiyasa ya dage yayi ruwa yayi tsaki wurin ganin ya aurar da ita ga wanda ya tabbatar yake yi mata son gaskiya tun bata san kanta ba....wata 'kila auren ne ka'dai zai zama katanga tsakanin ta da Mu'een.
~Wannan kenan~

*****
           Yanzu Rahma bata da burin da ya wuce taga an daina batun wannan auren nan...burin ta taji cewa an fasa aurar da ita, ko kuma taji ance mafarki ne take yi kawai ba gaskiya ba.

       Sai dai cikin rashin sa'a koda ta yiwa Hayat magana bayan ya dawo gida sai ya tabbatar mata da cewa batun auren ta gaskiya ne da fa'din " bazai ta6a iya sake barin ta a hakan ba...yace haba Rahma...kar ki manta fa da idanu na naga halin da kike ciki ba gaya min akayi ba, ta ya kike tunanin zan zuba ido inga lalacewar rayuwar ki?
Mu'een ba aure zaiyi yanzu ba balle ace shi ya fito ya aure ki na tabbata ba auren ki zai yi ba burin sa kawai ya ta6ar da rayuwar ki ne....ko kin fi son in barku ku cigaba da rayuwar dabbobin yafi miki?"

Rahma 'kasa ta sake yi da kanta sosai bata iya ta bashi amsa ba.

Shima sai ya jijjiga kansa sannan ya cigaba da fa'din ....." Darajar 'ya mace shine kafuwar mutuncin ta Rahma ki ringa tunani kafin ki aikata wani abin domin wani lokaci mutun kan manta da dacewar abu sai bayan ya aikata shi wanda in yayi wasa zai 'kare kaf 'din rayuwar sa ne yana me dana sani wacce bata da amfani sam,  kuma kinga
Daddy bashi da isasshen lafiya a yanzu so bazan so in 'kara masa wani ciwon akan wannan ba gaskiya shiyasa kawai na yanke wannan shawarar dan bana so watarana yayi kuka dani cewar ban kula da ke ba lokacin da babu idanun sa.....sannan kuma na 6oyewa kowa dalilin taso maganar auren gaba 'daya saboda in kare miki mutuncin ki Rahma.....ko kaka da su kawu shafi'u ma basu san ainahin dalilin ba, dan haka kije kawai ki cigaba da shiri...Amin na sonki sosai kuma na san zai kula da ke da amana".
Yana gama fa'din hakan yayi gaba abinsa....ya barta tana zubda hawaye.

NOORUL✔️Donde viven las historias. Descúbrelo ahora